Fityanul islam media Zango

Fityanul islam media Zango Godiya ga Allah da ya raya mu, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammadu s.a.w Tare da Ahlinsa da Sahabbansa.

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa'azi Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa...
01/10/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa'azi

Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa ya sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa'azi.

A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a yau Laraba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar ya kare kan sa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Ma'aiki.

A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakin sa a matakin Majalisar ta shura.

Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya bukaci da a kyale kwamitin ya kammala aikin sa.

Sagagi ya tabbatar da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da son rai ko rashin adalci ba.

Daruruwan mutane ne s**a halarci Jana'izar Sheikh Modibbo Dahiru Aliyu Ganye Yau😭, A Kofar Gidansa Dake Unguwar Madina a...
19/09/2025

Daruruwan mutane ne s**a halarci Jana'izar Sheikh Modibbo Dahiru Aliyu Ganye Yau😭, A Kofar Gidansa Dake Unguwar Madina a Karamar Hukumar Ganye, Jihar Adamawa.Allah Bamu Albarkacinsu Duniya Da Lahiraaa😭
Sai Munzo

AlhamdulillahSheikh Ahmad Tijjani University of NigeriaCibiyar Fitiyanunl Islam ta kasa tayi nasarar gamdakatar da wata ...
02/08/2025

Alhamdulillah
Sheikh Ahmad Tijjani University of Nigeria

Cibiyar Fitiyanunl Islam ta kasa tayi nasarar gamdakatar da wata katafariyar fili a Jihar Kaduna tare da sahhalewar Gomna Uba Sani dake Jan ragamar Jihar.

Cibiyar ta sanar da hakan ne ta bakin shugaban ta Sheikh Arabi Sheikh Abulfathy yayin ziyarar Filin a Karon farko a yammacin jiya bayan karbar takar sahhalewa daga gomnati tare da sanar da abunda za'a gudanar a wannan fili.

Shugaban ya tabbatar da cewa cibiyar ta Fitiyanu zata Gina University Mai dauke da sunan Shehu Ahmadu Tijjani a Karo na farko a Africa a wani yunkuri na habaka ilimin addinin Musulunci Tare da tabbatar da ayyukan kere-kere na zamani gami da cikakken tarbiyya Al'ummar manzon Allah SAW har ma da fasahar nan ta yanar gizo dake baza capacity a yanzu haka.

A yanzu haka wannan fili ya Zama mallakin Yan Tijjaniyya karkashin jagorancin cibiyar Fitiyanunl Islam.

Muna fatan Allah ya nuna mana ranar aza tubalin ginin wannan makaranta Alfarmar shuba SAW Ameeeeen.

✍️Basiru ibrahim zango

Allah ya yi wa Sheikh Ibrahim Niass fitaccen jagoran darikar darikar Tijjaniyya ta yammacin Afirka rasuwa a ranar 26 ga ...
27/07/2025

Allah ya yi wa Sheikh Ibrahim Niass fitaccen jagoran darikar darikar Tijjaniyya ta yammacin Afirka rasuwa a ranar 26 ga Yuli, 1975, da misalin 12 da mintuna 3 rana, a London, Ingila, a asibitin St. Thomas. Yana da shekaru 75 a duniya. Mutuwarsa ta faru ne a sashen Simeon's Ward na asibitin, a daki mai lamba 2632. Mutuwar Sheikh Ibrahim Niass wani muhimmin al'amari ne ga miliyoyin mabiyansa a fadin yammacin Afirka.

Yayin da bayanan da aka yi ya yi nuni da cewa ya je Landan ne don jinya, ba a fayyace ainihin musabbabin mutuwar ba. An mayar da jikinsa Senegal aka binne shi a Madina Baye, Kaolack, kusa da masallacinsa.

Tafiya ta karshe ta Shaikhul Islam, Alhaji Ibrahim Niass ta gudana ne a watan Yuni a shekarar 1975, wanda yayi daidai da watan Jumada thani na shekara ta 1395 bayan hijira.

Ya sanar da iyalansa cewa yana son yin takaitacciyar tafiya zuwa Landan. A lokacin yana da shekaru 75 a duniya. Kamar yadda ya saba, da yawa daga cikin ’ya’yansa maza sun so su tafi tare da shi, amma Shaihu ya ki amincewa da shawararsu bisa hujjar cewa tafiyar gajeriya ce.

Ya Allah ya jikan Shaikh Ibrahim inyass da rahama ya sada shi da masoyinsa Annabi Muhammad (Rasulillahi Sallallahu Alaihi wa Alihi Wasallama).

✍️Basiru ibrahim zango

إنا لله وإنا إليه راجعونCikin alhini da jimami ina miƙa saƙon ta'aziyya ga al'ummar musulmi, musamman iyalai da almajira...
26/04/2025

إنا لله وإنا إليه راجعون
Cikin alhini da jimami ina miƙa saƙon ta'aziyya ga al'ummar musulmi, musamman iyalai da almajiran Sheikh Mainasara Liman tudun wada Zariya, shugaban masu wa'azi na ƙasa na ƙungiyar Fityanul Islam.

Lallai anyi rashin babban malami wanda ya ƙarar da rayuwarsa ɗungurun gun akan hidiman addinin musulunci da yaɗa soyayyar manzon Allah ga zugatan al'ummar musulmi.

Allah ya jiƙansa ya gafarta masa ya sada shi da masoyinmu Annabi Muhammadu saw.

20/02/2025

MUNA SANAR DAKU YAU KAMAR KULLUM AKWAI WA'AZI KQMAR YADDA AKA SABA DUK SATI

Address

Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fityanul islam media Zango posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Fityanul islam media Zango:

Share