DCL Hausa

DCL Hausa DCL Hausa na yaki da labaran bogi ta hanyar kawo muku hirarraki da labarai sahihai
(8)

25/08/2026

Har yanzu ina kan matsayata ta dawo da tallafi man fetur a Nijeriya - Atiku Abubakar

25/08/2026

Ban ji dadin yadda hadimin Tinubu Ibrahim Masari da Gwamnan Yobe s**a bai wa kungiyar Izala ta Malam Jingir kyautar naira miliyan 600 ba alhali jihohinsu na fama da matsaolin yunwa da cututtuka - Prof. Usman Yusuf

Ghana na shirin fara sayar wa Nijeriya wutar lantarkiGhana ta bayyana shirin fara samar da wutar lantarki da za ta rika ...
25/08/2026

Ghana na shirin fara sayar wa Nijeriya wutar lantarki

Ghana ta bayyana shirin fara samar da wutar lantarki da za ta rika sayar wa Nijeriya, inda Nijeriya za ta samar da iskar gas, Ghana kuma ta yi amfani da iskar wajen samar da wutar lantarki.

Ministan makamashi na Ghana, John Abdulai Jinapor, ya ce tsarin zai kasance kamar “musayar kayayyaki”, inda Ghana za ta mayar wa Nijeriya wani kaso na wutar da ta samar daga iskar gas ɗin.

Kafar DW Africa ta ruwaito cewa za a yi amfani da bututun iskar gas na Afirka ta Yamma wajen gudanar da shirin. Bututun ya samo asali ne daga Nijeriya, ya ratsa Benin da Togo kafin ya isa Ghana.

Nijeriya na da kusan tiriliyan 210.5 na cubic feet na iskar gas, yayin da Ghana ke samar da wutar lantarki ga ƙasashen Benin, Togo, Burkina Faso da Ivory Coast.

25/08/2026

Labaran DCL Hausa na Bidiyo 25/08/2026

Shugaban Nijeriya ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta ceto mutanen da aka sace a jihar Niger

Sheikh Jingir mutumin kirki ne da ke ƙoƙarin samar da haɗin kan ƙasa, Inji Gwamnan Kano

Wani Shugaban ƙaramar hukuma, ya umarci mutanen da ba sa goyon bayan APC da su fice daga yankin sa

Mai Gabatarwa: Yahanasu MD Ibrahim

25/08/2026

Yadda aka gudanar da bikin Maulidi a Borno

25/08/2026

Ba za mu lamunci yadda wasu Malamai ke fakewa da addini don tallata Tinubu ba - Prof Usman Yusuf

Mutumin mai suna Rabiu Mukhtar, mai shekaru 34, wanda ke zaune a Tudun Yola Quarters, ya fusata ne sakamakon karar kiɗan...
25/08/2026

Mutumin mai suna Rabiu Mukhtar, mai shekaru 34, wanda ke zaune a Tudun Yola Quarters, ya fusata ne sakamakon karar kiɗan da ake yi a wajen bikin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana cewa wanda ake zargin ya fito daga gidansa ne riƙe da makami sannan ya yi wannan ɓarna, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu uku.

Ba zan yaudari mutane; na dawo da tallafin fetur sannan na cire shi ba tare da la’akari da illar da hakan zai yi ga jama...
25/08/2026

Ba zan yaudari mutane; na dawo da tallafin fetur sannan na cire shi ba tare da la’akari da illar da hakan zai yi ga jama’a ba in ji Atiku Abubakar, dan takarar shugabancin Nijeriya na ADC

Zan jagoranci yadda Tinubu zai samu kuri’u miliyan 20 daga jihohin Nijeriya a kungiyata ta Tinubu Again- Matawalle
25/08/2026

Zan jagoranci yadda Tinubu zai samu kuri’u miliyan 20 daga jihohin Nijeriya a kungiyata ta Tinubu Again- Matawalle

25/08/2026

Shugaban Karamar Hukumar Kuje ya ce ba zai lamunci rashin goyon bayan Tinubu da APC ba

Address

Arewacin Najeriya
Kaduna
800264

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DCL Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DCL Hausa:

Shortcuts

Share