Justice Abdool

Justice Abdool A photographer 📷
A film continuity 🎬
A Content creator 😍

LIKE AND FOLLOW PLEASE 🙏✅💜🤍
(5)

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN: Wani Yaro Ya Rasu A Wajen Jana'izar Sheik Dahiru BauchiRahotanni daga babban filin ...
29/11/2025

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN: Wani Yaro Ya Rasu A Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Bauchi

Rahotanni daga babban filin Idi na Kofar Wambai dake cikin garin Bauchi, sun tabbatar da cewa wani yaro da ba a tantance asalinsa ba ya rasu yayin gudanar da sallar jana’izar fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a yau.

Lamarin ya tayar da hankalin jama’a, kasancewar babu wanda ya san daga inda yaron ya fito, ko kuma tare da wane yake kafin faruwar rasuwar. Hakan ya sa ake kira ga jama’a da su taimaka wajen yada wannan bayani domin a gano danginsa ko wanda ya san shi.

Rahoto ya nuna cewa an kai gawar yaron Asibitin Bakaro bayan Fada a cikin garin Bauchi. Ana sa ran cewa da zarar an samu danginsa, za su zo su karɓe shi.

Sai dai, idan babu wanda ya bayyana a lokaci kusa, hukumomi za su mika gawar zuwa dakin ajiye gawa na Asibitin Koyarwa na Sir Abubakar Tafawa Balewa (ATBU Teaching Hospital) domin ci gaba da adana ta bisa ƙa’ida.

Allah Ya jikansa, Ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure wannan rashi idan aka same su.

Daga Eagle Radio

TSARO: Lokaci ya yi da zamu goyi bayan Shugaba Tinubu domin Murƙushe 'yan ta’adda A Arewa. Gwamna Abba Kabir Yusuf na Ka...
27/11/2025

TSARO: Lokaci ya yi da zamu goyi bayan Shugaba Tinubu domin Murƙushe 'yan ta’adda A Arewa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya bayyana cikakken goyon bayansa ga dokar ta baci kan tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana, yana mai cewa lokaci ya yi da za a ƙara matsa kaimi wajen murkushe ’yan fashi da masu garkuwa da mutane.

Ya ce Kano za ta dauki dukkan matakan da s**a dace don kare al’umma, musamman yankunan iyaka da s**a fuskanci hare-hare kwanan nan, inda aka sace mutane tare da tayar da hankulan jama’a.

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta yi shiru ba, kuma za ta tashi tsaye wajen kawar da barazanar ta’addanci a jihar.

Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya Ta Janyewa Atiku, Namadi Sambo, Wike, Aisha Buhari Da Sauran Wasu Mutane 17 Jami'an Tsaro,...
27/11/2025

Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya Ta Janyewa Atiku, Namadi Sambo, Wike, Aisha Buhari Da Sauran Wasu Mutane 17 Jami'an Tsaro, Inda Ta Umarce Su Da Su Koma Sansanoninsu

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai. Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W) ...
26/11/2025

Da Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinkai. Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W)

Nake Farin Cikin Gabatar Wa da masoyana sabon Shiri mai gajeran Zango na Farko da zan fara bada umarni mai suna 🎬🎬🎬🎬

Ingantaccen Labarin da yake dauke da muhimman sako da darasi wanda masu kallo zasu jima suna yabawa, dauke da Ingantattun jarumai wanda zasu isar muku da sakon yadda ya k**ata.

Zamu fara daukar sa ranar 5 ga Watan December Inn shaa Allah. Zai fara zuwar on 10th January Inn shaa Allah A YouTube channel din MAISHADDA GLOBAL RESOURCES da kuma Gidan Tv Na . Kada ku sake a baku labari

Daga Gawurtaccen Kamfanin MAISHADDA GLOBAL RESOURCES NIG LTD

Daukar Nauyi/Shiryawa/Bada Umarni


Labari
NURA HUSSAINI

Tsara Labari


M/Umarni


D.O.P


Daukar Hoto


Sponsorship Partners

ng



NASRUN MINALLAHI WA FATHUN QAREEB

GOBE NE Zamu sakar muku shahararren film dinmu mai suna KWANA DAYA. Wato 27th November 2025 a YouTube channel dinmu mai ...
26/11/2025

GOBE NE Zamu sakar muku shahararren film dinmu mai suna KWANA DAYA. Wato 27th November 2025 a YouTube channel dinmu mai suna Sultan film factory da kuma Algaitatv insha Allah .
Cc









**alumijinyawa

26/11/2025

An tabbatar da rasuwar wani uba da ke da ’ya’ya uku cikin daliban da aka sace a Makarantar St. Mary da ke Papiri, Jihar ...
26/11/2025

An tabbatar da rasuwar wani uba da ke da ’ya’ya uku cikin daliban da aka sace a Makarantar St. Mary da ke Papiri, Jihar Neja, bayan ya samu bugun zuciya saboda tsananin damuwa.

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) na Arewa da Babban Birnin Tarayya, Fasto John Hayab, shi ne ya bayyana hakan a hirarsa da Channels TV a jiya Talata.

A cewarsa: “Daya daga cikin iyayen yaran da aka sace ya rasu jiya saboda bugun zuciya. Mr. Anthony ya mutu ne saboda matsananciyar damuwar sace ’ya’yansa uku.”

Hayab ya ce har yanzu tashin hankali da tsananin damuwar da iyalan ke ciki yana da tsanani, inda ya bayyana cewa lokacin da s**a je wajen iyayen domin jin ta bakinsu, da yawa sun nuna tsoron yin magana.

A baya jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa dalibai 50 daga cikin wadanda aka sace sun tsere daga hannun ’yan ta’adda, inda s**a koma gidajensu cikin tsanaki. Hakan ya faru ne bayan kwanaki kadan da maharan s**a afka makarantar s**a sace dalibai da malamai 303.

Bishop Bulus Dauwa Yohanna, Shugaban CAN na Jihar Neja kuma mai kula da makarantar, ya tabbatar da dawowar yaran. Ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da addu’a don ceto sauran wadanda suke tsare a hannun ’yan bindiga.

Bai k**ata a nuna sakin yaran da aka sace a matsayin nasara ga gwamnati ba ~ Alhaji Atiku Abubakar
26/11/2025

Bai k**ata a nuna sakin yaran da aka sace a matsayin nasara ga gwamnati ba

~ Alhaji Atiku Abubakar

Gwamnatin Tinubu ta gaza Murƙushe 'yan bindiga yanzu ta koma Sulhu dasu domin karɓo Dalibai -Atiku Abubakar Atiku Abubak...
26/11/2025

Gwamnatin Tinubu ta gaza Murƙushe 'yan bindiga yanzu ta koma Sulhu dasu domin karɓo Dalibai -Atiku Abubakar

Atiku Abubakar ya caccaki Shugaba Tinubu kan yadda gwamnati ta kasa murƙushe ko k**a ’yan ta’addan da s**a sace ’yan matan Kebbi, maimakon a je kai tsaye a kare rayukan jama’a.

Atiku yace “Me ya hana a dakile su? Me ya sa gwamnati ta koma sulhu da masu garkuwa da mutane?”

Jama’a na tambaya: Tsaron Najeriya ya tsaya ina ne, idan gwamnati ke mika wuya ga ’yan ta’adda?

Ana Kara Jan Haknalin El-Rufai Da Ýa Dàuki Mataki Ķan Wasu 'Yaƴansa BìyuAna ci gaba da jan hankalin tsohon gwamnan jihar...
26/11/2025

Ana Kara Jan Haknalin El-Rufai Da Ýa Dàuki Mataki Ķan Wasu 'Yaƴansa Bìyu

Ana ci gaba da jan hankalin tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai da ya ɗauki tsatsauran mataki kan wasu yaransa biyu Ibrahim da Balkisu (Bilqis) a sak**akon wata hanya da su ka ɗauka na kauce wa addinin muslunci.

Binciken Hausa Daily Times ya gano cewa: Ibrahim wanda shi ne ɗan auta ga mayar El-Rufai ta farko Hajiya Hadiza, ya bayyana ƙarara cewa bai ýàďda akwai Alĺàh ba, don haka ya jima daga fita addinin muslùmci. Waɗannan furuci na shi na cikin wasu bidiyoyin da ya ke sakewa a shafinsa na Instagram.

Ita kuwa Balkisu (Biliqis) ita ce babbar ƴa (ƴar fari) ga matar El-rufai ta biyu Barista Asiya. Ta bayyana wa duniya cewa ita mai fafutukar kare masu auren jinsi ce wato ma'ana ita ƴar ĹĞBŢQ.

Wani abin lura a nan shi ne, dukka yaran biyu dai na zaune ne a ƙasashen waje.

Duk da cewa babu wani daga cikin ahalinsu da ya fito ya ƙaryata ko kuma ya gaskanta labarin da ke yawo a kansu biyo bayan fitan wasu hotuna marasa kyaun gani tare da bidiyoyin su suna iƙirari da ra'ayin abin da su ka yi imani da shi a kai ba tare da nadamar abin da su ke yi ba. A kan hakan ne ake jan hankalin mahaifisu da ya taka musu birki tun kafin lamarisu ya yi nisa.

Rahoton Hausa Daily Times

Address

Kaduna South

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Justice Abdool posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share