20/05/2025
ZIYARAR TA'AZIYYA DA GAISHE-GAISHE A GARIN ZARIYA
Daga: Tajudeen Abbas Media Frontliners
Ranar 18/05/2025 Hajiya Fatima Abbas Tajudeen, tauraruwar Iyan Zazzau, Rt Hon Tajudeen Abbas Phd GCON, Sifikan Nijeriya na 10 ta ziyarci garin Zariya domin ta'aziyya da kuma gaishe-gashe a garin Zariya, a inda ta zagaye wurare mabambanta masu yawa duk a garin Zariya.
Hajiya Fatima ta fara da ta'aziyya ne gidan Dallatun Zazzau, Alh. Muktar Ramalan Yaro, tsohon gwannan jihar Kaduna na rashin mahaifinsa da ya yi. Daga nan ta wuce barkan haihuwa gidan Sarkin Yakin Iyan Zazzau, inda ta taya shi murnar samun karuwan haihuwa da ya samu. Sannan tawagar ta zarce zuwa Fadan Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambassader Ahmad Nuhu Bamalli, domin gaisuwar ban girma a gare shi a matsayinsa na uban kasa.
Daga nan ziyarar ta ci gaba zuwa gidan Captain Shehu iyal dake Kwarbai cikin birnin Zariya, inda ta yi wa iyalansa ta'aziyar rasuwarsa, tare da nuna jimami da alhinin wannan babban rashi da karamar hukumar da ma jihar Kaduna baki daya ta yi. Sannan ta ci gaba da bin sako da lungu na garin Zariya, domin gabatar da ziyarce-ziyarce tare da nuna zumunci da kauna da mutanen Zariya ke nuna wa Kakakin Majalisan Tarayya, Rt. Hon. Abbas Tajudeen a matsayinsa na dansu, kuma mai nuna kishi a gare su.
Duk wadannan zagayen ta'aziyya da gaishe-gaishe an yi su ne karkashin jagorancin Dan Malikin Iyan Zazzau , Hon. Hamza Zubairu Albarka, wanda shi ne ya jagoranci tawagar Tauraruwar tun daga farko har zuwa karshe.
Muna addu'a Allah ya ji kan wadanda s**a riga mu gidan gaskiya, in tamu mutuwar ta zo ya sa mu mutu muna Musulmai masu imani🙏
Tajudeen Abbas Media Frontliners (TAMF)