04/12/2025
Daga Shafin Abdulmajid
Budadden Sako zuwa ga Masu kare Hakkin Hausa...
Musamman irinsu Malama Kaltuma da Gimbiyar Hausa, fatan kuna cikin koshin lafiya.
Tun bayan bullar labarin shirinmu na yin film kan rayuwar Nana Asma'u Dan Fodio, na ga kun tsananta da rubuce-rubuce da sakonni na murya inda kuke yin sharhi ko martani kan abinda har yanzu ma baku san menene ba.
Wannan ne dalilin da ya sa na ji ya kamata na fayyace muku wasu abubuwa guda uku kamar haka
1 Ni dai sunana Rahma Abdulmajid... A shekara mai zuwa zan cika shekaru 30 cif ina baiwa harshen Hausa gudunmawa ta hanyar rubutu wanda na fara tun ban wuce shekara 15 ba, watakil ma da yawanku a lokacin baku san wenene bahaushe ba. A cikin wannan shekaru na fuskanci kalubale da ya girmi barazanar ku, ba tare da na fasa ba. Babban abinda na ke da yakinin na nuna a wannan tsayin shekarun shine yadda bahaushe ke iya kyautar abu mafi kima gare shi wato harshensa don sadar da amfani har ga wanda ma ba bahaushe ba. Ba ni kadai ba, akwai dubban marubuta da malaman jami'a wadanda ba hausawa ba ne zalla sun yi wa harshen hausa hidimar tattara adabinsa da Ilminsa da tarihinsa tun kafin zuwana har aka iso yau ku ma kuka samu kuke amfani da aiyukansu wajen rubutunku.
2 Aikin Film din Nana Asma'u, na shirya yinsa ne don bayyana wani gagarumin aikin 'ya mace Musulma a Arewacin Najeriya kan yada ilmi ba yaki da cin garuruwa ba, aikin bai da alaka da kabilanci ko yare, manufar aikin shine Arewa ta fara bayar da labarin kanta da kanta.
Irin wannan aiki na bajinta ba mu sami irinsa a sauran gimbiyoyin da kuke fada na hausawa ba tukuna sai a kan Nana Asma'u, shi aikin tarihi ba aikin shaci-fadi ne ko fatar baki ko kiran sunaye ba, ita kanta Nana Asma'u duk da ta yi rubutu sai da aikin tace labarinta ya dauke mu shekaru uku, kun ga kenan ba wai aiki ne zamu yi akan tatsuniyoyin da basu da tushe sai don an hada su da sunan martani ko fushi ba