A M T Hausa

A M T Hausa "AMT Hausa (African Media Television Hausa) kafar yada labarai ce mai zaman kanta.

Ba ta da alaƙa da kowace gwamnati, hukuma ko wata kafar yaɗa labarai sai dai idan an bayyana haka

12/07/2026
04/07/2026

"A duk faɗin Najeriya, babu gwamnan da ya kai Uba Sani aiki!"
Wannan shi ne ra'ayin Jamili Roja, inda ya bayyana cewa irin ayyukan ci gaba da Gwamna Uba Sani yake aiwatarwa sun sanya shi a gaba idan aka kwatanta da sauran gwamnoni a Najeriya.

28/06/2026

"Zan Maidaku Tamkar 'Ya'yana" a cewar Gwamna Uba Sani lokacin da ya kai ziyarar ta'aziyya gidan Matar nan da aka yiwa kisan gilla a Mararraban Jos.

DA DUMI-DUMI:Dangote Ya Sake Rage Farashin Fetur Da Naira 50 Kan Kowace Lita Daga ₦1,175 Zuwa ₦1,125Daga AMT HAUSA Matat...
25/06/2026

DA DUMI-DUMI:Dangote Ya Sake Rage Farashin Fetur Da Naira 50 Kan Kowace Lita Daga ₦1,175 Zuwa ₦1,125

Daga AMT HAUSA

Matatar Dangote ta sake rage farashin fetur da Naira 50 kan kowace lita, inda ta sauke shi daga Naira 1,175 zuwa Naira 1,125.

Kamfanin ya danganta matakin da sauƙaƙewar rikicin Gabas ta Tsakiya, wanda ya janyo raguwar farashin makamashi a kasuwannin duniya.

Rahotanni sun nuna cewa sabon farashin ya fara aiki nan take, Ana sa ran sabon ragin zai taimaka wajen rage tsadar fetur a wasu sassan ƙasar.

Kwamishinan muhalli Iliya Kefas ya tabbatar da haka ga manema labarai a Jalingo, yana mai cewa hakan ya zama dole saboda...
23/06/2026

Kwamishinan muhalli Iliya Kefas ya tabbatar da haka ga manema labarai a Jalingo, yana mai cewa hakan ya zama dole saboda samun damar ɗaukar sabbin ma’aikata a jihar.

DA DUMI-DUMI: Jam'iyyar PDP ta anguwar Pantami ta gudanar da taron jaddada goyon bayanta ga dan takarar Gwamnan jihar Go...
21/06/2026

DA DUMI-DUMI: Jam'iyyar PDP ta anguwar Pantami ta gudanar da taron jaddada goyon bayanta ga dan takarar Gwamnan jihar Gombe Professor Isa Ali Pantami.

Haka zalika jam'iyyar PDP ta karbi mutane sama da 2,800 da s**a sauya sheka daga jam'iyyun APC, ADC da LP zuwa jam'iyyar PDP domin marawa Professor Isa Ali Pantami baya a zaben 2027.

Yanzu Yanzu:Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari a ƙauyen Tsamiya da ke Ƙaramar Hukumar Bagudo a Jihar Kebbi,...
21/06/2026

Yanzu Yanzu:Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari a ƙauyen Tsamiya da ke Ƙaramar Hukumar Bagudo a Jihar Kebbi, inda s**a sace wani mazaunin yankin mai suna Alhaji Yusuf Bazamfare tare da ƙona wasu gine-gine.

Lamarin ya faru ne a daren Asabar, lokacin da maharan s**a mamaye yankin tare da harbe-harbe ba tare da ƙa’ida ba, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici.

Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce maharan sun ƙone wani wurin sintiri na rundunar NSCDC, da wani gidan karuwai, da kuma gidan wani mutum mai suna Sule Mai Goge.

Bayan aukuwar harin, Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar ya bayar da umarnin tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin domin ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Rundunar ta ce tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin ceto mutumin da aka sace tare da kamo waɗanda s**a kai harin, yayin da ta buƙaci mazauna yankin su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai don taimakawa yaƙi da ayyukan ta’addanci.

Sabbin rahotannin tsaro sun nuna cewa an samu ƙarin barazana a wasu sassan gabashin jihar Sakkwato, inda ake zargin mabi...
21/06/2026

Sabbin rahotannin tsaro sun nuna cewa an samu ƙarin barazana a wasu sassan gabashin jihar Sakkwato, inda ake zargin mabiyan fitaccen ɗan bindiga Bello Turji na gudanar da horaswa kan amfani da makamai da dabarun yaƙi a yankunan da ke kan iyakar Sakkwato da Zamfara.

Wani rahoton sirri da Basharu Altine, mai kula da ƙungiyar Movement for Social Justice and Good Governance a jihar Sakkwato ya fitar, ya ce ana gudanar da atisayen ne a yankunan Bingabale Kudu, Bafarawa Gabas da Bargaja. Rahoton ya ce mayaƙan da ke da alaƙa da Turji suna amfani da sabbin makaman da aka samu wajen atisayen.

An kuma yi zargin cewa wasu na kusa da Turji, ciki har da Illa Manawa da Dodo, wanda ake kyautata zaton ƙanensa ne, suna taka rawa a wannan shiri. A cewar Altine, bayanan sirri sun nuna cewa ana koyar da mayaƙan yadda za su sarrafa sabbin makamai masu ƙarfi da aka shigo da su yankin.

‎Rahoton ya kuma yi ikirarin cewa an kawo wasu sababbin makamai tare da sabbin mayaƙa da ake zargin suna da alaƙa da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya. Haka kuma, an ce wasu daga cikinsu suna da ƙwarewa a fannin yaƙi da sarrafa makamai, kuma an turo su ne domin ƙarfafa mayaƙan Turji a yankunan kan iyaka.

‎Altine, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara sa ido tare da binciken waɗannan bayanai domin hana duk wata barazana ga rayuka da dukiyoyin jama'a. Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan waɗannan zarge-zarge ba, kuma ba a samu damar tabbatar da su daga wata majiya mai zaman kanta ba.

TURKASHI: Ba Zan Zauna Karkashin Ikon Namiji Ba — Inji Nafeesat AbdullahiDaga AMT HAUSA Jarumar wasan kwaikwoyo Nafeesat...
21/06/2026

TURKASHI: Ba Zan Zauna Karkashin Ikon Namiji Ba — Inji Nafeesat Abdullahi

Daga AMT HAUSA

Jarumar wasan kwaikwoyo Nafeesat Abdullahi, ta ce ba ta ga dalilin da zai sa mace ta zauna ƙarƙashin ikon namiji a sunan aure ba, tana mai cewa aure ba ya cikin tsarinta.

A wani bidiyo da ya yadu, ta ce mace na iya gina rayuwarta da dukiya ba tare da dogaro ga namiji ba, tare da ƙaryata cewa aure ko haihuwa ne kawai ke tabbatar da kulawa ko addu’a Daga ya'ya a lokacin tsufa ko bayan mutuwa.

Kalaman nata sun jawo muhawara, inda wasu ke s**ar ta yayin da wasu ke kare ta kan ‘yancin ra’ayin ku

Labari Mai Ɗumi: Oyebanji na APC ya lashe zaɓen gwamnan Ekiti na 2026 da ƙuri’u 319,224, ya kayar da Oluyede na PDP da B...
21/06/2026

Labari Mai Ɗumi: Oyebanji na APC ya lashe zaɓen gwamnan Ekiti na 2026 da ƙuri’u 319,224, ya kayar da Oluyede na PDP da Bejide na ADC.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana ɗan takarar jam’iyyar APC, Biodun Oyebanji, a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Ekiti na shekarar 2026.

Oyebanji ya samu gagarumar nasara bayan ya tattara ƙuri’u 319,224, inda ya kayar da babban abokin hamayyar sa, ɗan takarar PDP, Dakta Wole Oluyede.

An gudanar da zaɓen ne a dukkan ƙananan hukumomi 16 na jihar, sai dai an samu zarge-zargen kura-kurai da sayen ƙuri’u da yawa, lamarin da masu sa ido kan zaɓen s**a yi Allah-wadai da shi.

Bisa ga sakamakon hukuma da INEC ta sanar, Oluyede ya samu ƙuri’u 40,543, yayin da ɗan takarar jam’iyyar ADC, Dare Bejide, ya samu ƙuri’u 12,872, inda ya zo na uku a jerin masu takara.

Babbar jami’ar tattara sakamakon zaɓen kuma shugabar gudanar da zaɓen, Farfesa Adenike Oladiji, ce ta sanar da sakamakon a safiyar Lahadi, inda ta bayyana Oyebanji a matsayin wanda aka zaɓa bisa cika dukkan sharuddan kundin tsarin mulki na samun nasara a zabe

Address

Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when A M T Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to A M T Hausa:

Shortcuts

Share