21/06/2026
TSARIN AURE DA HANYAR ZAMAN LAFIYA KO RABUWA CIKIN MUTUNCI
Prof. Mansur Isah Yelwa Hafizahillah yace:
Tsarin aure fa
daya ne daga cikin biyu.
Ko a zauna lafiya,
ko a rabu cikin mutunci.
Amma ba wulakanci ba,
ba zama tsaka-tsaki ba.
Ba Wani abu tsaka-tsaki
Allah bai yarda da shi ba.
Ko ku zauna lafiya,
ku daidaita tsakaninku.
Ke ki yi masa kyakkyawan mu’amala,
ki sauke hakkinki.
Kai kuma ka yi mata kyakkyawan mu’amala,
ka sauke hakkinka.
Sai ku zama daidai,
cikin fahimta da mutunci.
Idan ba zai yiwu ba,
to kawai a rabu.
A fi zarginka da cewa ka saki cikin adalci,
fiye da a zargeka da wulakanta ‘yar mutane.
Idan ka ga cewa abun da ka ke mata tsammani
ba zai tafi daidai ba,
to a madadin ka wulakanta ta,
ka kira iyayenta.
Ka sanar da su cikin hikima,
ku yi kokarin gyarawa.
Idan ba za ta gyaru ba,
ka bar ta cikin mutunci.
Amma ka wulakanta ta,
kada ka yarda da haka.
Annabi ﷺ ya ce
ya ishi mutum sharri
ya wulakanta wanda ke karkashinsa.
Mace a karkashinka,
‘ya’ya a karkashinka,
duk suna da hakkoki.
Ya Allah Ka ba mu zaman lafiya a gidajenmu,
Ka sa soyayya da fahimta ta tabbata a tsakanin ma’aurata.
Ka kare mu daga zalunci da wulakanci,
Ka ba mu ikon sauke hakkokin da Ka ɗora mana.
Ka gyara mana iyalai,
Ka ba mu zaman lafiya mai albarka.
Amin ya Rabbal Alamin.
Mansur Isah Yelwa.