30/05/2025                                                                            
                                    
                                                                            
                                            AL'UMMAR ƘARAMAR HUKUMAR NASARAWA, SUN GAMSU DA AYYUKAN  WAKILCIN DA HONOURABLE HASSAN SHEHU HUSSAINI, A CIKIN SHEKARU BIYU 
Daga Ibrahim Muhammad.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Nasarawa, wato Honourable Hassan Shehu  Hussain, daya ne daga yan majalisu da ya ke samun kyakkyawan shaida na gudanar da ayyuka daban daban a  mazabarsa.
Al'ummar karamar Hukumar Nasarawa har da yan adawa, suna da kyakkyawan shaida a kansa na gudanar da ayyuka da  yake  yi musu a fannoni  daban daban,  da babu mai musun haka duk da cewa wannan  shine zuwansa  majalisar tarayya na farko.
Sannanen abu ne a kundin tsarin mulkin Nijeriya, babban aikin dan majalisa  a kowane mataki  shine ya  kai kudiri akan abinda ya shafi cigaban al'umma ayi duba akan  muhimmancinsa da amfaninsa ga cigaba   ayi masa karatu ayi doka  akai ko a yan kwanakin nan ya gabatar da kudirin na neman Gwamnatin  tarayya ta kawo daukin gaggawa ga masana'antun Kano ta tallafa musu da inganta harkar wutar lantarki.
Sannan akwai kudirin da yakai domin bunkasa Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da kuma samar da cibiyar kula cutukan zuciya a Asibitin.
Kai irin wannan kudiri ba kowane dan majalisa  ne ke iya  mikewa ya yi ba ,hatta yan majalisu da s**a  jima suna zuwa majalisar   wasu basu taba wani motsi don gabatar da wani kuduri ba,sanannen abu ne ga al',ummar jihar  Kano  dan majalisa tarayya  mai wakiltar karamar Hukumar Nasarawa Hon.Hassan Shehu  Husaini yana daga cikin wadanda s**a ciri tuta wajen  kai kudiri farfajiyar  majalisar  tarayya akan abinda  ya shafi al'ummarsa da cigaban jihar Kano.
Zuwan sa  majalisa  don wakiltar alummar karamar hukumar Nasarawa ya  shigar da kudurori da dama  da s**a tsallake karatu har s**a tabbata.
A bangaren  ayyuka kuwa irin gudunmawar da yake bayarwa a  bangaren Ilimi ya  haɗa da samawa matasa Maza da Mata gurbi a  manyan makarantu  da biya musu kudaden makarantun a kwalejin ilimi na saadatu Abubakar Rimi  da  Kano polytechnic  da collage of art and remedial studies
School of health and technology.
dalibai 600 sun ci gajiya.Ya kuma biya  kudin  jarabawar WAEC,NECO ,JAMB  na mutun 1800..Sannan ya dauki  nauyin karatun  marayu 150 tun daga makarantar renon ' nursery' har zuwa makarantar gaba da sakandire..
Haka fannin samar da  Ruwan sha ya gina Rijiiyoyin burtatse  guda 30 a mazabun  karamar  hukumar  Nasarawa 11.Ya samar da  tituna 
 masu tsawan kilomita  Biyu-biyu  a mazabun Gama da   tudun wada.Haka a mazabar Gawuna,
da tudun murtala da  mazabar hotoran kudu ya samar da tituna masu tsawon kilomita daya.
A bangaren  inganta samar  da wutar lantarki  ya samar tiransifoma  na wuta  mai karfin KW 500  a  mazabar Gwagwarwa da  mazabar hotoran arewa  da mazabar hotoron kudu.
A  bangaren gine -gine ya gina rukunin  ajujuwa 3  a makarantar. firamare  na lLadanai  a mazabar hotoron Arewa .ya  samar da gini   mai ajujuwa Biyu a  makarantar community school a unguwar  Tishama,   Hotoron Arewa ya 
 gina  ajujuwa Biyu  a makarantar sakandire da ke Dakata.
A  bangaren  inganta lafiya  ya samar da ginin Asibitin sha ka tafi "Clinic  hospital"  da kayan aiki a unguwar Yandodo Hotoran Arewa.Sannan ya samar da fitilu masu amfani da hasken Rana  a dukkanin mazabu 11 na  karamar hukumar Nasarawa.
Hon.Hassan Shehu  Husaini a karkashin wannan wakilcin nasa ya  samawa matasa aikin yi a mataki na  Gwamnatin jiha dana tarayya  kimanin mutum  20.
Sannan yana bayar da tallafi domin Gina rayuwar alumma a bangarori  da dama da  matasa maza da  mata  da iyaye  da dama s**a anfana  sannan a cikin watan azumin da na sallah ya tallafawa  al umma da  abubuwan more rayuwa  ta fannoni daban daban domin gina rayuwar su.
Duk wadannan ayyuka da dan majalisar tarayya  na Nasarawa Hon.Hassan Shehu Husaini  yake sauke nauyi ne na al'ummar da s**a zabe shi ,wanda a ma'auni na adalci yana yin abinda ya dace da ya shafi cigaban alummar sa..
Wasu yan siyasa sun ce Idan aka samu wasu na kalubalantar sa a iya cewa suna yine  kawai saboda wani abu   da ya haɗa su dashi akan kansu, amma ba don gazawa a wajen a sauke nauyin wakilci da al'ummar  ƙaramar hukumar Nasarawa s**a dora masa ba a majalisar tarayya.
Muhimmin aikinsa da doka ta tanada masa shine kai kudiri, yin ayyukan alummar sa  kuma yana yi  suma masu s**ar sa,  basa zarginsa da gazawa a wannan bangaren..
Sai da Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jinjinawa kokarin da dan majalisar yake a  wani taro na bude hanyoyi da dan majalisar yayi har yayi   jan hankali.ga  sauran yan majalisu suyi koyi dashi