07/08/2026
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya ce za a iya kawo karshen matsalolin Najeriya cikin shekaru uku
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Dr. Prince Adewole Adebayo, ya bayyana cewa za a iya magance matsalolin rashin tsaro, cin hanci da rashawa da kuma matsin tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta cikin shekaru uku, idan aka zabi shugabanni masu kwarewa da gaskiya.
Adebayo ya bayyana hakan ne a taron Arewa Awareness Summit on Unity Against Insecurity da aka gudanar a Kaduna, inda ya ce matsalolin kasar sun dade ne saboda rashin kyakkyawan shugabanci.
Ya ce hanyoyin magance matsalolin Najeriya a bayyane suke, abin da ake bukata kawai shi ne shugabannin da za su mayar da hankali wajen samar da mafita.
Dan takarar SDP ya kuma bayyana Arewacin Najeriya a matsayin ginshikin makomar kasar, yana mai cewa yawan al’umma da dimbin albarkatun kasa da yankin ke da su za su iya zama babbar hanyar bunkasa tattalin arziki idan aka samu shugabanci nagari.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da kada su dauki kansu a matsayin marasa karfi, domin dimokuradiyya ta ba su damar zabar shugabannin da za su magance matsalolinsu.