29/09/2025
A ranar Lahadin data gabata 28/09/2025, 'Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya amshi baƙuncin Gidajan Malamai daga birnin Zazzau da s**a haɗa gidan Kona, gidan sarkin Ladanai, gidan Sheikh AbdulQadir Banufe, gidan Alhazawa, gidan marigayi Sheikh Aliyu Mai Yasin wanda Sheikh Muhammad Zakir Shamsuddeen (Young Sheikh) ya wakilta, Gidan Limamin Zabi Gidan Limamin Dogarawa da kuma Malam Sunusi Mai Ashafa, da gidan Sheikh Ibraheem Kakaki.
Malaman sun jajantawa Malam Zakzaky (H) bisa ga waƙi'ar buhari (L) na shahadar Almajirai da Ƴaƴansa, sannan sunyi Addo'ar Allah ya amshi shahadar su.
Malamin ya yi masu ta'aziyyar wasu malaman da aka rasa ya roki Allah ta'ala ya gafarta masu, sannan ya aika da saƙon gaisuwa ga sauran ƴan'uwa da masoya.
Hausa TV