28/10/2025
Ɗan Majalisar Dattawa daga Jihar Delta, Sanata Ned Nwoko, ya ce yana tausaya wa maza da ke da mace ɗaya kawai a aure.
A cewarsa, auren mata fiye da ɗaya yana kawo daidaito da natsuwa ga namiji - yana hana tashin hankali da damuwa a cikin gida. 😄
Sanatan, wanda shi kansa yana da mata da dama, ya ce tsarin aure mai yawa ya dace da al’ada da halin rayuwar maza, musamman a Najeriya.
Wannan maganar tasa ta haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke dariya, wasu kuma ke muhawara - “To ai sai ka iya kula da su tukunna!” 🤭