29/09/2025
JAHILIYYA ✔,
Chiɓiri Nannagi, Lallai Akwai Matsala,
duk ranar da wasu al'ummar musulmai su ka taso basu san abin da ya gudana ko a ke kira zamanin jahiliyya ba, to fa za a iya kacha-kacha, ko gunduwa-gunduwa da addinin musulunci,
wannan ne ya sa mu ke so dole al'ummar musulmi su san wai shin menene jahiliyyan nan?, dole musulmi su san menene ya sa Annabi Muhammadu (S.A.W) ya saɓa da su 'yan jahiliyyan!,
domin yanzu idan kun lura da kyau, an riga an fara chaɓewa, da kwaɓewa, tare da chakuɗa addinin musulunci da na yan gargajiya,
a yanzu idan za ka nunawa mutum cewa wannan ne abin da Annabi (S.A.W) ya zo dashi, wannan na yan gargajiya ne, wannan na yan al'ada ne, ga na nasaranci, wannan kuma na yahudanci ne, to sai ka ji a na ce maka haba wane, yi shiru mana, taho nan, to zauna ka ji, wai za a fahimtar da kai, wato wai kai ba ka waye ba kenan,
chabɗi-jan, to irin wayan nan mutane ma su fadin haka, wato dai da ace Annabi Muhammad (S.A.W) ya na nan a raye to da mun ga yadda za su je su wayar masa da kai, ALLAH ya kyauta,
jama'a, a yi ƙoƙari a san menene jahiliyyan nan, kuma a san me ya gudana a zamanin jahiliyyan, domin kaucewa ruɗin shaiɗan, da kamusan malamai, madalla,
| Sir Babawo Fadan Chawai| ✔.