
16/07/2024
Su Kuɗi suna Karkata ne ga Ƙima (Value) kamar yadda Tururuwa take Karkata ga Sukari.
Duk wani mai kuɗi a duniya ya yi kuɗi ne ta hanyar karɓa daga hannuwan mutane. Kuma ba tare da ya yi masu tilas ba.
To kaima fa, duk kuɗin da ka kashe a baya da waɗanda zaka kashe a gaba zaka karɓe su ne daga hannun waɗansu.
Su kuɗi ba sa faɗowa daga sama kuma ba'a gina rami a ɗebe su ko a ciro su daga jikin bishiya, daga hannun mutane ake karɓar su.
Don haka idan kana so ka zama mai kuɗi, dole ne ka kware wurin karɓe kuɗin dake a hannun mutane.
Amma ta yaya zaka yi hakan?
Dole ka zama mai warware wa mutane matsalolinsu ko sauƙaƙa masu rayuwarsu.
Wannan shi ne abin da ake nufi da samar da ƙima.
Kuɗi ba komai ba ne face hanya ta musayar ƙima, wato "exchange of value," ko ka ce ba-ni-in-ba-ka.
Ka samar wa mutane da abin da suke so su kuma ba zasu ji nauyin miƙa maka kuɗaɗensu ba, a wani sa'in har magiya zasu yi maka don ka karɓa.
Mutane suna buƙatar abinci da ruwan sha, da sutura, da mazauni. Suna buƙatar littafai da makarantu don koyon karatu, suna buƙatar hawa jirgin sama don tafiye-tafiye.
Mutane suna buƙatar siyan data don su yi nishaɗi, suna buƙatar ɗaukar hotuna don adani, suna buƙatar abubuwan ƙawa da ado.
Kai buƙatun mutane ba sa taɓa ƙarewa.
Shi ya sa ko a cikin masu kuɗin ma, waɗanda s**a fi kuɗi sune waɗanda suke warware matsaloli mafiya girma ko kuma ga mutane masu yawa.
Don haka a kullum ku riƙa tuna cewa ba ku da matsalar kuɗi, babu wanda yake da matsalar kuɗi a duniya, saidai matsalar kasa samar da ƙima ko abin buƙata ga mutane.
Idan ka farka ko kika farka daga barci babu ko sisi, to ku tambayi kanku, wace irin matsala zan iya warware wa mutane a yau ko gobe don karɓe kuɗin dake hannunsu?
Daɗin abun shi ne matsaloli ba sa taɓa ƙarewa a duniya. A kullum wata tana buƙatar zuwa kitso ko yin kwalliya, motar wani zata yi faci, wani kuma zai yi rashin lafiya.
Wani zai faɗo daga bishiya ya karya haƙarƙari, kamar yadda wani kuma zai tafi yawon buɗe ido.
Wani