15/06/2025
YACCE AKE YANKA WUYA MAI COLLAR V.NECK COllar
Ita Irin wannan wuyan tana da matukar saukin Dinki, abu uku xa a mai da Hankali akan su.
1.sai bayan kahade gaba da bayan rigar sannan zaka huda wuyar.
2. Sanin fadin wuyan da sanin zurfin wuyan ta gaba.
3. Fahintar Fadin collar da kuka tsawon ta.
Tanada Tsarukan biyu 3🤞
1. Akwai wacce Ake mata zip ta kan collar
2. Akwia kuma wacce straight take baruwan ka da zip
3. Akwi wacce collar take kallon tsakiyar rigar, akwai wacce take kallon gefen rigar.
Amma kuma dukkan su dayane, kawai Abunda ake bukatar kamai da hankali shine sanin inchis din mai jiki da mara jiki.
Bayan kayi landing ajikin gaba da bayn Rigar, batare da anhuda wuyan rigar ba, sai kahadasu waje guda daganan, sai kanin kasu gida biyu ta tsawo kasoma fitar sa inchis din, kashiga bayan rigar da inchis 1 kacal, fadin wuyan rigar ta kyallen baya inchis 3, tsawon wuya rigar ta gaba inchis7 sai kazana line yabaka v.neck.
Bayan kayanka, sai ka bude zai baka cikakken zanen v sai ka gwada daga zipper allowance zuwa zagayen tsakiyar collar, zai baka inchis 13 kaga tsawon collar ka duk daya inchis 13 kenan, fadin collar Iri biyuce akwai mai fadi sosai Akwia mai fadi kadan, inchis biyar.
Daga karken ta tanada salebu mai tsawo, sannan ana manna mata Hestie gum ko piper gum harda landing dinta, sabida yana kara tsayuwanta da kyau.
Sannan tana bukatar guga wajen Mannawa da kuma gogeta kafin sata.
KALLI HOTON DANA KASA AKASA ZAKA FAHINTA BAYANINA DUKA INSHAVALLAH
DAN MAMA FASHION 👔👘👗 KGK
09168902176