DGL Hausa

DGL Hausa DGL Hausa – Duniyar Labarai kafar yada labarai ce ta zamani da ke kawo sahihai kuma ingantattun labarai cikin harshen Hausa.
(1)

A yau Litinin Sifaniya da Portugal za su fafata a zagayen ƴan 16 na Gasar Kofin Duniya.Ronaldo dai na da burin cin kofin...
06/07/2026

A yau Litinin Sifaniya da Portugal za su fafata a zagayen ƴan 16 na Gasar Kofin Duniya.

Ronaldo dai na da burin cin kofin duniya, kofin kaɗai da ya gagare shi zuwa yanzu yayin da shi ma Yamal ke harin kofin.

Yadda ƴan Brazil ke mamakin fitar da su daga gasarcin kofin duniya📷 Reuters
06/07/2026

Yadda ƴan Brazil ke mamakin fitar da su daga gasarcin kofin duniya

📷 Reuters

Mulkin Tinubu cike ya ke da rikici - Atiku Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce gwamnatin S...
06/07/2026

Mulkin Tinubu cike ya ke da rikici - Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kara fuskantar zarge-zargen badakala fiye da mayar da hankali kan gudanar da mulki.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce cece-kucen da s**a dabaibaye abin da ake kira Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) na nuna yadda ake yawan samun batutuwan da ba a warware ba a gwamnatin Tinubu.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya zargi gwamnatin da nuna son kai wajen gudanar da bincike kan zarge-zargen cin hanci da rashawa, yana mai cewa ana saurin daukar mataki idan wadanda ake zargi ba su da karfin siyasa, amma idan lamarin ya shafi masu kusanci da gwamnati, binciken kan tsaya cik.

Ya kuma ambaci batutuwan da s**a shafi dakatar da tsohuwar ministar jin kai, zarge-zargen satar danyen mai, kashe kudaden gyaran matatun mai, da kuma tambayoyi kan ayyukan NNPC a matsayin misalan batutuwan da har yanzu ba a yi musu cikakken bayani ba.

Atiku ya bukaci Shugaba Tinubu ya fito ya yi cikakken bayani kan wadannan batutuwa da kuma wasu cece-kuce da s**a shafi tarihinsa, yana mai cewa gaskiya da rikon amana su ne ginshikin shugabanci nagari. Ya gargadi cewa ci gaba da yin shiru kan irin wadannan zarge-zarge zai kara raunana amincewar jama'a da gwamnati.

Yau ce ranar da aka kebe a matsayin ranar sumbata ta duniya.Wani bincike ya nuna cewa dabbobi na kiss amma ba da niyyar ...
06/07/2026

Yau ce ranar da aka kebe a matsayin ranar sumbata ta duniya.

Wani bincike ya nuna cewa dabbobi na kiss amma ba da niyyar sha'awa ba, kawai suna yi ne don isar da wani sako a tsakaninsu.

Wane sako kiss ke isarma ?

Alƙalin wasa ɗan ƙasar Somaliya, Omar Artan wanda aka hana shi bizar Amurka don gasar cin kofin duniya, ya samu karramaw...
30/06/2026

Alƙalin wasa ɗan ƙasar Somaliya, Omar Artan wanda aka hana shi bizar Amurka don gasar cin kofin duniya, ya samu karramawa da jinjina daga hukumar Kuweït.

A kwanakin baya ne dai aka gudanar da wasan ƙarshe na cin kofin Kuwait tsakanin Kuwait SC da Al Qadsia inda Omar ɗin ne ya alƙalanci wasan.....

Me zaku ce?

Mun yi nasarar hallaka  yan ta’adda 199 a farmaki guda a Nijeriya - Gwamnatin AmurkaMe za ku ce?
30/06/2026

Mun yi nasarar hallaka yan ta’adda 199 a farmaki guda a Nijeriya - Gwamnatin Amurka

Me za ku ce?

30/06/2026

LABARI MAI SOSA RAI

Shin zaman Zina da mijin diyar ne yafi muni ko auren mijin diyar bayan yayi mata ciki ne yafi muni??

Daga karshe
KU baiwa diyar shawara

Da ɗumi-ɗumi: Kotu Ta Sake Bai Wa Omoyele Sowore Beli, Ta Gindaya Naira Miliyan 200 Da Mutane Biyu a Matsayin Masu Tsaya...
30/06/2026

Da ɗumi-ɗumi: Kotu Ta Sake Bai Wa Omoyele Sowore Beli, Ta Gindaya Naira Miliyan 200 Da Mutane Biyu a Matsayin Masu Tsaya masa.

Wata kotu ta sake bai wa fitaccen ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, , beli a shari'ar da ake yi masa.
Kotun ta amince da bayar da belin Sowore kan kuɗi Naira miliyan 200, tare da sharadin cewa dole ne ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa a matsayin masu tabbatar da belin.

Haka kuma, kotun ta umarci Sowore da ya miƙa fasfo ɗinsa na tafiya ƙasashen waje ga kotu har zuwa lokacin da za a kammala sauraron shari'ar.

Ana sa ran wannan hukunci zai ba Sowore damar ci gaba da kare kansa daga waje yayin da ake ci gaba da sauraron shari'ar.

Address

No. 45 Tudun Wada Kaduna
Sokoto
58973

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DGL Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DGL Hausa:

Shortcuts

Share

Category