10/01/2026
Maraba da Zuwa Shafin Hasmag TV Ku Bibiyemu ta WhatsApp Channel Domin Samun Labarai da Dumi-Dumin Sa
Follow the HASMAG TV channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7pygJEquiHaMEIZD2f
SUBHANALLAH: ’Yan bindiga sun sake kai mummunan hari a Borgu, Jihar Neja.
A daren Juma’a, 9 ga Janairu, 2026, wasu ’yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Damala da ke yankin Wawa, cikin Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja. Harin ya faru ne tsakanin ƙarfe 8:00 zuwa 8:30 na dare.
Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa maharan sun kashe mutane huɗu, tare da kwashe dabbobin jama’a gaba ɗaya, s**a tura su cikin daji. Haka kuma sun ƙona coci guda ɗaya da gidaje da dama, lamarin da ya jawo asarar dukiya mai yawa tare da tilasta wa iyalai da dama tserewa daga gidajensu.
Shaidu sun ce an kai harin ne kwatsam, kuma babu jami’an tsaro a yankin a lokacin, abin da ya sa al’umma s**a rasa kariya. Ya zuwa lokacin fitar da wannan labari, babu wata sanarwa a hukumance daga hukumomin tsaro.
Mazauna Borgu da ƙauyukan da ke kewaye sun sake yin kira ga gwamnatocin jiha da tarayya da su gaggauta tura jami’an tsaro domin kare rayuka, dukiyoyi da wuraren ibada.
Hasmag TV