Ayau News

Ayau News Your Number 1 source for instant Hausa breaking news and exclusive stories -Fresh & Fair! Contact us : 2347087776767 visit our website at www.ayau.ng
(9)

A jiya Asabar an nada matar shugaban kasa Oluremi Tinubu sarautar gargajiya Ku cinki a wace jihar ko masarautar?
10/08/2025

A jiya Asabar an nada matar shugaban kasa Oluremi Tinubu sarautar gargajiya

Ku cinki a wace jihar ko masarautar?

MU TATTAUNA: Yanzu da Rahama Sadau ta shiga daga cikin, wa kuke hasashen za ta maye gurbinta a Kannywood?
10/08/2025

MU TATTAUNA: Yanzu da Rahama Sadau ta shiga daga cikin, wa kuke hasashen za ta maye gurbinta a Kannywood?

KO KUN SAN: “Idan kun haura sama da shekara 40, to ku guji shan abubuwan sanyi.” -inji Masana
10/08/2025

KO KUN SAN: “Idan kun haura sama da shekara 40, to ku guji shan abubuwan sanyi.” -inji Masana

HAKKOKIN ANNABI MUHAMMAD ﷺ AKAN AL’UMMARSA (20)1. Imani da shiآمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ النَّبِيِّ الأُمِّيِّ (A‘rāf...
10/08/2025

HAKKOKIN ANNABI MUHAMMAD ﷺ AKAN AL’UMMARSA (20)

1. Imani da shi

آمِنُوا بِاللَّهِ وَرَسُولِهِ النَّبِيِّ الأُمِّيِّ (A‘rāf:158)

“Ku yi imani da Allah da Manzonsa Annabi marar karatu.”
Bayani: Wannan shi ne hakkin farko — dole ne musulmi ya gaskata shi Annabi ne na gaskiya kuma ya karɓi abin da ya zo da shi.

2. Ƙaunarsa fiye da kowa

Hadisi: “Ba ya cikawa imanin wani daga cikinku har sai na fi masa so fiye da iyayensa, ‘ya’yansa da dukkan mutane.” (Bukhari, Muslim)
Bayani: Ƙaunar Annabi tana sama da ta duk wani mutum, domin shi ne jagora zuwa aljanna.

3. Biyayya ga umarninsa

وَمَا آتَاكُمُ الرَّسُولُ فَخُذُوهُ (Ḥashr:7)

“Abin da Manzo ya baku, ku karɓa.”
Bayani: Yin biyayya ga umarnin Annabi biyayya ce ga Allah.

4. Guje wa abin da ya hana

وَمَا نَهَاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا (Ḥashr:7)

“Abin da ya hana ku, ku hanu.”
Bayani: Haramcin Annabi shi ne haramcin Allah, dole ne a bar shi.

5. Girmama shi

لَا تَرْفَعُوا أَصْوَاتَكُمْ فَوْقَ صَوْتِ النَّبِيِّ (Ḥujurāt:2)

“Kada ku ɗaga muryoyinku sama da muryar Annabi.”
Bayani: A rayuwarsa da bayan rasuwarsa, ana girmama shi cikin magana da hali.

6. Kiyaye sunnarsa

Hadisi: “Duk wanda ya tsarkake sunnata, yana ƙaunata.” (Tirmidhi)
Bayani: Yin aiki da sunnah alama ce ta ƙaunar Annabi da tsarkin niyya.

7. Kare shi daga ƙarya

Hadisi: “Duk wanda ya ƙirƙiri ƙarya a kaina, ya tanadi wurinsa a wuta.” (Bukhari, Muslim)
Bayani: Haramun ne a faɗi hadisi ƙarya da sunansa, saboda ɓata addini ne.

8. Yawan salati a kansa

إِنَّ اللَّهَ وَمَلَائِكَتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ (Aḥzāb:56)

“Lallai Allah da Mala’ikunsa suna yi wa Annabi salati.”
Bayani: Yin salati yana ƙara darajarsa, kuma Allah yana mayar da amsa ga mai yi.

9. Taimaka masa bayan rasuwarsa

Hadisi: “Duk wanda ya yi jihadi saboda kare addinina, Allah zai tsarkake shi.”
Bayani: Taimakon addini bayan wafatinsa kamar kare martabarsa da yada sunnarsa.

10. Kula da al’ummarsa

Hadisi: “Misalin ni da ku kamar mutum ne ya kunna wuta, kwari suna ta fadawa ciki, ni kuma ina rikice muku daga wuta.” (Muslim)
Bayani: Yana nuna yadda Annabi yake son mu tsira daga wuta.

11. Ƙaunar Ahlul Baiti

قُل لَّا أَسْأَلُكُمْ عَلَيْهِ أَجْرًا إِلَّا الْمَوَدَّةَ فِي الْقُرْبَىٰ (Shūrā:23)

“Ka ce: Ba na neman wata sakayya sai ƙaunar ‘yan uwana na jini.”
Bayani: Iyalin Annabi suna da matsayi na musamman a gare mu.

12. Ƙaunar Sahabbansa

Hadisi: “Kada ku zagi Sahabbaina. Da ku ba da zinari har girman Uhud, ba zai kai muddin daya daga cikinsu ba.” (Bukhari, Muslim)
Bayani: Sahabbai sun yi jihadi da rayuka don isar mana da addini.

13. Ziyartar masallacinsa

Hadisi: “Ana tafiya ne kawai zuwa masallatai uku: Masjid al-Haram, Masjidina, da Masjid al-Aqsa.” (Bukhari, Muslim)
Bayani: Ziyarar masallacinsa ibada ce mai lada.

14. Ziyartar kabarinsa

Hadisi: “Duk wanda ya yi ziyara gare ni bayan rasuwata, kamar ya ziyarce ni a raye.” (Dar Qutni)
Bayani: Ana yin wannan da ladabi da tsarkakakkiyar niyya.

15. Rarraba iliminsa

Hadisi: “Ku isar da saƙona ko da aya ɗaya ce.” (Bukhari)
Bayani: Dole ne mu yada koyarwarsa cikin hikima da gaskiya.

16. Kare addinin daga bidi’a

Hadisi: “Ku guji sabbin abubuwa (a addini), domin kowanne bidi’a ɓata ce.” (Abu Dawud, Tirmidhi)
Bayani: Duk abin da bai zo daga shari’a ba a addini, to an haramta.

17. Aiwatar da shari’arsa

فَلَا وَرَبِّكَ لَا يُؤْمِنُونَ حَتَّىٰ يُحَكِّمُوكَ (Nisā’:65)

“Kamar yadda Ubangijinka ya rantsa, ba za su yi imani ba sai sun yarda da kai a matsayin mai hukunci tsakaninsu.”
Bayani: Yin hukunci da shari’ar Annabi wajibin musulmi ne.

18. Jin daɗin ambaton sa

Hadisi: “Ku yi salati a kaina, domin salatinku tana zuwa gare ni.” (Abu Dawud)
Bayani: Ambaton sa yana kawo albarka da rahama.

19. Hana ɓatanci gare shi

إِنَّ الَّذِينَ يُؤْذُونَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ لَعَنَهُمُ اللَّهُ (Aḥzāb:57)

“Lallai waɗanda suke cutar da Allah da Manzonsa, Allah Ya la’ance su.”
Bayani: Cutar da Annabi ta hanyar magana ko aiki babban zunubi ne.

20. Yi masa koyi

لَّقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ (Aḥzāb:21)

“Lallai akwai misali mai kyau a gare ku a cikin Manzon Allah.”
Bayani: Halin Annabi shine mafi kyau, kuma shi ne misalinmu a rayuwa.

Abu Ja'afar Assunny ✍️

KO KUNSAN: Naira dubu Dari (N100k) a yanzu 2025 (zamanin Tinubu) bata iya sayen abunda Naira Dubu Takwas (N8k) za ta say...
09/08/2025

KO KUNSAN: Naira dubu Dari (N100k) a yanzu 2025 (zamanin Tinubu) bata iya sayen abunda Naira Dubu Takwas (N8k) za ta saya a shekarar 2006!

-inji hukumar kididdiga ta StatiSense

Wato kenan Naira dubu 8 a shekarar 2006 ta fi Naira dubu 100 a yanzu (2025) daraja...

Me zaku ce?

RAI DANGIN GORO: Sojojin Najeriya sun saka kida suna rausayawa domin shakatawa da nishadantar da kansuME ZAKU CE?
09/08/2025

RAI DANGIN GORO: Sojojin Najeriya sun saka kida suna rausayawa domin shakatawa da nishadantar da kansu

ME ZAKU CE?

Shanun daji ya yi ajalin wani attajiri da ya taso daga Amurka ya zo Afrika domin yin farautar Shanun DaninAbinka da kara...
09/08/2025

Shanun daji ya yi ajalin wani attajiri da ya taso daga Amurka ya zo Afrika domin yin farautar Shanun Danin

Abinka da karar kwana ashe Shanun Dajin ne zai yi ajalin Asher Watkins, dan shekara 52, wanda ya taso takanas daga Amurka zuwa kasar South African domin kafa tarihi da neman suna ta hanyar yin farautar Shanun daji. Ance dabbar ta mamayi Asher ta yi masa tunkurin bazata wanda yayi sanadiyyar rasa ransa

Me zaku ce?

Duk da karya masa hannu, rundunar yan sandan Najeriya ta ce bata ci zarafi ko azabtar da dan Gwagwarmaya Omoyele Sowore ...
09/08/2025

Duk da karya masa hannu, rundunar yan sandan Najeriya ta ce bata ci zarafi ko azabtar da dan Gwagwarmaya Omoyele Sowore ba.

A daren jiya ne dai rundunar ta saki Dan Gwagwarmayar bayan shan s**a da Allah-wadai daga manya da kanan yan Najeriya.

Tun a ranar farko Omoyele Sowore ya bayyana cewa yan sanda sun karya mashi hannun kuma har ya fitar da hotunan sannan ya ce an kaishi wajen ajiya an kulle shi tare da gaggan barayi da yan ta'adda su fiye da 30

Me zaku ce?

Mahaifin mu (mahaifin Rahama Sadau ) ne ya bar mata wasiyyar ta dage ta yi aure kuma yanzu ta cika wasiyyar  -inji kanni...
09/08/2025

Mahaifin mu (mahaifin Rahama Sadau ) ne ya bar mata wasiyyar ta dage ta yi aure kuma yanzu ta cika wasiyyar -inji kannin ta

Ta auri mai sunan babanta Ibrahim Garba

Wane fata kuke mata ?

Bismillah, Allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.Addu'ar saduwa da iyali ne, dan Allah ku riƙa...
09/08/2025

Bismillah, Allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.

Addu'ar saduwa da iyali ne, dan Allah ku riƙa daurewa kuna yinta dan gujewa haihuwar irin yaran can masu ƙwacen waya, da masu goya musu baya.

Daga Mamuda Wappa

Lokacinda Saleh Bala abokin aikin jaruma Rahama Sadau  ya zo mata da goro yana yi mata albishir cewa an daura aurenta da...
09/08/2025

Lokacinda Saleh Bala abokin aikin jaruma Rahama Sadau ya zo mata da goro yana yi mata albishir cewa an daura aurenta da Ibrahim Garba

Auren dai ya zo wa mutane bazata har aka zaci ko auren film ne kafin daga bisani ita da kanta ta shaida cewa "tabbas auren gaske ne" kuma tuni abokan aikinta irinsu Ali Nuhu da sauransu s**a taya ta murna

Auren Rahama ya baku mamak kuwa?

DA DUMI-DUMI: An daura auren jaruma Rahama Sadau da angonta Ibrahim Daraktan jarumar ya shaidawa Ayau News cewa auren ga...
09/08/2025

DA DUMI-DUMI: An daura auren jaruma Rahama Sadau da angonta Ibrahim

Daraktan jarumar ya shaidawa Ayau News cewa auren gaske ne kuma sunan mijin Ibrahim Garba

Wane fata kuke mata?

Kuyi following din Ayau News domin samun karin bayani

Address

A1 And A2 , Legacy Plaza 218, Magadishu Layout, Ahmadu Bello Way, Kaduna North
Kaduna
800212

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ayau News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ayau News:

Share