Suhaibu Yusuf Sambo

Suhaibu Yusuf Sambo Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Suhaibu Yusuf Sambo, Digital creator, Kaduna.

Wannan hanya ta Social Media wato hanyar Sada Zumunta, hanyace ta yada manufa ga Al'umma.Misali; Ra'ayi, Shawara, Labarai, Ilmantarwa, Luratarwa kai harma da Nishadantarwa.

08/04/2025

Assalamu Alaikum
Talata 10-10-1446 Hijiriyya
08-04-2025 Miladiyya

Haduwar Zukatan Al'ummah Wuri Guda, Shine Mafita Kuma Shine Mafi Dacewa Maimakon Rabuwa Akan Son Zuciya.

Komin Zakin Rabuwa - Dacin Haduwa Yafi Shi.

Ina Godiya Ga Allah Madaukakin Sarki Mahaliccin Kowa Da Komai, Kuma Ina Rokon Allah Yabani Damar Isar Da Wannan Sako Zuwa Ga 'Yan Uwa Na Musulmi, Musamman Iyayenmu Malamai Da 'Ya'Yan Wannan Kungiya Mai Albarka.

Zanyi Amfani Da Wannan Damar Domin Nusantar Da Junanmu Muhimmancin Haduwar Kan Al'ummar Musulmi Wuri Guda.

Haduwa, Umurnin Allah Ne, Shine Abinda Allah Keso.

Rabuwa, Allah Baya Tareda Wannan Manufar Ko Kadan.

Tsakani Da Allah Rabuwar Wannan Kungiya Mai Albarka Wanda Iyayenmu Masu Albarka S**a Assasa, Abin Yana Matukar Damunmu.

Ina Nufin Mu 'Ya'Yan Wannan Kungiyar Na Dukkan Bangarori Biyun.

Mun Taso Munga Iyayenmu Gwanin Ban Sha'awa Kansu Hade, Manufarsu Daya Gameda Aikin Addini, Sai Kuma Daga Baya Muka Ga Al'amura Sun Sauya Wanda Bamuso Faruwar Hakan Ba.

A Matsayinmu Na 'Ya'Yan Wannan Kungiya;
.Haduwar Kungiyar Wuri Guda, Dankon Zumunci Yana Karuwa A Tsakanin Junanmu Da Sauran Mabiya Tamkar Uwa Daya.

Sunnah Zata Kara Karfi Acikin Fadin Kasar Da Sauran Kasashen Da Suke Makwabtaka Da Ita.

Kungiyar Zatayi Karfin Da Zuwa Nan Gaba, Babu Abinda Hukuma Zatayi, Face Sai Ta Nemi Shawarar Malaman Cikinta Da Shugabannin Kungiyar.

Kimar Kungiyar Zai Kuma Karuwa A Idon Shugabanni Da Manyan Sarakunan Musulunci Fiye Da Shekarun Baya.

Dunkulewar Kungiyar Akan Shugabanci Ko Murya Daya, Hakan Zai Firgita Dukkan Masu Da'awar Babu Kungiya Da 'Yan Bidi'ah.

Azzaluman Shugabanni Hankalin Su Zai Tashi Kwarai Da Gaske.

Kuma Masu Da'awar Babu Mazhaba, Suma Hankalinsu Zai Matukar Tashi Kwarai Da Gaske.

Ruhi Da Karfin Addinin Musulunci Da Sunnah Zai Dawo A Fadin Kasar.

Zamu Zamto Tamkar Gwamnati Domin Hadin Kai Ya Wuce Tunanin Mai Tunani, Karfi Ne Daga Allah.

Mai Yuwuwa Zuwa Nan Gaba (Matukar An Hadu) Mabiyan Kungiyar S**afa Gwamnati (Wasu Su Zama Gwamnoni Wani Yazama Shugaban Kasa).

Amma Matukar Muna Ganin Cewar Rabuwar Tafi Mana Haduwar, To Wallahi Mun Dungi Ganin Kaskanci Mabanbanta Kenan.

Kuma Abinda Muke Ganin Cewar Munfi Karfinshi, To Sai Mun Zubda Hawaye Sosai Akan shi.

Muna Dai Ganin Yanda Ake Zagin Malamai Gami Da Cin Mutunci Da Akeyi Gare Su, An Raina Su, Babu Mai Taimakon Su Sai Allah.

Iyayen Mu Malamai, Don Allah Ku Tausaya Mana Ku Hade Kanku Wuri Guda, Domin Kauracema Wancan Kaskancin.

Mutuwa Akeyi Kullun, Mutuwa Tana Ta Yi Muku Dauki Dai Dai.

Don Allah Ku Taimake Mu Kada Ku Barmu A Gadar Zare.

Fatanmu Kukuma Hada Kanku/Zukatanku Wuri Guda, Domin Mu Kuma Ganinmu Acikin Farin Cikin Da Muke Fata.

Dukda Dai, Shekaru Kusan Shida Da S**a Gabata, Munyi Yunkurin Samar Da Zumunta Mai Karfi A Tsakanin Junanmu, Ina Nufin 'Ya'yan Malaman Kungiyar IZALA Na Dukkan Bangarori Biyu A Fadin Jihohi Da Kasa Baki Daya, Kuma Tabbas Munga Tasirin Haka.

Domin Har Yanzu Muna Tare Da Junanmu Kuma Muna Tattauna Al'amuran Da Zai Kaimu Gaci.

Kuma Da Yardar Allah, Zamuyi Abinda Zamu Iyayi Wajen Ganin Wannan Kungiya Ta Kuma Hadewa Wuri Guda.

Lokaci Bayan Lokaci, Mukan Ziyarci Gidajen Iyayen Mu Malamai Da Suke Raye, Har Da Gidajen Wadanda S**a Koma Ga Allah.

Muna Haduwa Da 'Yan Uwanmu Sannan Muna Yiwa Junanmu Fatan Alkhairi.

Iyayenmu Malamai Da Suke Raye A Yau, Mafi Yawancin Su Sun San Da Wannan Tafiyar, Kuma Babu Wanda Yasoki Tafiyar Acikin Su. Dukkansu Sun Goyi Bayan 'Ya'Yansu Suma Su Kasance Acikinta.

Duk Wani Fitaccen Malami Kuma Shugaba A Wannan Kungiyar, Muna Tare 'Ya'Yanshi A Wannan Tafiyar.

A Matsayin Mu Na 'Ya'Yan Wannan Kungiyar;

Nan Bada Dadewa Ba, Akwai Yunkurin Wa'azin Kasa Da Kasa Da Zamu Gayyaci Al'ummar Musulmi A Hedikwatar Sunnah, Filin Eidin Masallacin Sarkin Musulmi Bello Dake Jihar Kaduna Domin Baiwa Mara Da Kunya.

Dukkan 'Ya'Yan Manyan Malaman Kungiyar IZALA Na Dukkan Bangarori Biyunnan Suna Tareda Mu Akan Wannan Yunkurin.

Mune Zamuyi Wa'azin, Sannan Zamu Gayyaci Wasu Kadan Daga Cikin Iyayenmu Malamai Kuma Dattawan Kungiyar Domin Su Saurara Da Kunnuwansu.

Daga Karshe Susanya Mana Albarka.

Allah Muke Roko Yataimake Mu, Yabamu Nasara Mai Karfi.

Iyayen Mu Malamai;

- Allah Yataimake Ku
- Allah Yakara Muku Lafiya
- Allah Yakara Muku Basira
- Allah Yakara Muku Son Juna
- Allah Yakara Nisanta Shaidan Daga Gare Ku.
- Allah Yakara Daukaka Mana Ku.
- Allah Yabaku Gidan Aljannah Sakamakon Karantar Da Al'ummah Da Kukeyi Kyauta.
- Wandanda S**a Koma Ga Allah, Muna Addu'ah Allah Yajinkansu Da Rahama.
- Allah Yagafarta Musu Zubansu.
- Allah Yakai Haske Cikin Kaburburansu.
- Allah Yayi Musu Tukwici Da Samun Shiga Gidan Aljannah, Ameen.

Haduwar Zukatan Al'ummah Wuri Guda, Shine Mafita Kuma Shine Mafi Dacewa Maimakon Rabuwa Akan Son Zuciya.

Komin Zakin Rabuwa - Dacin Haduwa Yafi Shi.

 Wannan Itace Kalmar Da Alh Auwal Yusuf Sambo Yasaba Fadi A Duk Lokacin Da Yaga Wani Abu Wanda Ya Burge Shi.Yau Ga Katin...
03/04/2025



Wannan Itace Kalmar Da Alh Auwal Yusuf Sambo Yasaba Fadi A Duk Lokacin Da Yaga Wani Abu Wanda Ya Burge Shi.

Yau Ga Katin Daurin Auren Babbar 'Yarsa Mace (BASMA) Da Za'ayi Insha Allahu Da Dan Uwa Umar, Kuma Allah Ya Dauke Abinshi.

Ya Allah Ka Jikansa Da Rahama.
Allah Muke Roko Yasa Muga Wannan Lokaci Cikin Koshin Lafiya.

05/03/2025

Ramadan Day 04

Ranar Laraba
05/03/1446.
05/09/2025.

Tafsirin Alqur'ani Mai Girma (Audio) Daga Bakin Ustaz Suhaibu Yusuf Sambo

Tareda Hafiz Yakubu Ilyas Rigachikun.

Daga Masallacin Dake Kofar Gidan Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachikun.

Allah Yabada Ikon Sauraro na Fahimta, Ameen.

Assalamu Alaikum15 Sha'aban, 1446.14 February, 2025.Ina Farin Cikin Sanar Da 'Yan Uwa Da Abokan Arzi Nadin Sarauta Da Za...
14/02/2025

Assalamu Alaikum
15 Sha'aban, 1446.
14 February, 2025.

Ina Farin Cikin Sanar Da 'Yan Uwa Da Abokan Arzi Nadin Sarauta Da Za'ayi Min Na "Mallamawan Kunkelin Zazzau".

Rana: Ranar Lahadi 16-02-2025.
Wuri: Fadar Mai Girma Kunkelin Zazzau, Rigachikun Kaduna.
Lokaci: 10:30 am.

Allah Yabada Ikon Halarta, Ameen.
Addu'ar Ka/Ku Tana Da Matukar Muhimmanci A Garemu.

Address

Kaduna

Telephone

08166361293

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Suhaibu Yusuf Sambo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Suhaibu Yusuf Sambo:

Share