31/08/2024
YAWAN AMBATON ALLAH..!!.
Yawan ambaton Allah na daga cikin manyan ni'imomin Allah ga bayinSa na musamman. Ambaton Allah shi ne abincin zuciyarka da natsuwarta. Sannan kuma waraka ne daga qunci da damuwarka.
Yawan ambaton Allah na qara kusantar da bawa ga mahaliccinsa har bawa ya zama mai gata a wajen Allah, tare da bashi kariya daga mugayen mutane da shaidanu.
Sabo da darajar ambaton Allah Mala'iku kullun a cikinsa suke. Kuma shi ne numfashin 'yan Aljannah. Kar ka manta ! Malai'ku na rubuta dukkan ayyukanka; yi qoqari su rubuta maka ambaton Allah da yawa a kundin ayyukanka.
Akwai wasu bayin Allah da ambaton su ga Allah fa ya fi maganarsu yawa a wannan rayuwar. Yi qoqari ka samu rabonka.
Subhanallah, wal-hamdulillah, wa la ilaha illalLah, wallahu Akbar, wala haula wala quwwata illa billah.
Dr Jameel Muhammad Sadis Zaria Hafizahullah