
24/09/2022
Hukumar yansandan jahar Lagos ta k**a wata mota dauke da Alburusai
Hukumar yansandan jihar ta lagos ta k**a wasu motoci guda biyu wadan da ke dauke da Harsasai masu rai, mashin gudu uku wadan da aka kwance a poromope estate, ijede Road , Ikorodu dake jihar lagos.
A wani bayani da hukumar ta sama hannu ta bakin jami’i mai hudda da al’umma na hukumar , Benjamin Hundeyi a Ranar asabar da ta gabata, yace hukumar sunyi wani kamu.
Hundeyin yace, “ binciken farko ya tabbatar da wadan da ake zargi, Tukur Abdullahi mai shekaru 35, mu’azu Telim mai shekaru 50 da kuma Dahiru Idris mai shekaru 36 suna kam hanyarsu ta zuwa jihar katsina.
Hukumar tayi nasarar k**a Kayan laifin da kuma babur mai lamba KM. 438 YK da mai lamba KM 394 XK An daukesu zuwa Lagos state command Headquarters da ke ikeja domin kara tsaurara bincike.