06/09/2026
HALKAR IMAM MAHDI SUN GUDANAR DA MAULIDIN MANZON ALLAH (S).
Daga-: Fatima Khamis.
Daga cikin Maulidin Halƙoƙi da ake ci gaba da gudanarwa a Da'irar Kaduna, yau ma Yan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na Halkar mai zamani, (Imam Mahdi Atfj) sun gudanar da nasu Maulidin.
Taron wanda ya gudana a Rigasa Kaduna, ya fara ne da misalin karfe uku na rana, inda aka fara da buɗe taro da Addu'ah, bayan haka, sun gudanar da karatun Alƙur'ani mai girma domin neman albarka ga taron, daga bisani mawaƙa sun faranta ran masoya Manzon Allah (S), kammalawarsu kenan aka yi Tamsiliyya akan biyan hakkin Shuhada'u. Bayan haka an gudanar da ziyara da kuma Fareti, wanda yaran Fudiyya su ka gudanar domin girmamawa ga Annabin Allah (S).
Daga bisani an mika abin magana ga babban bako mai jawabi, Shaikh Shareef Ahmad Rufa'i wanda ya gudanar da jawabi akan darajojin Annabi (S) da iyalan gidan sa.
Bayan Kammala jawabin, Wakilin Ƴan uwa na garin Kaduna, Malam Aliyu Bakin Ruwa ya gabatar da Ta'aliƙi a wurin.
Daga ƙarshe aka yanka Alkaki, aka raba walima tare da yin addu'a, sannan aka yi Addu'ah aka Sallami kowa, anyi Taro Lafiya kuma an kammala lafiya.
Kaduna Media Forum.
6/September /2026M