Hausa Times

Hausa Times Jaridar Hausa Times Wata Kafar Yada Labarai Ce Da Ke Yada Labarai Da Harshen Hausa.
(3)

TIRƘASHI: Ku Amince Tinubu Ya Sake Yin Maimai, Domin Sake Zaɓensa Ba Matsala Ba Ce, Kuma Sauya Gwamnati Ya Fi Illa Fiye ...
29/08/2026

TIRƘASHI: Ku Amince Tinubu Ya Sake Yin Maimai, Domin Sake Zaɓensa Ba Matsala Ba Ce, Kuma Sauya Gwamnati Ya Fi Illa Fiye Da Canja Sabo, Sannan Idan Batun Talauci Ne Da Matsalar Tsaro, Ƴan Nijeriya Ba Baƙonsu Ba Ne, Inji Shêikh Sa'idu Aliyu Maikwano

Menene ra'ayinku?

Bashir El-Rufai ya caccaki ɗan uwansa Bello kan siyasaBashir El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir el-Rufai, ya cac...
29/08/2026

Bashir El-Rufai ya caccaki ɗan uwansa Bello kan siyasa

Bashir El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir el-Rufai, ya caccaki ɗan uwansa, Bello El-Rufai, bisa zargin rashin biyayya ga iyali da kuma sauya matsayar siyasa.

Bashir ya bayyana hakan ne cikin wasu sakonni da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya zargi Bello da kasancewa tare da Gwamnan Kaduna, Uba Sani, har sai da ya fahimci cewa ana watsi da shi.

Bello, wanda ke wakiltar Kaduna North a Majalisar Wakilai, ya bar jam’iyyar APC a watan Mayun 2026, inda ya koma ADC, tare da mahaifinsu.

Bashir ya kuma zargi Bello da neman ya dakatar da sukar da yake yi wa Uba Sani, tare da bayyana shi a matsayin munafuki. Wasu daga cikin zarge-zargen da ya wallafa daga bisani an goge su.

A halin yanzu, Nasir el-Rufai yana fuskantar shari’o’i kan zargin almundahana da amfani da ofis ba bisa ka’ida ba a lokacin da yake gwamnan Kaduna tsakanin 2015 zuwa 2023.

MUHAWARA: Tsakanin Janye Tallafin Man Fetur Da Dawo Da Tallafin Wane Zai Amfani Talakan Najeriya?ZAƁI GWANINKA: Atiku Ab...
29/08/2026

MUHAWARA: Tsakanin Janye Tallafin Man Fetur Da Dawo Da Tallafin Wane Zai Amfani Talakan Najeriya?

ZAƁI GWANINKA: Atiku Abubakar Ko Tinubu ?

A Kafta.... Ni

Kana ganin wanann hoton, me ne ya zo ranka?
29/08/2026

Kana ganin wanann hoton, me ne ya zo ranka?

Uban Kasa, Uban Duk 'Yan Nigeria, Mallam Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.Wani Fata Kuke Masa A Zaben 2027 Dake Tafe?
29/08/2026

Uban Kasa, Uban Duk 'Yan Nigeria, Mallam Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Wani Fata Kuke Masa A Zaben 2027 Dake Tafe?

Senator Uba Sani Ya Bayyana A Murtala Square Kaduna Wajen Taron Maulidi.Achan Jahar Kaduna Gwamnan Jahar Mallam Uba Sani...
25/08/2026

Senator Uba Sani Ya Bayyana A Murtala Square Kaduna Wajen Taron Maulidi.

Achan Jahar Kaduna Gwamnan Jahar Mallam Uba Sani Ya Samu Damar Halartan Taron Tunawa Da Ranar Haihuwar Annabi Muhammad (SAW) Wato Maulidi Wanda Ake Gabatarwa Duk Duniya Kuma A Jahar Kaduna Ake Gudanarwa A Murtala Square Kaduna.

Allah Ya Karawa Annabi Daraja.

Maulidi: Remi Tinubu ta bukaci Musulmi su yi koyi da halayen Annabi Muhammad (SAW)Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Ol...
25/08/2026

Maulidi: Remi Tinubu ta bukaci Musulmi su yi koyi da halayen Annabi Muhammad (SAW)

Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta bukaci Musulmi su yi koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW), musamman tausayi, yafiya da zaman lafiya.

A sakonta na bikin Maulidi da gidan talabijin na ARISE ya ruwaito, Remi Tinubu ta ce tunawa da haihuwar Annabi Muhammad (SAW) wata dama ce ta yin nazari kan rayuwarsa da kyawawan dabi'unsa.

Ibrahim Masari, hadimin Tinubu da Gwamnan Yobe sun bai wa kungiyar Izala ta Malam Jingir kyautar ₦600mGwamnan jihar Yobe...
25/08/2026

Ibrahim Masari, hadimin Tinubu da Gwamnan Yobe sun bai wa kungiyar Izala ta Malam Jingir kyautar ₦600m

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni da babban mai bai wa Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari, sun yi alkawarin bayar da Naira miliyan 600 domin aikin gina jami'ar Fortune University mallakin kungiyar JIBWIS.

Jaridar Daily Trust ta ce an sanar da kyautar ne a yyayin wani taro da kungiyar ta gudanar a Jos, inda Masari ya sanar da bayar da Naira miliyan 300, yayin da ya ce Gwamna Buni shi ma ya yi alkawarin bayar da Naira miliyan 300.

Shugaban Majalisar Malamai ta JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bukaci Musulmi da sauran masu hannu da shuni su tallafa wa aikin, yana mai cewa jami'ar ba mallakinsa ba ce, kuma idan an kammala ta za ta amfani Musulmi da Kiristoci.

Daga Barrister Hamza Nuhu Dantani Tunda Atiku Abubakar yace zai Dawo ta Tallafin Mai Petrol. ( Subsidy)  idan yaci zaben...
24/08/2026

Daga Barrister Hamza Nuhu Dantani

Tunda Atiku Abubakar yace zai Dawo ta Tallafin Mai Petrol. ( Subsidy) idan yaci zaben 2027, Hankalin Omologo ya tashi. Ya Mayar da martani tare da Tura su Abdulazeez Abdulazeez da sauran mukarraban Gomnatinsa don Kalubalantar Atiku Abubakar anma lamari ya Gagara!

Matsalar itace shine, Atiku Abubakar ya san dacewa Alkawari na da Nawi. Kar yayi Dadin Baki don neman Mulki daga Karshe ya kasa cikawa. Rashin Cika Alkawari na durkusar da martabar mutum har yakai ga taba Nagartar Mulkinsa. Yana daya daga cikin Dalilin da yasaka mulkin Omologo ya kasance babu Nagarta!

Saboda Haka mu dai namu Ido.. Anma Muna jiran Ranar da zamu Kwarfe Olu!

Aikin Kaduna Northern Bypass da ake gudanarwa da kankare na ci gaba da tafiya yadda ya kamata, bisa umarnin Shugaban Ƙas...
24/08/2026

Aikin Kaduna Northern Bypass da ake gudanarwa da kankare na ci gaba da tafiya yadda ya kamata, bisa umarnin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Aikin, wanda Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ƙarƙashin jagorancin Ministan Ayyuka, Injiniya David Umahi, ke gudanarwa, zai taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa zirga-zirga tare da rage cunkoson ababen hawa a cikin birnin Kaduna.

Address

Kaduna

Telephone

+2348034666844

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Times posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share