Adalci multimedia Tv

  • Home
  • Adalci multimedia Tv

Adalci multimedia Tv Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Adalci multimedia Tv, Media/News Company, .

11/09/2026

Kakakin Jam’iyyar APC na Jihar Kaduna, Muhammad Sani Haruna, ya bai wa al’ummar jihar Kaduna tabbaci cewa Gwamna Sanata Uba Sani zai ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da kawo ci gaba a fadin jihar.

Muhammad Sani Haruna ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Uba Sani ta himmatu wajen inganta rayuwar al’umma tare da aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa.

Senator Uba Sani zai runanya ayukan raya kasa idan aka zabeshi zango na 2





Yanzu wannan mutumin da yake yankan farce Yana iya fin Kamsilansu musamman ma idan a ce Ibrahim Masari ne zai rika biyan...
11/09/2026

Yanzu wannan mutumin da yake yankan farce Yana iya fin Kamsilansu musamman ma idan a ce Ibrahim Masari ne zai rika biyan kuɗin aikin.
🤌😂😂😂😂😂

11/09/2026

Shugaban ‘Yan Shinkafa da Wake da Mai da Yaji na Siyasa, Alhaji Ismail Batir Condem, ya bayyana matsayinsa kan siyasar Kaduna da Najeriya.
Alhaji Ismail Batir Condem ya bayyana cewa a jihar Kaduna, za su ci gaba da mara wa Sanata Uba Sani baya a matsayin Gwamnan Jihar Kaduna.
Haka zalika, ya bayyana cewa a matakin tarayya, za su mara wa Alhaji Atiku Abubakar baya domin ya zama Shugaban Ƙasar Najeriya a zaben 2027.
Ya ce wannan matsaya tasu ta samo asali ne daga yadda suke ganin ya kamata a samu shugabanci mai dacewa da muradun al’umma.
Rahoto: Adalci Multimedia TV



Senator Uba Sani

11/09/2026

I got over 30 reactions on one of my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

10/09/2026

Shirin tsumagiya na yau alhamis 10-9-2026

09/09/2026
09/09/2026

Abdullahi Suleiman: ADC Ta Samu Karbuwa Bayan Shigar Malam Nasir El-Rufa’i

Jigo a jam’iyyar ADC, Abdullahi Suleiman, ya bayyana cewa shigar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, cikin jam’iyyar ADC ya kara mata karbuwa da farin jini a tsakanin al’umma.

Abdullahi Suleiman ya ce kasancewar Malam Nasir El-Rufa’i a cikin jam’iyyar ya kara mata armashi, tare da samar da karin kwarin gwiwa ga masu goyon bayan jam’iyyar.

Haka zalika, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya daura damarar dawo da Najeriya kan turbar ci gaba tare da farfado da tattalin arzikin kasar.

Daga karshe, Abdullahi Suleiman ya yi kira ga al’ummar Karamar Hukumar Igabi da su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa Bello Muhammad Jalo zai kawo sauyi tare da dora Karamar Hukumar Igabi a kan turbar ci gaba da samun nasara.

Daga: Adalci Multimedia TV

K.mashi Multimedia



Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, sun bukaci Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai r...
07/09/2026

Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, sun bukaci Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), da ya janye wani zargi da ya yi kan tsohon gwamnan, ko kuma ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da zargin. Ko kuma ya fuskanci matakin shari'a.

A cikin wata sanarwa da Hon. Mohammed Bello El-Rufai ya fitar a madadin iyalan, sun bayyana matuƙar damuwa kan kalaman da Janar Christopher Musa ya yi a ranar 3 ga Satumba, 2026, yayin wata hira kai tsaye a shirin Politics Today na Channels Television.

A yayin shirin, an bayyana cewa Ministan Tsaron ya zargi Nasir El-Rufai da hannu wajen tsarawa da shirya kashe-kashen mutane a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamnan jihar.

07/09/2026

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Adalci multimedia Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share