Dandume Post

Dandume Post Domin Samun Labarai ku Kasance da jaridar baturiya Hausa

27/02/2024
04/09/2023

Al'ummar yankin Funtuwa zone sun yabawa Sanata Muntari Dandutse bisa kokarinshi na samar da zaman lafiya da kuma tallafawa Al'umma

Daga jamilu Garkuwan Dandutse Dandume

Awani binciken jin Ra'ayin jami'a da kungiyar Dandutse Media Reporters ta gunanar, kungiyar ta gudanar da binciken ne a daukacin kananan hukumomin yankin Funtua zone, 11 Ƙungiyar Ta gudanar binciken ne Domin jin ra'ayin jama'a Akan yadda suke ganin kamun Ludayin wakilcin Sanata Muntari Dandutse.

Sanata Muntari Mohammed Dandutse Shine Satanan dake Wakiltar Funtua zone, Katsina ta kudu a Majalisar Dattawan Nigeria kuma shugaban kwamitin kula da harkokin gidauniyar cigaban manyan makarantun Nijeriya TETFUND.

A tattaunawar da Muka yi da Al'ummomin da Ban da Ban, jami'a da'dama sun bayyana ra'ayinsu akan Sanatan, mafiyawanci mutanen da muka tattauna dasu, sun yabawa sanatan bisa Ƙoƙarin da yake yi wajan ganin yankin Funtua zone yasamu zaman lafiya, da kuma tallafawa al'ummar shi awannan lokacin da jama'a suke cikin Kuncin rayuwa.

A tattaunawar da muka yi da Hon. Murtala Muhammad Malamiyya Funtua mazaunin karamar hukumar Funtua, Malamiyya ya bayyanawa majiyarmu ta Dandutse Media Reporters cewa" Sen Muntari Dandutse dan siyasa ne wanda ya dade yana taimakon al'umma kuma Mutum ne mai kishin al'umma wanda kullum burinshi Taimakon Al'umma"

yaci gaba da cewa nasan Dandutse Jajirtacce ne wajan Ganin ya kawo ma Al'ummar cigaba, ya cigaba da cewa" daga Zuwan shi majalisar Dattawa Dandutse ya rabawa manoma takin zamani ya kuma baiwa Jami'an tsaro Babura da motoci domin Ganin Kawo karshen matsalar tsaron dake addabar Yankin Funtua zone.

"Dandutse ne ya Jagoranci masu Ruwa da tsaki na Yankin Funtua zone, wajan ganin ansamu Babbar makaranta a wannan Yankin, Dandutse ya kuma kai Kudiri a Majalisa akan Halin da Yankin Funtua zone yake ciki, ya kuma kai Kudiri akan dakatar da hukumar Kwastan wajan kashe Al'umma a jihar Katsina.

Dandutse yayi ayyuka da dama Acikin wata uku Saboda haka idan Allah yasa Dandutse ya shekara 4 a wannan kujera Allah kadai yasan iyakar cigaban da zai kawo awannan Yankin.

Dukkanin Al'ummomin da muka zanta dasu sun bayyana Dandutse a matsayin Jajirtaccen shugaba sun kumayi addu'a akan Allah ya baiwa Sen. Muntari Dandutse damar sauke nauyin dake kanshi,

daga karshe muna addu'ar Allah ya Kawo mana zaman lafiya Ameen

24/07/2023

'Raba wa talakawa kuɗi don rage radadin cire tallafin mai ba shi ne mafita ba'

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya soki tsarin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da shi na raba wa ƴan Najeriya tallafin rage radadin cire tallafin mai.

Ita dai gwamnatin ta ce za ta raba wa ƴan kasar miliyan goma sha biyu ne, daga cikin su sama da miliyan 200, Naira dubu dari takwas har tsawon watanni shida.

Sai dai a cewar gwamnan na Kaduna, babu fa'ida a wannan al'amari domin ba zai taimaka k**ar yadda ita gwamnatin ke fata ba.

Ya ce ''Abin da muka gano shi ne mu a nan Arewa, kashi 75 cikin 100 na al'ummarmu ba su da asusun ajiya, idan kuma mutum bai da asusun ajiya a banki ta yaya wannan tallafi zai same shi?''

Gwamna Uba Sani, ya ce shi ya sa duk lokacin da aka yi maganar bayar da tallafi a Najeriya sai ka ga ƴan Kudu ne ke amfana, domin yawancinsu, na da bankunan ajiya, da kuma sani kan yadda za su ci gajiyar tsarin.

''Kuma yanzu idan aka ce za a raba wannan kudi da ake magana sama da dala miliyan 800 da za a karbo daga wajen Bankin Duniya, ina tabbatar maka da cewa daga karshe yan Arewa ba za su ci gajiyar ko kashi goma ba'' in ji shi.

Ya ce a kokarin gwamnatinsa na samar da ingantaccen tsari, za ta fara shiga yankunan karkara domin tabbatar da bude wa jama'a asusun banki, don samun saukin tafiyar da harkokinsu.

A halin da ake ciki a iya cewa cire tallafin man fetur din da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanar ya jefa ƴan
kasar da dama cikin tasku, la'akari da yadda farashin komai ya tashi, k**a daga kan sufuri, kayan abinci, da sauran bukatun yau da kullum.

A yawancin jihohin kasar dai maganar da ake ana sayar da litar man fetur sama da Naira dari shida, sak**akon kari na biyu na baya-bayan nan da aka yi.

Sai dai gwamnatin Shugaba Tinubu na ganin cewa tsarin da ta bullo da shi na raba wa mutum miliyan 12 Naira dubu takwas zai taimaka wajen rage wa jama'a radadin taskun da s**a shiga.

Masu s**a dai na ganin cewa duk da cire tallafin ya zama dole a halin da ake ciki, gwamnatin ba ta yi kyakkyawan tsari na yadda za a aiwatar da shi ba.

Maganin_____madagwal❤️❤️❤️
27/04/2023

Maganin_____madagwal❤️❤️❤️

Mr__Cee___Manager__💰💰💰💰💰
26/04/2023

Mr__Cee___Manager__💰💰💰💰💰

Address

Ddm
Kaduna
KJR

Telephone

+2348087715994

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dandume Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dandume Post:

Videos

Share