14/07/2025
RASUWAR BUHARI: Ko Zage Shi, Ko Ka Yi Masa Mùmmùnaŕ Fata, Insha Allahu Ya Huta
Daga Amb Azaz
A matsayina na ɗan asalin Borno, wanda na tsinci kaina cikin tsananin rikicin Boko Haram, dole ne in miƙa godiya da girmamawa ga waɗanda s**a sadaukar da rayuwarsu don kare mu. Wannan ba magana bace ta siyasa ko jin kai wannan gaskiya ce da tarihi ba zai iya goge ba.
Baba Muhammadu Buhari tsohon shugaban ƙasa da zuciya ɗaya, na ce Allah ya jikan sa, ya jikansa da rahamarsa. Duk da cewa wasu suna zage-zage bayan rasuwar sa, ni dai na yafe masa. A matsayina na ɗan ƙasa, na roƙi Allah ya yafe masa. Wanda ya mutu, ya riga mu gidan gaskiya, koma kowa lokaci kawai yake jira.
Ina kuma miƙa godiya ta musamman ga Gwamna mai rikon gaskiya, Prof. Babagana Umara Zulum. Wannan gwarzon mutum ya kasance ginshiƙin zaman lafiya da ci gaban Borno. Ya ɗauki nauyin da yawa, ya ƙalubalanci masu tada ƙayar baya, ya jajirce wajen tallafa wa talakawa da maido da martabar jihar mu. Duk wanda ke da zuciya, sai ya yaba masa.
Mutuwar Buhari, ba ƙaramin rashi bane ga Zulum. Ya rasa uban gida wanda yake kauna da samun goyon baya gare shi. Amma muna addu’a Allah ya ba ka ƙarfin zuciya Prof, ya kare ka daga dukkan sharri, ya kawo ƙarshen masifofin da ke addabar Borno da Najeriya baki ɗaya.
Ya Allah, Ka jikan Buhari, Ka sanya shi cikin Aljannatul Firdaus. Kuma Ka baiwa Prof. Zulum nasara a aikinsa.