13/10/2024
Ƙungiyar Arewa Media Writers Ta Halarci Taron Wayar Da Kan Al'umma Da Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya Ta Shirya A Jihar Katsina
Daga Kungiyar Arewa Media Writers
Ƙungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani "Arewa Media Writers" ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Comr Haidar H. Hasheem, ta halarci taron wayar da kan al'umma a jihar Katsina. Taron na kwana guda an shirya shi ne ƙarƙashin gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya (Coalition of Northern Groups - CNG), wanda aka gudanar a jiya Asabar bisa jagorancin Shugaban kwamitin amintattu na CNG, Dr. Nastura Ashir Sharif.
Taron ya samu halartar shugabannin ƙungiyar a matakin jiha da kuma mambobi daga Katsina, inda aka samu wakilcin shugaban Arewa Media Writers na jihar Katsina, Comr Nura Siniya, tare da shugabannin ƙungiyar na jihar Katsina da sauran mambobi. Wannan taro na da muhimmanci wajen tattauna matsalolin tsaro da kuma yadda za a kare yara daga shan miyagun ƙwayoyi, musamman a yankin Arewacin Najeriya.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Comr Haidar H. Hasheem, ya yi jawabi a wajen taron, inda ya nuna muhimmancin haɗin kai wajen magance matsalolin da suke addabar yankin Arewa. Ya kuma jaddada cewa, akwai buƙatar gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su haɗa hannu wajen kare martabar yankin ta hanyar magance matsalolin tsaro da shaye-shayen kayan maye.
A yayin taron, an gabatar da tattaunawa mai zurfi kan hanyoyin da za a bi domin ƙarfafa tsaron al'umma da kuma samar da shawarwari akan dabaru da za su taimaka wajen tsaftace rayuwar matasa da kare su daga faɗawa cikin haɗarin shaye-shaye. Haka kuma an yi kira ga iyaye da su yi amfani da damar wajen kula da tarbiyyar 'ya'yansu.
A ƙarshe, Comr Haidar H. Hasheem, ya buƙaci mambobin ƙungiyar da al’umma baki ɗaya su ci gaba da bayar da goyon baya domin samun nasarar burin da aka sanya a gaba na inganta tsaro da walwalar al’umma.
Arewa Media Writers na bukatar addu'oinku domin ganin ta sauke babban aikin da ta É—auka a wannan lokaci.