23/02/2025
Hukumar Alhazai ta Najeriya, wato NAHCON, ta ce ta ci karfin shirye-shiryen aikin Hajjin bana, domin ta tantace adadin maniyatan da ake sa ran za su tafi Saudiyya, da jiragen da za su yi jigilarsu da dai sauransu.
Ta ce ta daddale yarjejeniya tsakaninta da kamfanin da zai yi wa alhazan kasar hidima a kasa mai tsarki, bayan da ta gayyato jami'ansa zuwa Najeriya, inda aka kawar da duk wata kura da ake hasashen ta taso a tsakaninsu.
Farfesa Abdullahi Saleh Usman, shugaban hukumar alhazan Najeriyar,ya shaidawa BBC cewa sun yi duk wani abinda ya k**ata.
''Mun riga mun gama tantance jiragen sama da masu bada sabis a Saudiyya, da na Madina da na Makah da na Masha'ir
Duk dai abinda ya k**ata mu yi dangane da shirye shiryenmu, za mu iya cewa mun gama''. in ji shi
Game da kurar da taso da ake ganin za ta iya kawo cikas kuwa hukumar ta ce duk da cewa kurar ta tayar mu su da hankali amma komai ya lafa saboda sun cimma matsaya da kamfanin Saudiyyar.
'' Ta tayar muna da hankali domin ba mu san tushenta ba , ba mu san an yi wannan abu ba , wannan ne dalilin da yasa muka gayyoto kamfanin da aka ce sun rubuto takada akan cewa za su kai hukumar kara akan wai na soke mu su kwangilar da aka basu''
Ta ce shugaban kamfanin na Saudiyya da mukarabansa sun zo kasar kuma su ma sun yi mamakin jin wannan labari
Wasu jaridu sun ruwaito cewa hukumar ta NAHCON ta soke kwangilar da aka bai kamfanin na aiki a Masha'ir watau Minna , da Musdaliffa da kuma Arafat. Sai dai hukumar ta ce rashin fahimta ce ta janyo sabanin da aka samu tsakaninsu.
''Mu nan Najeriya an bamu kujeru na mutum dubu 95, toh mun lura cewa gaskiya ba zamu iya kawo mutane dubu 95 ba''
''Su kuma suna jiran lalai mu kawo mu su dubu casain da biyar, to sai su ke ganin ko wasu kamfanonin mu ke kokarin mu dauki wani bangare na aikin mu ba wa, mu ka ce mu su a'a'' in ji shi.
Shugaban hukumar na NAHCON ya ce sun nemi wakilan kamfanin a kan su zo Najeriya domin su karyata labarin da ke cewa sun kai hukumar kotu.