Creatives Media TV

Creatives Media TV Media Activist, Movie Subtitles, Graphic Designs, Written translations, video I.V's, News updates, E

01/05/2025
Happy Eid from all of us.
31/03/2025

Happy Eid from all of us.

27/03/2025

Sarkin Kano na 15th Alhaji Aminu Ado Bayero ya janye hawan sallah karama saboda dalilin tsaro

26/03/2025

*Ana fargabar sojojin Najeriya da dama sun mutu bayan harin Boko Haram a Barno*

26/03/2025
25/03/2025

DA DUMI-DUMI: Za a biya masu NYSC bashin alawus ɗinsu

Rundunar 'yansadan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ce ta k**a mutum 12 da zargin kai wa masallaci hari a Kaduna da ke ar...
22/03/2025

Rundunar 'yansadan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ce ta k**a mutum 12 da zargin kai wa masallaci hari a Kaduna da ke arewacin ƙasar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ta Kaduna, DSP Mansur Hassan, ya fitar ta ce harin ya yi sanadin kashe wani matashi mai suna Usman Mohammad mai shekara 23.

A cewar DSP Mansur, rundunar ƴansandan ta samu rahoto daga wani mazaunin yankin Rigasa cewa ƴandaba ɗauke da mak**ai na shirin kai hari kan masu sallar Tahajjud.

"Da jin rahoton ne kuma dakaru s**a bazama amma kafin su ƙarasa har sun daɓa wa wani matashi mai suna Usman Mohammed wuƙa, wanda likita ya tabbatar da mutuwarsa a asibiti," in ji shi.

Ya ce sun isa wurin ne bisa rakiyar dakarun sa-kai na Civilian Joint Task Force (CJTF), kuma tuni sun ƙaddamar da cikakken bincike kan lamarin.

Wasu alƙaluma da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar ya nuna yadda kusan baƙin haura dubu 9 s**a rasa rayukansu akan hanyar...
22/03/2025

Wasu alƙaluma da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar ya nuna yadda kusan baƙin haura dubu 9 s**a rasa rayukansu akan hanyar shiga nahiyar Turai don cirani cikin shekarar da ta gabata ta 2024.

Alƙaluman, waɗanda ke ƙunshe cikin rahoton da hukumar kula da Ƙaurar Baƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar a wannan Juma’a, ya nuna cewa ƴan cirani dubu 8 da 938 ne s**a rasa rayukansu a mabanbantan hanyoyinsu na bulaguro don cirani a manyan ƙasashe.

Rahoton ya nuna cewa wannan ce shekara ta 5 a jere da ake ganin mafi ƙololuwar ƴan ciranin da ke mutuwa akan hanyarsu ta zuwa cirani.

Mataimakiyar babban daraktan hukumar kula da ƙaurar baƙi ta IOM Ugochi Daniels ta bayyana cewa abin takaici ne yadda ɗimbin ƴan cirani ke mutuwa kowacce shekara ta dalilin matsalar da za a iya magancewa ko kuma kange ta daga faruwa.

A cewar jami’ar lamarin da tayar da hankali matuƙa, ganin cewa kowanne rai da aka rasa, ɗan uwa ne ga wani da rashinsa zai jefa ahalinsa cikin zullumi.

Hukumar IOM ta ce adadin da ake iya fitarwa na yawan ƴan ciranin da ke mutuwa kowacce shekara ka iya zarta hakan, ganin cewa akwai ɗimbin waɗanda ke rasa rayukansu ba tare da an tattara alƙalumansu ba.

Hukumar ta ci gaba da cewa hatta waɗanda aka iya samun gawarwakinsu ba a iya gano ahalinsu.

Nahiyar Asia ce kan gaba a yawan mutanen da ke mutuwa a wannan balaguro da adadin dubu 2 da 778 biye da Afrika mai dubu 2 da 242 kana Turai da mutum 233.

Sanata Ali Mohammed Ndume, ɗan majalisar dake wakiltar Jihar Borno ya ce shi baya goyan bayan dakatar da zaɓaɓɓen gwamna...
21/03/2025

Sanata Ali Mohammed Ndume, ɗan majalisar dake wakiltar Jihar Borno ya ce shi baya goyan bayan dakatar da zaɓaɓɓen gwamnan jihar Rivers Simi Fubara, da kuma ƴan majalisun dokoki k**ar yadda shugaban ƙasar ya yi.

Ndume ya ce duk da yake harkar tsaro ta k**a hanyar taɓarɓarewa a jihar, korar zaɓabben gwamnan ba abu ne mai kyau ba, duk da yake ya goyi bayan kafa dokar ta bacin.

Ya ƙara da cewar, ta yaya za'a cire zaɓaɓɓen gwamna domin maye gurbin sa da soja?

Ɗan majalisar ya kuma amsa zargin da aka yiwa majalisar ƙasa cewar ita ma ta gaza wajen kasa sasanta rikicin da ya dabaibaye majalisar dokokin Rivers, wadda ta rabe gida biyu har zuwa lokacin da Kotun Koli ta yanke hukunci akan takaddamar.

Jagoran jam'iyyar adawa ta NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan ayyana dokar ta-...
21/03/2025

Jagoran jam'iyyar adawa ta NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan ayyana dokar ta-ɓaci da ya yii a jihar Rivers da ke kudancin ƙasar nan.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis da dare, Kwankwaso ya siffanta matakin na Tinubu da "mai haɗari ga dimokuɗiyya".

A ranar Juma'a ne Tinubu ya sanya dokar da ta dakatar da Gwamna Fubara, da majalisar dokokin jihar tare da maye gurbin gwamnan da kantoman riƙo saboda abin da ya kira "rashin doka da oda" sak**akon rikicin siyasa tsakanin Fubara da tsohon Gwamna Nyesom Wike.

"Ina ganin rikicin siyasar da ake ciki a Rivers bai isa ya sa a ayyana sashe na 305(1) na kundin tsarin mulki ba," in ji shi.

"Abin da ya fi damu na ma shi ne yadda majalisun dokokin ƙasa s**a amince da buƙatar shugaban ƙasa. Na yi fatan ba za su yarda da wannan abu da ya karya doka ba...Wannan mataki nasu zai kawo wa dimokuraɗiyyarmu cikas."

20/03/2025

*May Allah’s immaculate grace and exceptional wisdom conquer your life as you celebrate this holy month of Ramadan. Have a blessed and peaceful Iftar!*

*Iftar Mubarak*

Address

Kaduna

Telephone

+2347067682029

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Creatives Media TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Creatives Media TV:

Share