Zage-Zagi A Yau.

Zage-Zagi A Yau. [email protected]
08034610013. Chairman CEO Ayyan Carpentary &Joinery Enterprises
A home of quality services

Shafin Zage-Zagi A Yau, Shafi ne da Za ta Rika kawo Muku Tarihin Gidajen Sarautan Zazzau da al'adu Tare Muhimman Labarai da ya Shafi Arewa da kasar Nijeriya da Duniya baki daya.

INNĀ LILLĀHI WA INNĀ ILAIHI RĀJI'ŪNAllah Ya yi wa Alhaji Abdullahi Yusuf (Uban Faki) rasuwa a yau.Za a yi Sallar Jana'iz...
31/07/2026

INNĀ LILLĀHI WA INNĀ ILAIHI RĀJI'ŪN

Allah Ya yi wa Alhaji Abdullahi Yusuf (Uban Faki) rasuwa a yau.

Za a yi Sallar Jana'izarsa a Masallacin Juma'a na Madarkaci bayan Sallar Juma'a, In shā Allah.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata kabarinsa, Ya sa mala'ikun rahama su yi masa maraba, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.

Allah Ya gafarta masa, Ya sa ya huta daga wahalhalun duniya, Ya tashe shi cikin bayinsa na ƙwarai, Ya haɗa mu da shi a Aljannatul Firdausi. Āmīn Yā Rabbal 'Ālamīn.

Ya Allah! Guide our steps and decisions, grant us strength in hardship, bless us with what is sufficient and beneficial,...
31/07/2026

Ya Allah! Guide our steps and decisions, grant us strength in hardship, bless us with what is sufficient and beneficial, and keep us under Your protection. Hear our du’as, grant our hearts peace in Your wisdom, forgive our sins, and have mercy on our loved ones. Reward them with Al-Jannatul Firdaus and make us among those who earn Your pleasure.

Ya Ar-Rahman, Ya Ar-Raheem, Ya Dhul-Jalali wal-Ikram, accept our du’as and envelop us in Your mercy. Ameen

JUMA’AH MUBARAK

Hajiya Dr. Maimuna M.S Abdullahi Director Quality Assurance National Board for Arabic and Islamic Studies! NBAS, Ta Hala...
25/07/2026

Hajiya Dr. Maimuna M.S Abdullahi Director Quality Assurance National Board for Arabic and Islamic Studies! NBAS, Ta Halarci Taron yayen dalibai na Makarantan Sunshine Models Academy Zaria, Tare da Murnan cika Shekara Goma (10) da kafa Makarantan, Wanda Alhaji Rabi'u Abubakar Mai Bulo ya samar. Taron ya gudana ne a Babban dakin taro dake Kwalejin Barewa dake Zariya. A lokacin Taro an karrama malamai da dalibai, masu gwazo da mai da hankali.

Dr Maimuna ta bayyana jindadinta da yabama mahukunta Makarantan wajen koyar da nagartaccen ilimi ga yara dalibai. Tayi godiya da fa tanan Alheri,

MAKARANTAN SUNSHINE MODEL ACADEMY ZARIA, TA GUDANAR DA TARON YAYEN DALIBAINTA NA ZANGON 2025/2026 TARE DA MURNAN CIKA SH...
25/07/2026

MAKARANTAN SUNSHINE MODEL ACADEMY ZARIA, TA GUDANAR DA TARON YAYEN DALIBAINTA NA ZANGON 2025/2026 TARE DA MURNAN CIKA SHEKARA GOMA DA KAFA MAKARANTAN.

Mai Girma Sarkin Ayyukan Zazzau, Malam Abbas Muhammed Fagachi, ya Halarci taron yayen dalibai na Makarantan Sunshine Models Academy Zaria, Tare da Murnan cika Shekara Goma da kafa Makarantan, wanda Alhaji Rabi'u Abubakar mai Bula da samar. Taron ya gudana ne a Babban dakin Taro na Mai Alfarma sarkin Musulmi dake Kwalejin Barewa dake Zariya. Mai mai Sarkin Ayyukan Zazzau, ya muka kyaututuka ga malamai da dalibai masu gwazo da himmma.

📜 KAKAN MAI MARTABA SARKIN ZAZZAUWannan shi ne Marigayi Mai Girma Turakin Babban Zazzau, Malam Abdurrahman Dikko, wanda ...
24/07/2026

📜 KAKAN MAI MARTABA SARKIN ZAZZAU

Wannan shi ne Marigayi Mai Girma Turakin Babban Zazzau, Malam Abdurrahman Dikko, wanda yake daga cikin fitattun dattawan da s**a taka muhimmiyar rawa a tarihin Masarautar Zazzau.

Marigayin shi ne kakan Mai Martaba Sarkin Zazzau, Amb. Ahmad Nuhu Bamalli, CFR, domin shi ne mahaifin Hajiya Khadija, mahaifiyar Mai Martaba Sarkin Zazzau. Haka kuma, shi ne mahaifin Marigayi Alhaji Umaru Dikko, tsohon Ministan Sufuri na Tarayyar Najeriya.

Asalin Zuriyarsa

Marigayi Turakin Babban Zazzau, Malam Abdurrahman Dikko ɗan Junaidu, ɗan Galadima Chacho Haliru, ɗan Sarkin Musulmi Aliyu Babba, ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ɗan Shehu Usmanu Ɗanfodiyo (Allah Ya yarda da su baki ɗaya).

Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa, Ya sanya aljannar Firdausi ta zama makomarsa. Haka kuma muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙan magabatanmu baki ɗaya, Ya yalwata musu rahama, Ya sa suna cikin mafificin matsayi a Aljannatul Firdausi. Amin.

SAKON BARKA DA JUMA'A. Mahukunta Shafin Zage-Zagi A Yau, Suna amfani da wannan dama wajen mika sakon Barka da Juma'a Zuw...
24/07/2026

SAKON BARKA DA JUMA'A.

Mahukunta Shafin Zage-Zagi A Yau, Suna amfani da wannan dama wajen mika sakon Barka da Juma'a Zuwa ga Mai Girma Arch Sani Abubakar Abbas Sardaunan Chikun. Muna Addu'ur Allah Ya kara albarka, ya sadaka da dukkan alherin wannan Rana, ya kyautata Rayuwanka.

SHEKARA ƊAYA DA RASUWAR MARIGAYI ABDULFATAHYau ne Marigayi Abdulfatah yake cika shekara ɗaya da rasuwa.Marigayin na ɗaya...
24/07/2026

SHEKARA ƊAYA DA RASUWAR MARIGAYI ABDULFATAH

Yau ne Marigayi Abdulfatah yake cika shekara ɗaya da rasuwa.

Marigayin na ɗaya daga cikin fitattun matasan Kasar Zazzau da s**a yi fice a fagen (Media). Ya kasance matashi mai ƙwazo, jajircewa da kishin al’umma, wanda ya yi amfani da kafafen yaɗa labarai wajen isar da sahihan bayanai da kuma hidimtawa al’ummarsa.

Ko da yake ya riga mu gidan gaskiya, kyawawan ayyukansa da gudummawar da ya bayar za su ci gaba da kasancewa abin tunawa ga iyalansa, abokansa da al’ummar Zazzau baki ɗaya.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata masa kabari, Ya haskaka masa makwancinsa, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Allah Ya ba iyalansa da masoyansa haƙurin jure rashinsa. Amin Ya Rabbal ‘Alamin.

MAI GIRMA KACHALLAN ZAZZAUMaigirma Kachallan Zazzau, muna yi maka fatan alheri tare da addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya...
24/07/2026

MAI GIRMA KACHALLAN ZAZZAU

Maigirma Kachallan Zazzau, muna yi maka fatan alheri tare da addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara maka lafiya, Ya tsawaita kwana da nisan rai cikin imani da ƙoshin lafiya.

SAKON BARKA DA JUMA'A. Mahukunta Shafin Zage-Zagi A Yau, Suna amfani da wannan dama wajen mika sakon Barka da Juma'a Zuw...
24/07/2026

SAKON BARKA DA JUMA'A.

Mahukunta Shafin Zage-Zagi A Yau, Suna amfani da wannan dama wajen mika sakon Barka da Juma'a Zuwa ga Mai Girma Sulaiman Ibrahim Dabo Wakilin Birnin Zazzau. Muna Addu'ur Allah Ya kara albarka, ya sadaka da dukkan alherin wannan Rana, ya kyautata Rayuwanka.

SAKON BARKA DA JUMA'A. Mahukunta Shafin Zage-Zagi A Yau, Suna amfani da wannan dama wajen mika sakon Barka da Juma'a Zuw...
24/07/2026

SAKON BARKA DA JUMA'A.

Mahukunta Shafin Zage-Zagi A Yau, Suna amfani da wannan dama wajen mika sakon Barka da Juma'a Zuwa ga Mai Girma Malam Bashir Shehu Idris Uban Garin Zazzau, Hakimin Gundumar Soba Muna Addu'ur Allah Ya kara albarka, ya sadaka da dukkan alherin wannan Rana, ya kyautata Rayuwanka.

Address

No 15 Kwarbai Zaria City
Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zage-Zagi A Yau. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zage-Zagi A Yau.:

Shortcuts

Share