ClockwiseReports Hausa

  • Home
  • ClockwiseReports Hausa

ClockwiseReports Hausa Sabowar kafar yada labarai masu inganci

Yadda aka yi bikin bankwana da tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa bayan shugaban ƙasa Bola Ahme...
31/10/2025

Yadda aka yi bikin bankwana da tsohon babban hafsan sojin Najeriya, Janar Christopher Musa bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ritayarsa.

Musa ya cika shekaru 38 yana aikin soja.

Ayammacin wannan rana ta litinin Mai Girma Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba K Yusuf tare da Ambasadan kasan Rwanda a Nijer...
27/10/2025

Ayammacin wannan rana ta litinin Mai Girma Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba K Yusuf tare da Ambasadan kasan Rwanda a Nijeriya, Mr Christopher Bazivamo, sun bude gidan PALMA da aka gyara a fadar Gwamnatin Kano, wanda Gwamnatin jihar kano ta sabunta shi dan mai dashi na Zamani.

Wannan gida shi ne mazaunin Gwamnan mulkin mallaka na farko a jihar Kano, Sir RH Palmer, wanda aka samar a Shekarar 1914.

Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin Kano ta sauyawa makarantar mata ta Mai Kwatashi matsuguni zuwa Kaura Goje Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta ɗa...
27/10/2025

Gwamnatin Kano ta sauyawa makarantar mata ta Mai Kwatashi matsuguni zuwa Kaura Goje

Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta ɗauke Karantar Sakandare ta Mata ta Mai Kwatashi daga titin France Road, Sabongari zuwa unguwar Kaura Goje a karamar hukumar Nassarawa.

Freedom Radio ta rawaito cewa Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya bada umarnin sakewa makarantar matsuguni biyo bayan koken ƴan unguwar Kaura Goje da kewayenta akan zargin yadda ake wa ɗaliban makarantar kwace da sauran su.

Tuni dai kungiyar cigaban unguwannin Kaura Goje, Gwagwarwa, Gawuna, Riga, da Gamar Fulani ta mika sakon godiya ga Gwamna Yusuf bisa cika alƙawarin sauyawa makarantar.

Mazauna unguwannin sun nuna farin ciki yadda aka kai makarantar kusa da su, musamman ma ganin cewa ta mata ce, inda su ka nuna cewa hakan zai kara habaka ilimin mata a yankin nasu.

Dalilin da ya sa mu ka soke batun auren Mai Wushirya da Ƴarguda - Hisbah Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa ta...
26/10/2025

Dalilin da ya sa mu ka soke batun auren Mai Wushirya da Ƴarguda - Hisbah

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa ta soke batun auren jarumin Tiktok din nan Ashiru Idris Mai Wushirya da Abashiyya Yarguda bayan sun tabbatar da cewa babu soyayya a tsakanin su.

Idan za a iya tunawa dai a kwanakin baya ne, wata kotun Majistiri ta umarci hukumar Hisbah ta shirya kan auren jaruman biyu bayan an same su da laifin wallafa hotuna da bidiyoyi na badala.

Sai dai, a wata sanarwa da mataimakin Babban Kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Dakta Mujahideen Aminudeen ya aiko wa jaridar Daily Nigerian Hausa ya bayyana cewa bayan an gudanar da gwaje-gwaje, Mai Wushirya da 'Yar Guda sun tabbatar wa da hukumar cewa "Content Creation" kawai suke yi ba wai soyayya ba.

Acewar Dakta Mujahideen, daman sharadi ne a addini cewa sai Amarya da Ango sun amince da junansu kafin a kai ga daura aure.

"Tun kafin a zo maganar Sadaki ma, s**a nuna gaskiya baza su iya ba, mai girma babban kwamanda ya yi la'akari da cewa, a Musulunci Shari'a ake karewa , kuma a shari'a ba a auren dole".

Ya kara da cewa tunda ba soyayya tsakanin Haruna Tiktok din kuma na akwai bambancin halitta tsakanin su, to ta tabbata cewa za a iya rasa wannan batu na aure domin za a iya samun matsaloli bayan auren.

"Mu kuma a Hisbah, so mu ke yi aure ya zama mutu-ka-raba, ba wai a rika samun matsaloli har ta kai ga cin zarafi ba," innji Dakta Mujahideen

Haka kuma, ya ce Hisbah za ta mayar da su gaban kotu domin daukar mataki na gaba.

Majalisa ta amince a ƙirƙiro jihohi shida a NajeriyaHaɗaɗɗiyar kwamitin majalisar dattawa da ta wakilan Najeriya kan yi ...
26/10/2025

Majalisa ta amince a ƙirƙiro jihohi shida a Najeriya

Haɗaɗɗiyar kwamitin majalisar dattawa da ta wakilan Najeriya kan yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar garambawul ta amince da a ƙirƙiro jihohi guda shida.

Wannan na cikin matsayar da aka cimmawa a ƙarshen taron ƙara wa juna sani na kwana biyu, wanda mataimakin majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin da mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu s**a jagoranta a jihar Legas.

Kwamitin ya tattauna ne kan buƙatu guda 69, ciki har da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da buƙatar a ƙirƙirar ƙananan hukumomin 278 kamar yadda jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito.

A game da buƙatar ƙirƙirar jihohi 55 da aka gabatar a ranar Asabar, kwamitin ya amince da ƙirƙirar jihohi guda shida a duk shiyoyin ƙasar guda shida.

Idan aka amince da ƙirƙirar sababbin jihohi, Najeriya za ta zama tana da jihohi 42 ke nan.

Yadda ake gudanar da maukibin Ƙadiriyya karo na 75 a Kano, wanda Ƙaribullah Shiekh Nasir Kabara ke jagaron.
04/10/2025

Yadda ake gudanar da maukibin Ƙadiriyya karo na 75 a Kano, wanda Ƙaribullah Shiekh Nasir Kabara ke jagaron.

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa'azi Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa...
01/10/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Kano ta dakatar da Malam Lawan Triumph daga yon wa'azi

Majalisar Shura da gwamnatin Kano ta kafa ya sanar da dakatar da Malam Lawan Shuaibu Triumph daga yin wa'azi.

A wani taron manema labarai da Sakataren majalisar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ya yi a yau Laraba, ya ce an dakatar da Malam Lawan ne domin bashi damar ya zo gaban majalisar ya kare kan sa daga zarge-zargen da ake yi masa na yin kalaman ɓatanci ga Ma'aiki.

A cewar Sagagi, an dakatar da Malam Lawan har sai an kammala bincike da jin ta bakin sa a matakin Majalisar ta shura.

Ya kuma yi kira ga ƴan siyasa da su guji tsoma baki a batun, inda ya bukaci da a kyale kwamitin ya kammala aikin sa.

Sagagi ya tabbatar da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah ba tare da don rai ko rashin adalci ba.

Ina daf da daina waƙa kafin fitowar wakar da na yi da Omah Lay - Davido Shahararren mawaki Davido ya bayyana cewa ya kus...
30/09/2025

Ina daf da daina waƙa kafin fitowar wakar da na yi da Omah Lay - Davido

Shahararren mawaki Davido ya bayyana cewa ya kusan yin bankwana da harkar waka kafin fitar da wakarsa da ta zaga duniya mai suna “With You” wadda ya yi tare da Omah Lay.

A cikin wata hira da aka yi da shi a Noire TV, Davido ya yi nazari kan nasarar da ba a zata ba da wakar ta samu, wadda ke cikin sabon albam dinsa mai suna “5ive.”

Duk da ya ke ya yi imani cewa wakar da ya yi da Omah Lay za ta ja hankali, Davido ya ce bai taba zato cewa zata zama shahararriya haka ba.

Davido ya bayyana wakar a matsayin wata baiwar Ubangiji da ta zo a muhimmin lokaci a rayuwar sana’arsa.

Ya nuna matukar godiya, yana mai cewa abu ne da ba kasafai yake faruwa ba a samu irin wannan babban buri bayan fiye da shekara goma sha biyu a masana’antar waka.

“A fili, ita ce mafi girma a cikin albam. Ba za ka taba iya cewa wace waka za ta yi fice a albam ba. Amma na san duk inda aka hada Davido da Omah Lay, za ta yi tasiri. Amma ban zata za ta zama irin wannan babbar nasara ba,” in ji shi.

“Mun gode wa Allah cewa bayan shekara 13 zuwa 14 da na shafe a waka, na samu irin wannan waka. Yawanci mutane kan samu irin wannan a farkon sana’arsu ko a tsakiyarta.

“Ni ma na riga na fara shirin yin bankwana da waka, sai Allah ya bani irin wannan waka. Wannan ya kara haske a rayuwata. Ina godiya. Kuma abokan hadin wakar sun kasance na musamman.”

Gwamnatin Tinubu za ta fara karbar haraji a hannun mata masu zaman kansu -Taiwo Oyedele
30/09/2025

Gwamnatin Tinubu za ta fara karbar haraji a hannun mata masu zaman kansu -Taiwo Oyedele

Yanzu dai complaint biyu ne a kasa. A iya Kano kawai. Sheikh Triumph ya zo ya nuna inda ya ga cewa duk wanda yace an hai...
29/09/2025

Yanzu dai complaint biyu ne a kasa. A iya Kano kawai. Sheikh Triumph ya zo ya nuna inda ya ga cewa duk wanda yace an haifi Manzon Allah SAW da shayi karya yake. Sai kuma Shehu Alkarmawi shi ma ya zo ya nuna inda ya ga cewa idan ka ga ƙatoton rakumi Annabi ne.

Duk wanda ya kasa nuna wurin mun yarda kawai a fille wuyan sa.

Zargin kalaman ɓatanci: Majalisar Shura ta gaiyaci Malam Lawan Triumph Majalisar shura ta jihar Kano ta gaiyaci Sheikh L...
26/09/2025

Zargin kalaman ɓatanci: Majalisar Shura ta gaiyaci Malam Lawan Triumph

Majalisar shura ta jihar Kano ta gaiyaci Sheikh Lawan Abubakar Triumph bisa ƙorafe-ƙorafe da aka miƙa mata na zargin furta kalaman ɓatanci ga Ma'aiki Annabi Muhammad (SAW).

Haka zalika majalisar ta gaiyaci waɗanda s**a mika ƙorafe-ƙorafen domin zama a ji ta bakin ki wanne ɓangare.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan zaman majalisar na farko tun da aka kafa ta, Sakataren majalisar kuma Kwamishinan Kasuwanci, Shehu Wada Sagagi ya tabbatar da cewa an mikawa majalisar ƙorafe-ƙorafe har guda 8 daga kungiyoyin addini da na al'umma.

Ya ce majalisar ta duba ƙorafe-ƙorafen kuma za ta gayyaci kowanne ɓangare, har da shi ma Malam Triumph din don jin ta bakin sa.

Haka zalika Sagagi ya kara da cewa Majalisar za ta yi aiki tsakani da Allah don baiwa gwamnati shawarar da ta dace.

Majalisar Dokoki ta nemi Gwamnatin Kano ta gyara babban masallacin jihar Majalisar dokokin jihar Kano ta nemi Gwamnatin ...
24/09/2025

Majalisar Dokoki ta nemi Gwamnatin Kano ta gyara babban masallacin jihar

Majalisar dokokin jihar Kano ta nemi Gwamnatin jihar ta gyara Babban Masallacin cikin Gari mai cike da tarihi.

Freedom Radio ta rawaito cewa a zaman majalisar jihar da aka gudanar yau, ɗan majalisar Birni, Aliyu Yusuf Daneji, ya sake kira ga gwamnati da ta gaggauta fara aikin gyaran masallaci da aka riga aka gabatar mata a baya, amma har yanzu ba a aiwatar ba.

Haka kuma, ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Rano, Ibrahim Muhammad Malami Rano, ya bukaci gwamnati ta gyara muhimman hanyoyin cikin garin Rano.

Yan majalisun biyu sun bayyana cewa gyaran masallacin da kuma hanyoyin na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar al’umma, tare da roƙon gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa.

Address


Opening Hours

Monday 07:00 - 19:00
Tuesday 07:00 - 19:00
Wednesday 07:00 - 19:00
Thursday 07:00 - 19:00
Friday 07:00 - 19:00
Saturday 07:00 - 19:00
Sunday 07:00 - 19:00

Telephone

+2349030769760

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ClockwiseReports Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share