24/07/2026
Menene Wajiban Sallah?
Wajiban sallah guda takwas ne, kuma su ne:
1. Duk sauran takbirori, ban da Takbiratul Ihram.
2. Faɗin: "Sami'Allahu liman hamidah" ga liman da kuma wanda yake sallah shi kaɗai.
3. Faɗin: "Rabbana wa lakal hamd."
4. Faɗin: "Subḥāna Rabbiyal 'Aẓīm" sau ɗaya a cikin rukū'u.
5. Faɗin: "Subḥāna Rabbiyal A'lā" sau ɗaya a cikin sujada.
6. Faɗin: "Rabbi-ghfir lī" a tsakanin sujada biyu.
7. Tashahhud na farko.
8. Zama domin Tashahhud na farko.