16/06/2025
JAGORA (H) YA GABATAR DA JAWABIN RANAR GHADEER
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Da yammacin Lahadi 18 ga Zulhijja, 1446 (15/6/2026), Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabin Ranar Idil Ghadeer a gidansa da ke Abuja,
Jagoran ya fara jawabi ne da godiya ga Allah Ta’ala dangane da sanya mu da ya yi a cikin masu Wilaya. Yace, ba shakka wannan yini ne mai muhimmanci. “An tambayi Imam Jafarus Sadiq (AS), baya ga Idodin nan biyu da kuma Juma’a, Musulmi na da wani Idi ne? Sai yace, kwarai kuwa, shi ne ma ya fi dukkansu, shi ne Idil Ghadeer. Yace Allah bai aiko wani Annabi ba daga cikin Annabawa face ya yi Idi da wannan Idin.”
Jagora yace, ba bisa hadari ba ne ya zama dukkan Annabawa sun saka ‘Ausiya’ dinsu a irin wannan rana ta Ghadeer, wato 18 ga Zulhijja. Yace, ba wani Annabi da ya taba zuwa da sako, ya tafi ya bar al’ummarsa wawai, ba tare da wanda zai cigaba da bayanin sakonsa a bayansa ba. “Wannan hankali ba zai dauka ba, ace Allah Ya aiko Annabi, ya shiryar da al’umma, har ma ya kafa daula, - ko da ma bai kafa daula ba, ballantana kuma ace ya kafa daula, - amma shikenan sai ya tafi ya bar su, yace ‘amrukum shura bainakum’, kawai sai su yi shawara su zabi wanda ya dama. Hankali ba zai yarda da wannan ba. Tunda dai shi Allah Ya aiko shi, kuma ya san abinda ya fi dacewa ga al’umma, to (dole) shi ne zai shiryar da su izuwa ga wannan abin.”
Jagora ya bayar da uzuri ga ‘yan uwa dangane da rashin yiwuwar gabatar da taron Ghadeer tare da shi a babban muhalli. Yace, hakan ya faru ne sak**akon takura mu da mahukuntan kasar nan, wadanda karnukan Sahayina ne s**a yi. Ya kuma karfafi cewa, a nemi jawaban da ya gabatar a shekarun baya wanda duk an sajjala su a kaset mai hoto da kuma na sauti. “Akwai Cibiyar Wallafa, sun saka karatuttukan da muka yi na baya, amma sauti ne, saboda haka ba bukatar mu yi ta maimaita abu guda.”
Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Mu muna magana da junanmu ne, ba muna yi da wasu ba ne, muna yi da Ahlul Wilay