19/10/2025
Matasan Arewa Sun Shirya Zanga-Zanga Kan Nuna Masu Saniyar Ware.
Wata kungiya ta matasa mai suna Matasan Arewa Youth Development Initiative ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ke nuna sakaci da raini ga matasa ta hanyar kin ba su gurbi a cikin mulki.
Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a Kano a ranar Alhamis, shugaban kungiyar na kasa, Abba Muhammad, ya ce kungiyar, wacce ta kunshi matasan Arewa da s**a taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a zaben 2023, ta kammala shirin fara zanga-zangar lumana da zagayen wayar da kai a jihohin Arewa 19.
Ya ce manufar wannan zanga-zanga ita ce nuna rashin jin dadin yadda gwamnati ta yi watsi da matasa, tare da fadakar da al’umma kan muhimmancin wakilcin matasa da hada su cikin harkokin mulki da ci gaban kasa.
“Mu ne muka yi yakin neman zabe, muka tashi tsaye muka tabbatar da nasara. Amma yanzu kusan shekaru biyu kenan cikin wannan gwamnati, matasan Arewa da s**a tsaya a gaba a lokacin zabe an yi watsi,” in ji Abba.
Ya kara da cewa kungiyar na nuna damuwa da yadda Shugaban kasa da jam’iyyar APC s**a kasa cika alkawuran da s**a dauka ga matasa, musamman wajen muk**ai da tsare-tsaren gwamnati.
“Ba mu neman tallafi ko kyauta,” in ji shi. “Abin da muke nema shi ne a gane muhimmancin matasa, a ba su dama su ba da gudunmawa wajen gina kasa.”
Abba ya bayyana cewa zanga-zangar lumana da zagayen wayar da kai zai fara daga jihar Kano a karshen wannan watan, kuma zai hada da tarukan tattaunawa da jama’a, hulda da kafafen yada labarai, da shirye-shiryen fadakarwa a kauyuka.
A cewar kungiyar, wannan mataki na da nufin ta da wayar da kai da kuma karfafa himmar siyasa a tsakanin matasan Arewa, tare da kira ga gwamnati da ta girmama rawar da matasa s**a taka a lokacin zabe da kuma hada su cikin tafiyar mulki.