04/08/2026
JAGORA (H) YA RUFE TATTAKIN ARBA'EEN NA IMAM HUSAINI (AS) NA SHEKARAR 1448H
Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar da jawabin rufe Tattakin Arba'een na Imam Husaini (AS) a yau Talata, 20 ga Safar 1448H, wanda ya yi daidai da 4 ga Agusta, 2026. An gudanar da taron ne a Babban Filin Wasa na Suleja, kusa da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A farkon jawabinsa, Jagora (H) ya tunatar da mahalarta cewa ranar 20 ga Safar ita ce ranar cikar kwanaki arba'in da shahadar Imam Husaini (AS), iyalansa da sahabbansa. Ya bayyana cewa ziyarar Arba'een wata ibada ce da ta samo asali tun daga shekara ta 61 bayan Hijirar Manzon Allah (SAW), lokacin da Sahabi Jabir bn Abdullahi Al-Ansari (RA) ya fara ziyartar kabarin Imam Husaini (AS) bayan aukuwar waƙi'ar Karbala.
Ya ci gaba da bayyana muhimmancin ziyarar Arba'een tare da kawo hadisai da s**a nuna falalarta, yana mai ƙarfafa muminai su ci gaba da raya wannan al'ada ta Ahlul Baiti (AS).
Shahidanmu TV