AHMAD ALIYU LADAN

  • Home
  • AHMAD ALIYU LADAN

AHMAD ALIYU LADAN Shafin Tarihi Da Alamuran Yau Da Kullum

MAI MARTABA SARKIN ZZ YAU A ABUJA A Zauren Taro na Transcorp Hilton a Babban Birnin Tarayya, Abuja da safiyan yau a mats...
06/09/2024

MAI MARTABA SARKIN ZZ YAU A ABUJA

A Zauren Taro na Transcorp Hilton a Babban Birnin Tarayya, Abuja da safiyan yau a matsayinsa na Uban Taro Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR ya halarci bikin kaddamar da Manhajan Zamani na Tafe Da Gidanka (Mobile Application) da Na'uran Sadarwa domin saukake Hulda da Hukumar Kiyaye Haddurra na Kasa (FRSC).
Wannan sabbin Fasaha dai Sabon Shugaban Hukumar Kiyaye Haddura na Kasa Shehu Mohammed ya samar dasu domin samun ci gaba da kuma inganta hulda da Hukumar.

Ahmad Aliyu.

26/08/2024
Wannan shine layin da nake
26/08/2024

Wannan shine layin da nake

{WAKEN KASATA NAJERIYA}(1) Kasata Najeriya Ina yi muku gargadi            Kuzo muyi Muslim Tiket muhau Jirgin AnnabiDa S...
02/03/2023

{WAKEN KASATA NAJERIYA}

(1) Kasata Najeriya Ina yi muku gargadi
Kuzo muyi Muslim Tiket muhau Jirgin Annabi
Da Sunan Allah Daya!
Salati ga Nabiyyuna!
Sahabbai nasa na sako!
Da Wadanda suke bibiyarsu har ranar Taruwa!

(2) Kasata Najeriya Ina yi muku gargadi
Kuzo muyi Muslim Tiket muhau Jirgin Annabi
Ga Wasika budaddiya!
Ga Muslimin Najeriya!
Ga Siyasar Najeriya!
Kudan saurara kujini don za kuyi karuwa!

(3) Kasata Najeriya Ina yi muku gargadi
Kuzo muyi Muslim Tiket muhau Jirgin Annabi
Ga Siyasa yau ta matso!
Kungiyar Arna sunfito!
Sunci Mushe sun sha Giya!
Wai suna son Arna su Mulki duk 'Yan Najeriya!

(4) Kasata Najeriya Ina yi muku gargadi
Kuzo muyi Muslim Tiket muhau Jirgin Annabi
Nan Musulmai s**a zabura!
S**a ce Tinibun zamuyi!
Shida Kashim Muslim suke!
Muslim Muslim Shugabanmu harma da Mataimaki!

(5) Kasata Najeriya Ina yi muku gargadi
Kuzo muyi Muslim Tiket muhau Jirgin Annabi
Malamai Ala saka maku!
Kunfa sha s**a mai yawa!
Kunyi Jan Aikin Jinjina!
Allah sadaku da Jannatul Firdausi Gidan Kawa!

(6) Kasata Najeriya Ina yi muku gargadi
Kuzo muyi Muslim Tiket muhau Jirgin Annabi
Ya Sarakan Najeriya!
'Yan Siyasan Najeriya!
Har Matasan Najeriya!
Ku zo muyi Kuri'a mu zabi Muslim Muslim Tiket!

(7) Kasata Najeriya Ina yi muku gargadi
Kuzo muyi Muslim Tiket muhau Jirgin Annabi
Ba kasala ba damuwa!
Zamu je Kwanmu da Kwarkwata!
Don mu kayar da Mutan giya!
Jalla Allah zai taimakemu in mun yo kokari.

Ahmad Aliyu Ladan.....✍️

23/02/2023

(4): Ɗan takarar da zan zaɓa

A wannan fitowar, zan bayyana ɗan takarata haɗe da dalilan da ya sa zan zaɓe shi. Kuma zan kawo wasu daga cikin ƙorafin da wasu jama'a suke yi gameda shi, haɗe da tsokacina.

Kowa ya san matsalolin Najeriya a yau fanni-fanni ne. Amma na fahimci galibin matsalolin suna da alaƙa da karayar tattalin arzikin da ya same mu. Karayar tattalin arziki yana kawo taɓarɓarewar tsaro, ya illata harkar ilimi, ya kawo cikas a fannin kiwon lafiya, da sauran al'amuran rayuwa. Sai na fahimci gyaran Najeriya za'a faro shi ne daga ceto tattalin arzikin ƙasar.

Bayan na kalli ƴan takarar baki ɗaya, sai na ga cikinsu akwai wanda ya fi sauran kyakkyawar fahimta gameda tattalin arziki. Bugu da ƙari, har ya taɓa jagorantar wasu masana da s**a kawowa Najeriya sauyin yanayi a lokacin da ta taɓa samun karayar arziki fiye da shekaru 20 baya. Don haka na zaɓi wannan ɗan takarar a matsayin wanda ni Ibrahiym zan jefawa ƙuri'ata. Ɗan takarar kuwa shine Alhaji Atiku Abubakar, na jam'iyyar People's Democratic Party (PDP).

Ma'abota hankali sun koyi darasi mai yawan gaske a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa yau. Sun fahimci cewa baka cika-baki gameda ɗan siyasa, kace lallai zai yi kataɓus. Kai dai faɗi abubuwan da ka fahimta, kayi zaɓe, kayi addu'a. Amma shi kansa ɗan takara bai san yadda mulkinsa zai zama ba. Dalilin hakane zan bayyana iyakar abinda na gamsu da shi gameda Atiku Abubakar, ba tareda na cika baki ba cewa lallai idan ya samu Shugabanci zai maida ƙasar tamkar wata Ingila. A'a. Sanin wannan sai Allah, Wanda ya kaɗaita da sanin gaibu.

Waɗannan sune mafiya nauyin ƙorafe-ƙorafen da wasu jama'a suke yi gameda Atiku Abubakar, haɗe da abinda nake fahimta:

1. Adawa da dokar Shari’ar Musulinci a Najeriya: Nayi bincike mai zurfi ta hanyar bibiyar maganganun Atiku Abubakar da kanshi akan Shari’ar Musulinci a Najeriya tun farowarta a shekarar 1999. Na samu maganganun shi suna cin karo da juna. A farkon al'amari, Atiku ya goyi bayan Shari

23/02/2023

Koda Malami Yayi Kuskure Bazai Tabayin DaiDai da Jahiliba,
Mutuncin Malamai Gubane Duk Wanda Taci Sai Ya Lalace.

17/02/2023

Wallahi Koda Anyi Zaben Babu Abinda Zai Canza Matukar Bamu Canza Dabi'unmu Ba

Nafi Shekara Biyu Zuwa Ukku, Ina Wannan Nazarin da Bibiyar Comments a Social Media.'Yan kudancin Nigeria, Musulmin su da...
29/01/2023

Nafi Shekara Biyu Zuwa Ukku, Ina Wannan Nazarin da Bibiyar Comments a Social Media.
'Yan kudancin Nigeria, Musulmin su da kiristocin su, 'yan APC da 'yan PDP, basu zagi da cin mutuncin Professor Yemi Osinbajo Koda ko sun saba masa a ra'ayi.
Kiristocin Nigeria tare da banbancin darikun su basa zagi da cin mutuncin Mathew Hassan Kukah, duk da cewa, da yawan su basa biyar sa sallah. Wannan shi ake cewa "Disipline"( not technical meaning).

Abin mamaki, anan Arewa musamman ta Musulmi, abu ne mai sauki Yaro dan kasa da shekara 30 ya zagi Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alh. Atiku Abubakar, Dr. Ahmad Gummi, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ko wani daga cikin manyan Malamai ko Sarakuna, ko yayi masa cin zarafi don dai ya sabawa ra'ayin sa.

Babban abin lura anan shine, mutum biyu baza suyi sabani ba cewa, daga 1999 zuwa yanzu 'yan kudu sun fimu cin gajiyar demokradiyya nesa ba kusa ba. Ashe ba zagi da cin mutuncin manya kesa a samu ba!!

Bayan Manzon Allah S. A. W. ba wanda biyar maganar sa ko ra'ayin sa yake cilas. Ra'ayin kowa ijtihadi ne, yakan yiyu ya zama daidai yakan yiyu ya zama kuskure. Amma rashin yarda da ra'ayin wani baya nufin sai kayi masa cin mutunci da cin zarafi.

Ina kira ga Musulmin Arewa musamman matasa da muji tsoron Allah, mu k**a bakunan mu da hannayen mu daga cin mutuncin mutane musamman Wadanda Allah ya baiwa manyan shekaru da matsayi a cikin mu, dasunan sabanin ra'ayi. Wannan bai taba zama wayewa da ci gaba a kowane civilasation ba, haka kuma bazai taba zama addini ba.

Allah Ya dora mu akan hanya madaidaiciya Ameen

✍️ Dr. Jabir Sani Maihula.

Changing The Nation Through Education
29/01/2023

Changing The Nation Through Education

Address


Telephone

+2348037620888

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AHMAD ALIYU LADAN posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to AHMAD ALIYU LADAN:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share