07/04/2025
I got 26 reactions and 16 replies on my recent top post! Thank you all for your continued support. I could not have done it without you. ๐๐ค๐
ZAMO MIJI NAGARI MANA ฦAN'UWA!
Idan matarka tayi bacci a parlor, ka cicciษeta ka kai ta ษaki, ka sanya taji kamar jaririya ce ita wani lokacin. ๐ถ
Batun gaskiya kowacce mace tana son ana kula da ita kamar yar shekara 2, shiyasa zaka ga wani lokacin suna yarinta ko wauta komai girman su.
haka abin ya ke bawai zagi ba. ๐ซก
Zaka iya jayayya da matar ka, abu na gaba da zata yi shine zaka ga ta sauฦe akwati tana shirya kayanta, bawai saki take nema ba, a'a yarinta kawai take yi, kawai tana son ka zo ka riฦe ta kace da ita:
"kiyi haฦuri jayayyar da mukayi" ๐
ฦan'uwa nah, idan matar ka ta taka ฦafar ka da gangan ko bisa kuskure, kada kabari idanun ka suyi jajur, kayi mata murmushi, idan da gangan tayi, wasa take maka, idan bisa kuskure tayi maka, ba laifin ta bane ๐
karkayiwa matar ka tsawa bisa wani ฦaramin kuskure, a matsayin ka na namjii, ka koyi kawar da kai bisa wasu abubuwan, kada ka zama mai yawan raki akan komai๐
Ka riฦa yi mata waฦoฦin soyayya kana zolayar ta, kana kiran ta da sunaye masu daษi domin mata suna son sunaye masu daษi domin haka zuciyarsu take da son a tarairaye su โค๏ธ
Taimaka mata da ayyukan gida idan kana gidan ranar da baka fita, kada ka ษauke ta kamar ฦดar aikin gida..๐ฏ
Kana rufe mata idanu kana mata cakwulkwuli, ko ka bata tsoro wani lokacin kamar dai yadda akema yara, Idan ka fita wajen aiki ka kira ta a waya kace mata I LOVE YOU BABY..๐ฅ
Samu paper ka rubuta mata Kalaman soyayya ka ajiye mata su a ฦasar pillow ko kan mirrow ko cikin drawer kafin ka fita aiki๐...
ka riฦa ce mata ita kyakkyawar gaske ce kuma kayi murna da nasara da Ubangiji Ya baka ita a matsayin abokiyar zama ๐ฅฐ...
Dukkanin waษannan hanyoyi ne na zamewa ROMANTIC HUSBAND ba wai kawai sai a gado ba....๐
๐ฅ๐ฅ
Allah Ya mana jagora ya bamu mata nagari โบ๏ธ