Littafin yaki by ibrahim bebeji

Littafin yaki by ibrahim bebeji Littafin yaki,soyayya,ban dariya etc

13/03/2025

Ramadan mubakrak

26/01/2025

ALLON SIHIRI
Littafi na Uku (3)
Part D
Typing Ibrahim bebji
09079376322
Buy ur data Here for all network

LOKACIN da Bakom Jarumi ya fita daga cikin
wannan daki na kayan sihirin Bokab Darbusa sai
ya
tunkari inda turakarsa ta barci take,kai tsaye sai
kace
dama can yasan kowanne lungu da sako na
gidan.Da isowarsa kofar turakar sai ya tsaya cak
sannan ya juyo baya.Take yayi arba dasu
sarauniya
Akisatul Sauwara suna biye dashi.Cikin matukar
mamaki ya dubesu sannan ya dubi Dazyan s**ayi
magana k**ar yadda s**a sabaDazyan ya dubi
su
Sarauniya Akisatul Sauwara yace shugabana
yace na
gaya muku ba zai taba yiyuwa ba ya kwana da
dayanku a cikin daki guda ba,shi kadai zai
kwanta a
cikin wannan turaka tare da ALLON SIHIRI,don
haka
ya zama wajibi kowannenku ma yaje ya nemi
inda
zai sa hakarkarinsa.Kuma yace lallai ku kwantar
da
hankalinku tamkar tsumma a randa,yayi muku
alkawarin cewar babu abinda zai taba lafiyar
jikinku
koda kuwa kwarzane guda da izinin
ubangijinsa.Koda gama fadin hakan sai Bakon
Jarumi ya shige cikin turakar ya janyo kofar ya
rufeta ruf ya bar Dazyan tsaye sororo a kofar
dakin
tare dasu Sarauniya Akisatul Sauwara,suma sunyi
cirko cirko suna mamakin bakon jarumin.Abinda
ya
fara fado musu arai shine."Menene dalilin dayasa
bakon Jarumin bazai iya kwana tare dasu ba a
cikin
daki guda?Kuma menene dalilin dayasa duk a
tsawon wannan lokaci bai yarda anga fuskarsa
ba?
To waishin ma shi Namije ne ko Mace?Lallai
akwai
bukatar su tantance hakan domin su san hanyar
dazasu bi su rabashi da ALLON SIHIRI.Sarauniya
Akisatul Sauwara ta dubi dan wada Dazyan tace
ashe maigidan naka ma bai yarda da kai ba
tunda ya
kasa kwana tare dakai a cikin daki guda?Koda jin
wannnan batu sai Dazyan ya takarkare ya bushe
da
dariya lokaci guda kuma yace yake wannan
sarauniya kiyi sani cewa ni kaina bansan ko waye
maigidana ba,ban san matsayinsa ba ko
asalinsa,hasalima haduwata dashi bata wuce ta
shekara uku ba,kuma a tsawon wannan lokaci
ban
taba ganin fuskarsa ba,kuma ban taba jin
muryarsa
ba bare kuda kuka hadu dashi a yau din
nan.Shawarar da zan baku kawai itace,ku yarda
da
duk abinda kukaji ya fada,kuyi imani dashi,in ba
haka ba kuwa karshenku shine NADAMA gami da
yin MUMMUNAN KARSHE!Nidai yanzu zanje na
nemi
inda zan kwanta saboda na gaji likis kuma nima
barci nakeji.Amma maigidana yace na shaidawa
miki
ke Sarauniya Akisatul Sauwara cewa lallai kema
ki
ware dakinki ke kadai domin a ka'idar addininmu
haramun ne kiyi cudanya da mutanen da basu
kasance muharramanki ba.Koda gama fadin haka
sai
dan wada Dazyan ya hango wani karamin daki
dake
can gefe daya wanda kofarsa ke bude
wanwar,kawai
sai ya tafi izuwa cikin dakin ya kunna kai
ciki.Koda
ganin haka sai Sarki Darmanu ya bishi da
sauri.Ita
kuwa Sarauniya Akisatul Sauwara sai ta tsaya ta
k**a duru duru ta rasa dakin dazata shiga.Daga
can
kuma sai ta nufi wani babban daki wanda
kofarsa ke
rufe.Da isarta sai tasa hannunta ta murda
kofar,bisa
mamaki sai taga kofar ta bude da
kanta.Sarauniya
Akisatul Sauwara ta kunna kai izuwa cikin
daki.Tana
shiga sai kanta ya daure tamau ta kamu da
tsananin
mamaki,ba don komai ba sai saboda ganin irin
kayan kawar dake cikin dakin.A tsakiyar dakin an
ajiye wani lumtsumen gado mai girman gaske
wanda
aka cikashi da kayan taushi na alfarma.Sannan
kuma akwai kofar kewaye a cikin dakin.Sarauniya
Akisatul Sauwara ta leka cikin kewayen shima
taga
an kawatashi da bahon wanka na zinare.Kawai
sai ta
koma falon tayi tsalle ta fada kan wannan
luntsumemen gado cikin jin dadin huce
gajiya.Amma
kuma har a sannan raunikan jikinta basu daina yi
mata dan zogi da radadi ba.Nan take Sarauniya
Akisatul Sauwara ta fada kogin tunani.
¤P¤H¤Y¤S¤I¤C¤I¤S¤T¤
AL'AMARIN Yarima Lubainu kuwa,bayan yaga
kowa
ya shige cikin daki an tafi an barshi shi kadai a
tsaye sai ya k**a yawo a cikin gidan yana
neman
dakin dazai shiga ya kwanta shi kadai.Ba don
komai
yake son ya sami inda zai kwanta ba shi kadai
sai
saboda ya sami damar dazai zauna yayi tunani
da
nazari ya yankewa kansa shawarar da zata
fissheshi.Da yake wannan fada ta Boka Darbusa
tana
da tsananin girma tamkar gari guda,kuma gashi
anyi
gine gine da yawa a cikinta na kawa,sai Yarima
Lubainu ya rude ya rasa ma bangaren dazai
shiga
domin da yayi yunkurin shiga wani dakin saiya
hango wani wurin wanda ya fishi kyau da
kawa.Yana
cikin wannan kai kawo ne ya shigo wani bangare
dabam na musamman wanda aka killaceshi a
wuri
mai ban al'ajabi.Shi dai wannan wuri ya kasance
tamkar lambu kuma an kewayeshi da katangar
zinare,sannan an zuba shuke shuke na 'ya'yan
itatuwa na marmari kala kala ga kuma tsuntsaye
masu kyau ababan sha'awa kuma kofar wannna
lamby a bude take.Har Yarima Lubainu ya gifta
kofar
zai wuce gaba sai ya jiyo shesshekar kuka cikin
muryar MACE!Al'amarin dayai matukar bashi
mamaki kenan,domin a zatonsa bandashi dasu
bakon jarumi babu sauran wani mahaluki a cikin
wannan gida.Yarima Lubainu ya dawo da baya ya
tura babbar kofar kambun ya kunna kai ciki.Yana
shia sai ya kame,idanunsa s**a zazzaro
sak**akon
abinda yayi arba dashi.Ba komai ne abinda yayi
arba
dashi din ba face wata zabgegiyar kyakkyawar
Budurwar ALJANA a daddaure cikin wata
murtukekiyar sarkar tsafi waccce ta kanannade
hannayenta,kafafuwanta da sauran sassan
jikinta,kuma sarkar an zagayata ne a jikin wata
dirkar tsafi mai tsananin kaurin gaske wacce fiye
da
rabinta ya nutse a cikin karkashin kasa.Abin daya
daurewa Yarima Lubainu kai dangane da wannan
Aljana shine ko a bakin masana labarai bai taba
jin
cewar akwai halitta mai siffarta ba.Rabin jikinta
na
bil'adama ne,daga kasan cibiyarta zuwa
kanta.Daga
gwiwar kafafunta zuwa tafin
kafafunta kuwa na Aljanu ne.Kash!in badon
wannan
ratsin siffa ta Aljana ba dake jikinta da Yarima
Lubainu zai iya cewa duk duniya babu wata 'YA
MACCE mai kyan wannan budurwa ba.Koda
Yarima
Lubainu ya hada idanu da wannan budurwa yaga
idanunta sunyi sharkaf da hawayemkuma gata a
daure cikin sarka,sai nan take yaji ya kamu da
tsananin tausayinta.Amma da ya tuna cewa nan
fa
gidan Boka Darbusa ne babu mamaki ma wani
tuggun ne aka shirya musu aka ajiye wannan
Aljana
domin su fada tarkon wahala,sai kawai ya juya
da
nufin ya fice daga cikin lambun,kawai sai yaji
aljanar
ta budi baki cikin murya mai zaki da bai taba jin
irinta ba kuma mai tsananin taushin gaske
tace,haba
yakai Yarima Lubainu,ya ya kai daka kasance
mai
tausayi da jin kai zaka tafi ka barni a cikin
wannan
hali?Ka sani cewa shekara uku kenan wannan
azzalumin Boka Darbusa na tsare dani anan,ina
jiran
ranar da zakuzo ku koreshi daga cikin wannan
fada
ku ceceni.Koda jin wannan batu sai mamaki ya
sake turnuke Yarima Lubainu ya dubi Aljanar
cikin
alamun rashin yarda yace,wace ce ke kuma ya
akayi
kika sanni har kika san cewa zamu zo wannan
fada
mu kori Boka Darbusa?Sa'adda aljanar taji
wadannan
tambayoyi guda biyu ko uku sai hawaye ya zubo
mata,tace ni sunana BADI'ATUL SARIRA,Kuma
nice
'ya guda daya jal a wajen mahaifina Sarkin
Bokayen
Aljanu na duniya kaf,wato ZARHASU IBINI
SAMBILA.A cikin wannan duniya kaf in banda
Boka
Darbusa babu wani mahaluki daya kai mahaifina
karfin sihirin tsafi da kuma tarin sirrikansa.Loka
cin
da mahaifina da Boka Darbusa s**a gano cewa
karfinsu yazo daya a sirrin tsafi sai s**a zamo
manyan ABOKAN GABA ya zamana cewa
kowannensu na kokarin ya hallaka dayan ya
rabashi
da dukkan sirrikan tsafinsa.Asalin wannan ALLON
SIHIRI da kuka daukoshi a dakin tsafin Boka
Darbusa
a hannun mahaifina yake,daga baya ne bayan
Boka
Darbusa ya samu nasarar kashe shi ya
daukeshi.Ba
komai ne yasa Boka Darbusa yaki kasheni ba ya
daureni anan face cewa koya hada ragowar bari
biyun na ALLON SIHIRI dana Mahaifina bazai iya
cika
burinsa ba face nidin nan na karanta masa
wadansu
dalasiman tsafi dake jikinsa na fassara masa su
yadda zai fahimta,saboda yaren a akayi rubutun
dashi a jikin Allon Sihirin mahaifina ni kadai ce na
iya shi a duk fadin duniya,saboda mahaifina ne
ya
kirkireshi kuma tun ina yarinya karama ya koya
minshi.Ina mai rokonka daka taimakeni ka
kwanceni
daga cikin wannan sarka yanzu in dai kayi min
haka
ni kuma nayi maka alkawarin cewa zan iya raba
bakon jarumi da wannan ALLON SIHIRI,a cikin
dakika
daya jal,sannan na daukeka na kaika KOGIN
BAHAR
IMFAL a cikin abinda baikai rabin sa'a ba mu
shiga
cikin karkashin kogin na tsinko maka dan itaciyar
dazaka sha ka warke daga cutar da YARIMA
MANGUL ya sanya maka ka dawo cikakken da
namiji
ka koma ga matarka,babbar masoyiyarka
YAZARINA
ku fara sabuwar rayuwar aure cikin farin
ciki.Ladan
wannan aiki nawa kawai shine ka bar min
wannan
ALLON SIHIRI.Koda Aljanar tazo nan a jawabinta
sai
hankalin Yarima Lubainu ya dugunzuma ainun ya
rasa irin amsar da zai bata.Abinda ya fado masa
a
rai shine,shin zai iya yarda da wannan Aljanr
kuwa?
To ai idan ma ya yarda da ita k**ar yaci amanar
su
Sarauniya Akisatul Sauwara ne!
WACE IRIN SHAWARA YARIMA LUBAINU ZAI
YANKE
AKAN WANNAN DAMA DA YA SAMU?
MAI ZAI FARU TSAKANIN SU SARAUNIYA
AKISATUL
SAUWARA DA BAKON JARUMI IDAN GARI YA
WAYE?
WANE HALI BOKA DARBUSA YAKE CIKI BAYAN
YA
FALFALA DA GUDU IZUWA CIKIN DAJI BAYAN
SUN
FAFATA AZABABBEN YAKI SHI DA BAKON
JARUMI
DON YA TSIRA DA RAYUWARSA?
WANENE BAKON JARUMIN DAYA BAYYANA?
YAUSHE YARIMA YAKE CIKA BURINSA NA
SAMUN
LAFIYA DAGA LALURAR DA YAKE CIKI?
WAISHIN INA LABARIN YARIMA MANGUL?
WAYE ZAI MALLAKI ALLON SIHIRI.
Mu hadu a littafi na hudu(ALLON SIHIRI-4)don jin
cigaban wannan kayataccen kasaitaccen labari.
Akwai data fa nakowanni network aciki farashi mai sauki
Mtn
Airtel
Glo
Dan Karin bayani akirani a 09079376322
9mobile saina jiku
Ibrahim bebeji ne 🤩🤩🥳

13/01/2025

ALLON SIHIRI
Littafi na uku (3)
Part C

Labari yazo ma bebeji cewa
Batun ALLON SIHIRIN Boka Darbusa wanda
mukazo
nema yanzu a cikin gidansa.Koda jin wannan
tambaya sai Bakon Jarumin ya dubi Dazyan ya
sake
yi masa zancen kurame da hannu.Dazyan ya dubi
sarauniya Akisatul Sauwara yace maigidana yace
yanzu zamu bazama neman wannan ALLON
SIHIRI a
cikin wannan gida,amma ku ukun ne zaku fara
neman ALLON SIHIRIN da karfinku sihirinku,idan
kuka kasa sai mu roki ubangijinmu ya nuna mana
inda yake mu daukeshi da izininsa mu baku.Koda
gama fadin hakan sai Yarima Lubainu ya dubi su
Sarauniya Akisatul Sauwara yace to kunji yanzu
dai
shawara ta rage ga mai shiga rijiya.Sarauniya
Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu s**a dubi
junansu s**ayi murmushi kuma s**a budi baki
cikin
hadin murya s**a ce muma mun amince da
hakan.Nan take Sarauniya Akisatul Sauwara,Sarki
Darmanu da Yarima Lubainu s**a sake kunna kai
izuwa cikin gidan Boka Darbusa kowannensu na
karanta dalasiman tsafinsa a cikin ransa.Shi
kuwa
Bakon Jarumi da Bawansa Dazyan sai s**a bisu
a
baya kawai suna kallonsu kuma suna neman
tsarin
Allah daga dukkan mugun abun dake cikin
gidan.Abu dai k**ar wasa saida su sarauniya
Akisatul Sauwara s**a shiga duk wani sako,lungu
da
dukkan dakunan dake gidan kuma s**a caje
komai
da ko ina a cikin gidan amma har s**a gaji likis
ko
alamar ALLON SIHIRI basu gani ba.Daga karshe
ne
s**a ga wani daki mai katuwar bakar kofar karfe
a
kulle wanda ya rage basu shiga ba.Ita kanta
kofar
wannan daki ta isa abar tsoro domin anyi tane da
mulmulallen karfe mai kaurin gaske,sannan akwai
hoton KWARANGWAL din kan BIL'ADAMA da
kafafuwansa a jikinta alamar cewa wannan
daki,daki
ne me mugun hadari wanda mutum zai iya rasa
rayuwarsa a ciki.Koda s**ayi arba da kofar
wannan
daki sai sarauniya Akisatul Sauwara,Yarima
Lubainu
da sarki Darmanu s**a dubi junansu s**ayi cirko
cirko suna kallon kofar.Kawai sai Sarki Darmanu
ya
dubi sarauniya Akisatul Sauwara yace ai sai fara
jarraba taki sa'ar mu gani.Ba tare da wata
gardama
ba kuwa sarauniya Akisatul Sauwara ta k**a
kofar
taja da nufin ta budeta amma sai ta kasa kawai
sai ta
fara karanta wadansu dalasiman tsafi tana
tofawa a
kofar.Maimakon kofar ta bude sai wata irin iska
mai
karfin gaske ta fito daga cikin kofar ta doki kirjin
Sarauniya Akisatul Sauwara tayi sama da ita da
karfi,bayanta ya gwaru da jikin bango ta fado
kasa a
galabaice.Koda ganin abinda ya faru sai hankalin
Sarki Darmanu ya tashi jikinsa ya k**a tsuma ya
dubi Yarima Lubainu yace saura kai.Yarima
Lubainu
ya numfasa yace shin ka mantane kai abinda
Sarauniya Akisatul Sauwara ta kasa yi nima
bazan
iya ba.Koda jin haka sai Sarki Darmanu ua ciza
lebe
sannan ya dunkule hannayensa biyu yayi nuni
dasu
izuwa ga kofar yana mai rintse idanu.Faruwar
hakan
keda wuya sai iska mai karfi ta fito daga cikin
hannayensa ta rinka duka kofar dakin tana
jijjigata
k**ar zata burma ciki amma sai hakan ya
gagara.Maimakon ma kofar ta bude sai ta maido
masa da iskar hannun nasa ta sureshi sama ta
rinka
katantanwa dashi a sama ya rinka ihu yana
neman
hallaka.Koda ganin haka sai Bakon Jarumin ya
daka
tsalle sama ya riko rigar Sarki Darmanu.Take
iskar
tsafin ta dauke dif sarki Darmanu ya fado kasa
tim.Shi kuwa Bakon Jarumin sai ya diga a kasa
bisa
kafafunsa cikin koshin lafiya.Sarki Darmanu kuwa
saida hancinsa da bakinsa s**a k**a yoyon
jini.Bakon Jarumin ya dubi Dazyan yayi masa
zance
da hannu sannan Dazyan ya dubi sarauniya
Akisatul
Sauwara da Sarki Darmanu yace shugabana yace
zai
bude muku wannan kofa da izinin ubangijinsa
wato
ubangijin musulunci.Koda jin haka sai Sarauniya
Akisatul Sauwara ta dubi Yarima Lubainu da
Sarki
Darmanu tayi musu kallon ko menene ra'ayinsu?
Duk
su biyun sai s**a sunkui da kawunansu
kas.Faruwar
hakan keda wuya sai Sarauniya Akisatul Sauwara
ta
dubi Bakon Jarumi tace mun baka dama.Dajin
haka
sai Bakon Jarumin ya tunkari kofar dakin kai
tsaye
ba tare da shakkar komai ba,da isarsa bakin kofar
sai ya dungureta da dan yatsansa guda
daya.Take
kofar ta bude a hankali tamkar yaro ne karami
wanda
baifi shekara hudu ba ya turata ta bude din.Saida
kofar ta gama wangamewa gaba dayanta sannan
su
Yarima Lubainu s**a matso kusa da Bakon
Jarumin
suna leka cikin dakin jikinsu na tsuma saboda
tsoro
da fargabar ko wata masiface zata taso,amma
sai
s**a ji shiri k**ar maye ya ci shirwa.Koda ganin
cewa su Yarima Lubainu sun kasa shiga dakin sai
Bakon Jarumin ya juyo ya dubi Dazyan yayi masa
inkiya.Take Dazyan ya rugo ya bishi a baya,s**a
kunna kai izuwa cikin dakin su biyu,ba tare da
fargabar komai ba.Duk da haka sai su Yarima
Lubainu s**a kasa shiga dakinDaki ne babba mai
girman gaske tamkar wata karamar unguwa.Babu
komai a cikin dakin face durowa da tebura a jere
a
layi,layi kuma sahu sahu reras,iyakar ganin
idanun
mutum babu iyaka.Akan teburan da durowoyin
kwalabe ne birjik.Cike da RUWAN SIHIRI kala
kala.A
cikin durowoyin kuwa kayan TSATSUBA ne iri iri
k**ar kahonni,Layu,Guraye,Kawunan Tsuntsaye
da
sauran sassan jikin dabbobi dana dan Adam dana
Aljanu.Shi kansa bakon jarumin daya shigo cikin
wannan daki saida ya cika da mamakin irin
abubuwan dake cikinsa da yadda akayi aka iya
tarasa.Koda Ya ga sun dan jima a ciki amma su
Sarauniya Akisatul Sauwara sun kasa biyosu
izuwa
ciki sai ya dubi Dazyan yayi masa maganar
kurame.Take Dazyan ya juya da baya ya ruga
waje
yace da su Yarima Lubainu maigidana yace ku
cire
tsoron komai a cikin ranku ku shiga ciki saboda
kune kuka san abinda kukazo nema,kuma akwai
rubuce rubucen sihiri da yawa a cikin dakin a
jikin
abubuwa da yawa wadanda ba zamu iya
karantasu
ba mu fahimta.
Koda jin haka sai Sarki Darmanu yayi wuf ya
wuce
gaba ya shige cikin dakin.Koda Ganin haka sai
Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima Lubainu
ma
s**a bi bayansa da sauri.Shima dan wada
Dazyan
sai ya bisu da sauri s**aje s**a riski bakon
jarumin
a tsaye a cikin tsakiyar daki.Da isarsu Dazyan ya
dubesu yace maigidana yace ya baku damar ku
dudduba ko za kuga abinda kukazo nema.Koda
jin
haka sai duk su ukun s**a rarrabu s**a rinka
bude
durowoyi suna duba kan tebura.Saida s**a shafe
sama da sa'a daya da rabi suna neman ALLON
SIHIRIN Boka Darbusa amma basu ganshi
ba.Al'amarin dayai matukar dugunzuma
hankalinsu
kenan s**a rasa abinda yake musu dadi a
duniya.Koda Bakon Jarumi yaga yadda hankalinsu
ya tashi sai mamaki ya turnukeshi yace a
ransa"Hakika iska na yawo da mai kayam kara!
Yanzu fa saboda kwadayin abin duniya ne yasa
wadannan mutane idanunsu s**a rufe akan
neman
wannan ALLON SIHIRI?A cikinsu ma babu wanda
yafi
cancanta a taimakawa sama da Yarima
Lubainu,domin shine wanda aka zalunta kuma
ake
neman salwantar da rayuwarsa".Koda gama
Aiyana
hakan a cikin ransa sai bakon Jarumi ya tafa
hannayensa sau uku.Koda jin sautin tafin sai
Yarima
Lubainu,Sarki Darmanu da Sarauniya Akisatul
Sauwara s**a tsaya cak ga barin binciken da
sukeyi
s**a dawo inda yake tsaye.Da zuwansa sai dan
wada Dazyan ya dubesu yace,maigidana yace
tunda
dai kun kasa gano inda wannan ALLON SIHIRIN
yake
to shi zai bincikoshi da yardar ubangijinsa.Cikin
alamun karayar zuciya Akisatul Sauwara tace
shike
nan mun amince ya dauko ALLON SIHIRI.Koda
jin
haka sai Bakon Jarumin ya nufi inda jerin
durowoyin
suke.Har yabi layi na farko domin ya fara
bincikawa
sai ya tsaya cak,ya kirga layi na tara ya shiga
yana
kirgasu saida yazo kan durowa ta tara sannan ya
tsaya cak ya dubeta da kyau.Babu kofa a jikin
durowar kuma a rife take ruf.Babu alamar akwai
wani
abu a jikinta inda za'a iya budewa har aga abinda
ke
cikinta.Kawai sai ya daga hannunsa ya doki
tsakiyar
durowar take ta wargaje,ai kuwa sai ga ALLON
SIHIRI
kaso na uku a cikinta.Koda Yarima Lubainu,Sarki
Darmanu da sarauniya Akisatul Sauwara s**ayi
arba
da wannan ALLON SIHIRI sai s**a cika da
tsananin
mamaki.Kawai sai Sarki Darmanu da Sarauniya
Akisatul Sauwara s**a yunkura cikin bakin zafina
nama duk su biyun a lokaci guda s**a kaiwa
ALLON
SIHIRIN cafka,kowannansu na kokarin yariga
dayan
dauka,amma sai bakon jarumin yayi caraf ya
rigasu
dauka ya dubesu cikin murmushi yace,ai dama
nasan cewa sai hakan ta faru a tsakaninku.Da
zancen kurame yayi wannan bayani kuma Dazyan
ne
yayi musu jawabin.Bakon jarumin ya cigaba da
cewa
Kunga wannan ALLON SIHIRI dakuke gani duk
wanda
ya hada gudu uku a cikinsu bai isa ya iya rikeshi
ba
a hannunsa daidai da tsawon dakika goma
ba,amma
idan kuma shakkar hakan ku kawo ragowar bari
biyun dake hannunku kuga zahiri.Koda jin wannan
batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki
Darmanu s**a k**a muzurai suna duru duru
s**a
kasa miko Allunan Sihirin nasu.Koda ganin haka
sai
Bakon Jarumi yayi murmushi kawai sai ya ajiye
ALLON SIHIRIN Boka Darbusa a tsakiyar dakin ya
koma gefe daya zura musu idanu.Nanfa
Sarauniya
Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu s**a k**a
Kallon juna kuma suna kallon wannan ALLON
SIHIRI.Nan take kowannensu ya zaro nasa Allon
Sihirin kuma lokaci guda sai kowannensu ya daka
tsalla ya kaiwa Allon Sihirin Boka Darbusa
cafka.Ai
kuwa sai hannayensu s**a cafki Allon Sihiri a
lokaci
guda.Nan fa s**a mike tsaye a tare s**a k**a
naushin juna kowannensu na kokarin ya kwace
Allunan biyu ya hade da nasa.Gashi dai
kowannensu
yana dakuwa domin naushin junansu sukeyi a
fuska
da ciki amma saboda naci sunki yarda su saki
ALLON SIHIRIN.Shi kuwa Yarima Lubainu dama
ya
koma gefe daya ya zuba musu idanu kawai yana
jiran yaga yadda karshen al'amarin zai
kasance.Bakon Jarumin da dan wada Dazyan
kuwa
sai s**a kara matsawa can gefe daya s**a
zauna
akan wata doguwar kujera suna morewa
idanunsu
da kallon fadan da akeyi.Sarauniya Akisatul
Sauwara
da Sarki Darmanu na cikin kwarmazuwa sai
kawai
s**a ga wata irin GUGUWA ta shigo cikin
daki.Nan
take ta suri komai na cikin dakin har da Sarki
Darmanu,Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima
Lubainu tayi sama dasu ta rinka gwara kansu a
jikin
bango.Amma bakon Jarumi da dan wada Dazyan
kuwa ko kusa dasu wannan guguwa batazo ba
kuma
suma s**a ki suyi wani motsi s**a cigaba da
zuba
idanu kawai.Cikin yan dakiku kadan su Yarima
Lubainu s**a jigata s**a fita daga
hayyacinsu.Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki
Darmanu basu san Sa'adda s**a saki duka
Allunan
Sihirin uku ba s**a fado kasa.Faruwar hakan
keda
wuya sai Allunan Sihirin s**a hade waje guda
s**a
manne da juna tamkar ba'a taba rabasu ba s**a
zama babban Allo guda daya.Faruwar hakan
keda
wuya sai wannan guguwa ta rikide ta zama
wadansu
irin SAMUDAWAN BAKAKEN ALJANU dauke da
muggan MAKAMAN YAKI.Nan fa samudawan
bakaken aljanun s**a ruguntsume da masifaffen
azababben yaki a tsakaninsu,ya zamana cewa
kowannensu na kokarin ya dauki ALLON SIHIRI
ya
gudu dashi amma duk wanda hannunsa yaki kan
ALLON SIHIRI sai kaga an dankara masa SARA
ko
S**A ko kaga an mangareshi ya fadi can gefe
daya
sumamme,ko kallonsa babu mai yi saidai ma
acigaba da tattakeshi a kokarin gwagwarmayar
daukar ALLON SIHIRIN.Tunda aka watsar dasu
Sarauniya Akisatul Sauwara gefe daya a
galabaice
s**a kasa mikewa tsaye s**a cigaba da zama
dirshen a kasa suna kallon wadannan Aljanu
kawai
suna ganin masifaffan yakin da ake yi tsakanin
wadannan samudawan bakaken aljanun.Su kansu
sun san cewa basu isa su iya tarar wadannan
aljanu
da yaki ba bare su iya karbar wan
Nan ALLON SIHIRI daga hannunsu.Saida aka
shafe
sama da sa'a biyu da rabi ana yin wannnan
azababben yaki ya zamana cewa da yawa daga
cikin
aljanun sun zama nakasassu wasu ba
hannaye,wasu
ba kafafu,wasu ma an datse rabin jikinsu,amma
saboda taurin rai irin na aljanu basu fasa cigaba
da
kokarin daukar ALLON SIHIRIN BA.Koda bakon
jarumi yaga ana ta bata lokaci amma an rasa
wanda
zamo GWARZON JARUMIN da zai iya daukar
ALLON
SIHIRIN sai kawai ya mike tsaye zumbur daga
inda
yake tsaye yana mai kwalla KABBARA ya falfalo
da
gudu izuwa inda akeyin wannan gumurzun
yako.Da
karfin tsiya ya ratsa ta tsakiyar samudawan
bakaken
aljanun yana bankesu suna zubewa kasa tamkar
yana sassabe a gona.Koda yazo tsakiyar aljanun
sai
ya sake saka tsalle sama izuwa inda Aljanun
s**ayi
tsiri sama wani kan wani domin s**ai izuwa kan
wani Gansamemen Aljani mafi tsawo,kauri da
Kirar
SADAUKANTAKA wanda shi ne ya sami nasarar
cafe
ALLON SIHIRIN ya bude fuka fukansa yai sama
da
niyyar ya gudu,amma sai wadansu daga cikin
aljanun s**a ruko kafafun nasa suna janyoshi
kasa
don ya fado,amma sai s**a kasa saboda
tsananin
karfin damtsensa.A haka sadaukin Aljanin ya
cigaba
da fuffuka yana kai yakushi SARA DA S**A da
faratan kafafuwansa.Lokacin da bakon jarumin ya
daka tsalle a sama tamkar an harboshi daha
cikin
baka sai da ya iso inda basamuden sadaukin
aljanin
yake,yana isowa daidai fuskarsa sai ya takarkare
ya
zabga masa wawan naushi a fuska.Saboda karfin
naushin take karan hancin aljanin ya karye ya
kurma
uban ihu sak**akon tsananin zafi da zogin da
yaji.Nan take ya dimauce bai san sa'adda ya
saki
ALLON SIHIRIN ba.Caraf sai bakon jarumin ya
cafe
Allon Sihirin da hannu daya alhalin su kansu
samudawan aljanun basa iya daga Allon Sihirin
da
hannu daya saboda tsananin nauyinsa.Koda
Aljanun
s**a ga wannan bil'adama ya karbe ALLON
SIHIRIN
sai s**ayi caa!a kansa s**a yanyameshi suna
masu
kai masa sara da s**a ta ko ina domin su
hallakashi.Ai kuwa sai ya tarwatsa su a lokacin
da
ya sake kwalla Kabbara ya zare takobinsa cikin
bakin zafin nama ya shiga kare kansa gami da
maida martani.Wohoho!wanda Allah ya kare yafi
gaban Magauta!Duk da tsananin yawa na
wadannan
samudawan bakaken aljanu da tsananin karfin
damtsensu da mugayen mak**ansu sai gashi
bakon jarumi ya zame musu ALAKAKAI,Sai gashi
yayi musu mummunar barnar datafi wacce
s**ayiwa
kansu,domin kuwa duk aljanin da yayiwa duka
daya
tofa idan ya baje a kasa wanwar da kyar ma
yake iya
numfashi wasu ma k**ar sun zama gawa.Kai!da
bala'i yakai bala'i sai gashi aljanun suna cika
wandunansu da iska suna ficewa daga cikin
dakin
da gudu.Kafin a jima duk sun tarwatse sun fice
daga
cikin dakinsu duka sun bar bakon jarumin shi
kadai
a tsaye rike da ALLON SIHIRIN a lokacin da dakin
yayi tsit tamkar babu wani mutum daya mai rai a
cikinsa.Yarima Lubainu,Sarauniya Akisatul
Sauwara
kuwa saboda tsananin mamaki bisa ganin irin
gagarumar jarumtakar da bakon jarumin yayi sai
s**a kura masa idanu kawao s**a kasa budar
baki
s**e wani abu,kai mikewa ma tsaye sai ya
gagaresu.Koda ganin haka sai bakon jarumin ya
dubi dan wada Dazyan yayi masa wata inkiya,shi
kuma sai ya dubi Sarauniyar Akisatul Sauwara da
Sarki Darmanu da Yarima Lubainu
yace,Maigidana
yace bazai baiwa dayanku wannan Allon Sihiri ba
face an zauna an tattauna kuma koda ma ya
baiwa
dayanku shi bazai sami damar karantashi ba bare
har ya cika burinsa saboda masu farautar Allon
Sihirin suna da yawa kuma sunfi ku karfin damtse
dana Sihiri.Wadannan Bakaken Samudawan
Aljanu
da s**azo yanzu maigidana ya fatattakesu Yaran
Boka Darbusa ne anan gaba kuma akwai sauran
Manyan MATSAFAN DUNIYA da MANYAN
JARUMAI
dazasu fito farautar wannan ALLON SIHIRI.Kuma
shi
kanshi Boka Darbusa ba hakura zaiyi ba zai
cigaba
da kokarin karbarsa ne.Yanzu sai kowa yaje ya
nemi
dakin da zai kwanta a cikin wannna fada domin
ya
huta tunda dare yayi in yaso gobe da safe mu
tattauna akan abinda muke ganin cewar shi ya
k**ata ayi.Gama fadin hakan keda wuya sai
Bakon
Jarumin ya juya domin ya fice daga cikin
wannan
daki,amma sai Sarauniya Akisatul Sauwara tayi
wuf,ta mike tsaye kuma tayi gyaran murya
tace,yakai
wannan JARUMIN JARUMAI kayi sani cewa mu
muna
cikin tsoro da fargaba don haka bazamu iya
sakin
jikinmu ba har mu kwanta a cikin wannnan fada
ta
Boka Darbusa mu iya kwana a cikinta saboda a
ko
yaushe zai iya kawo mana ZIYARAR BAZATO ya
cutar damu.Koda jin wannan jawabi sai Bakon
Jarumin yaji k**ar ya bushe da dariya amma sai
ya
dake ya dubi dan wada Dazyan yayi masa zancen
kurame.Nan take Dazyan ya dubi Sarauniya
Akisatul
Sauwara yace,ashe bakuyi mamakin yadda
shugaban
ya iya yakar Boka Darbusa ba da dukkan
Aljanunsa?
Shin bakuyi mamakin yadda ya gano inda Allon
Sihirinsa yake ba ya daukoshi kuma har ya hana
wasu saceshi?To ku sani cewa zamanku anan
cikin
wannnan gida tare da shugabana shine kadai
abinda
zai baku kariya amma da zarar kun fita daga nan
to
fa komai zai iya faruwa a gareku,kuma abune
mayuwaci dayanku ya iya tsira da rayuwarsa
bare
har ya sami damar cika burinsa.Koda gama fadin
hakan sai Bakon Jarumin ya saba ALLON SIHIRI
a
hammatarsa ya juya ya fice daga cikin wannan
daki
Dazyan na biye dashi.Koda ganin haka ai
Sarauniya
Akisatul Sauwara,Yarima Lubainu da Sarki
Darmanu
s**a bishi da sauri cikin alamun tsoro suna ta
waige
waige,gani suke k**ar ma a koda yaushe Boka
Darbusa ko wakilinsa zasu iya kawo musu hari a
ko
yaushe. kuyi hakuri dangane da jinkirin post yau

Ibrahim beveji ne

Masu siyan data ina godiya sauranma Allah yabaku Ikon siya
Data are available at all network

04/01/2025

PublicALLON SIHIRI
Littafi na Uku (3)
Part B
Typing Ibrahim bebeji

A CAN FADAR Boka Darbusa kuwa bayan an
shafe
kusan rabin sa'a ana gumurzun yaki tsakanin su
Yarima Lubainu da dakarun dake cikin fadar,su
Lubainu nata samun nasara suna ta ragargazar
dakarun saida s**a karar dasu gaba daya.A
lokacin
ne s**a gaji likis don haka sai s**a zube kasa
suna
haki da numfarfashi k**ar ransu zai fita.Faruwar
hakan keda wuya sai s**a ji takun sawaye da
yawa
daga can wasu bangarori na gidan da yawa ana
rugowa izuwa inda suke.Al'amarin dayai matukar
firgitasu kenan suke mimmike tsaye a
tsorace,kafin
suyi wani yunkuri sai ga wadansu samudawan
dakarun mutane masu kirar MUTANEN
FARKO,rike da
mugayen mak**ai suna ta tuttudowa cikin fadar
ta
gabas da yamma,kudu da arewa,su da yawa ba
adadi.Nan da nan s**a yiwa su Yarima Lubainu
KAWANYA.Koda ganin haka sai Sarauniya
Akisatul
Sauwara ta yarda takobinta,ta dubi sarki
Darmanu da
Yarima Lubainu cikin alamun karayar zuciya
tace,ai
shike nan kuma tamu ta kare,domin babu yadda
zamu iya kare kanmu daga sharrin wadannan
dakaru
a wannan yanayi da muke ciki.Babu wani karfin
dantse ko na Sihiri dazai cecemu.A yanzu duk
burinmu ya rushe,kuma karshen rayuwarmu
yazo,saidai mu rungumi kaddara.Idan muka ce
zamu
yaki wadannan dakaru ma zamu bata karfinmu
ne a
banza ba tare da mun samu koda nasarar sisi a
kansu ba.Koda Sarauniya Akisatul Sauwara tazo
nan
a zancenta sai jikin Yarima Lubainu dana Sarki
Darmanu yayi sanyi,take shima Sarki Darmanu ya
yarda takobin hannunsa,shima Yarima Lubainu
har
ya yunkura zai yarda takobinsa sai ya fasa yace
kai!
Aida dai na mutu RAGO gwara na mutu
JARUMI,tsakanin mutum da sa'a da rabo,mutuwa
ce
don haka dole ne na jarraba sa'ata.Yana gama
fadin
hakan sai ya daga takobinsa sama ya riketa da
hannu biyu.Koda ganin haka sai shugaban
dakarun
ya bushe da dariyar mugunta yace,kai yaro
hakika
ganganci ne ya kawoku nan gidan domin babu
abinda zaku samu face AJALINku.Koda gama
fadin
hakan sai shugaban dakarun ya daga hannunsa
sama ya bayar da inkiyar a afkawa su Yarima
Lubainu.Kafin daya daga cikin dakarun nasa yayi
wani yunkuri sai aka jiyo KABBARA ta cika fadar
gaba dya.Take kowa ya waiga baya izuwa inda
sautin kabbarar ya fito,kawai sai aka hango
BAQON
JARUMI rike da takobinsa ya falfalo da
azababben
gudu,tazarar dake tsakaninsa da wadannan
dubban
samudawan dakaru yakai taku ashirin amma
daua
daka tsalle guda daya sai gashi ya fado a
tsakiyarsu
ya hausu da sara da s**a.Nanfa ya tarwatsasu
shi
kadai ya zame musu GUGUWAR ANNOBA.Da
zarar
sun yunkuro da nufin su yanyameshi sai kaga ya
tarwatsasu yana filfilawa a kasansu da samansu
tamkar katantanawa ake murza wa,kuma duk
inda
yakai sara guda sai dai kaga Mazaje sama da
arba'in sun zube kasa Matattu.Koda su Sarauniya
Akisatul Sauwara s**aga wannan gagarumar
jarumtaka ta ban al'ajabi wacce tafi gaban
hankalinsu da tunaninsu sai s**a cika da
tsananin
mamaki s**a zazzaro idanu s**a zubawa
sarautar
Allah idanu kawai.Nanfa YAKI ya kara TSAMARI
ya
zamana cewa dakarun sun fusata ainun suna
dada
afkawa bakon jarumin ta ko ina da dukkan
karfinsu
suna kai masa sara da s**a,duk da cewa
ragargazarsu bakon jarumin yake,JINI na feshi da
fantsama kuma sassan jikinsu na yawo a sama
yana
zubowa kasa suna ihu da kururuwa suna zubewa
kasa.Saida aka shafe sa'a biyu da rabi ana
wannan
mummunan azababben yaki daya daga cikin
dakarun
bai sami nasarar koda kwarzanar jikin bakon
jarumin ba,kuma basu ga ya gajiya ba.Cigaba
yake
da ragargazarsu kawai amma saboda tsananin
yawansu sai kaga k**ar karuwa sukeyi.Duk
wannan
abu dake faruwa dan wada Dazyan ya shige
karkashin wani tebur ya buya yana morewa
idanunsa kallo,kuma yana karanta addu'ar neman
tsari don kada tsautsayi ya haushi domin shi a
rayuwarsa ko rike takobi bai taba yi ba bare ya
iya
yaki ko ya kare kansa.Haka dai aka cigaba da
wannan mugun azababben yaki har aka sake
shafe
wata sa'ar gudu,a sannan ne fa samudawan
dakarun
s**a gane cewa SHAYI RUWA NE!Domin tuni
bakon
jarumin ya gama kashe kaso biyu cikin kaso
ukinsu.Wadanda basu mutu ba kuwa sun zama
nakasassu,wasu sun rasa kafafu,wasu
hannaye,aki
wasu ma sai kaga an zabtare rabin
kafadarsu,tsabar
taurin rai ne yasa basu mutu ba.Koda ragowar
samudawan dakarun s**a tabbatar da cewar
lallai
bazasu iya kashe wannan takadirin jarumi
ba,kuma
indai aka cigaba da wannan yaki sai ya karar
dasu
gaba dayansu sai s**a ciki wandunansu da iska
s**a bar ragowar nakasassun a wajen.Nan take
fadar tayi tsit,tamkar babu wani mahaluki mai
numfashi a cikinta,kuma sai aka fara kallon kallo
tsakanin bakon jarumin dasu Yarima Lubainu.Shi
kuwa dan wada Dazyan ya fito daga inda yake
boye
ya tsaya a bayan bakon jarumin yana murmushi
gami da karkade kurar jikinsa sak**akon kurar
data
baibaye masa jiki saboda a lokacin da bakon
jarumin yake yaki da wadannan samudawan
dakaru,sun ragargaje duk wani abu mai amfani
dake
cikin fadar an tashi 'kura mai yawa.Bayna anyi
kallon kallo tsakanin bakon Jarumin dasu
Sarauniya
Akisatul Sauwara sai Sarauniya Akisatul Sauwara
ta
tako kafafunta ta matso kusa da bakon Jarumin
ta
dubeshi tace wanene kai kuma menene dalilin
dayasa ka ceci rayuwarmu?Koda jin wannan
tambaya sai bakon jarumin ya dubi Dazyan shi
kuma sai ya dubi Sarauniya Akisatul Sauwara ya
risina a gareta cikin alamun girmamawa
yace,yaku
wadannan jarumai guda uku,kuyi sani cewa
shugabana baya magana ba don ya kasance
kurma
ba,kuma ya rufe fuskarsa ba don bashi da kyau
ba,saboda wani babban sirri ne yasa yake aikata
hakan da fatan bazaku damu ba.Kuyi sani cewa
mu
baki ne daga wata nahiya dabam,kuma munzo
nan
nahiyar ne
domin mu gabatar muku da Addinmu wanda ake
kira
ADDININ MUSLUNCI!ADDININ MUSULUNCI shine
ADDININ GASKIYA,don haka duk wani addini da
kukeyi walau na BAUTAR GUMAKA ko RANA ko
WATA ko ALJANU duk bata ne mabayyani!!!Tsafi
shima shirka ne babba saboda haka muna kira
agareku daku tuba ku bar wadannan addinai naku
ku karbi namu.Ba komai ne yasa shugabana ya
ceci
rayuwarku ba face saboda ya fahimci cewa
wannan
Boka da kuke yaki dashi AZZALUMI ne kuma
mushriki.Shin yanzu zaku karbi wannan Addini
namu ne ko kuwa zaku bijire masa?Koda jin
wannan
batu sai Sarauniya Akisatul Sauwara da Yarima
Lubainu da Sarki Darmanu s**a dubi junansu
s**ayi
shiru aka rasa wanda zaice kala.Daga can sai
Sarauniya Akisatul Sauwara tayi gyaran murya
sannan ta dubi dan wada Dazyan tace,yakai
wannan
gutun mutum..."Koda jin haka sai Dazyan ya
turbune fuskarsa kuma ya tari numfashin
Sarauniya
Akisatul Sauwara yace ke yarinya kada kici min
fuska ko kiyi min rashin kunya.Ki sani cewa na
haifi
k**arki don haka bai k**ata ki kirani da dan
guntu
ba!!!Koda jin haka sai Sarauniya Akisatuk
Sauwara ta
risina cikin biyayya tace,k gafarceni amma
bansan
sunan da yak**ata na kiraka dashi bane.Dan
wada
Dazyan yace sunana na yanka shine DAZYAN!
Amma
ana kirana da ABUL YAZRIN.Sarauniya Akisatul
Sauwara tace,daga yau nayi alkawarin zan rinka
kiranka da Abul Yazrin don girmamawa.Ka
gayawa
mai gidanka cewa muna bukatar cikakkiyar hujja
wacce zata sa mu gamsu da cewa lallai wannan
addini dakukazo dashi shine ADDININ
GASKIYA.Baya
ga haka kuma muna bukatar muyi nazari da
shawara
domin mu sanar dakai abinda muke ganin zaisa
mu
sami nutsuwa da yarda akan wannan sabon
addini
naku.Koda jin wannna batu sai Bakon Jarumin ya
dubi Dazyan yayi masa zance da hannu.Dazyan
ya
dubi Sarauniya Akisatul Sauwara yace maigidana
yace yaki bayananku,kuma ya aminta da duk
uzurin
dakukazo dashi amma kuma yana son yasa abu
guda biyu a tare daku.Abu na farko da yake son
sani shine shin me ya kawo ku nan gidan har
yaki
ya barke tsakaninku da wannan Boka?Abu na
biyu
kuma shine yana son yasan iya tsawon lokacin
dazaku yanke shawara da kuma abinda kuke son
yayi muku wanda zaisa ku gamsu cewa addininsa
shine ADDININ GASKIYA?Ya ce na gargadeku
akan
cewa ku tabbatar da cewar duk abinda zaku fada
masa ku fadi iyakar gaskiya,in ba haka ba kuwa
bazai sake taimakonku ba kuma zaku iya zama
ABOKAN GABA a gareshi!!Kuma yace a sanar
daku
cewa har yanzu fa baku tsira daga sharrin
wannan
Boka ba,domin ba mutuwa yayi ba guduwa
yayi,babu mamaki ma yana nan a labe wani
wurin
yana fakonku.Koda Dazyan yazo nan a zancensa
sai
Hankalin Yarima Lubainu,Sarauniya Akisatul
Sauwara
da Sarki Darmanu ya dugunzuma ainun,s**ayi
tsuru
tsuru suna kallon junansu s**a kasa cewa
uffan.Kawai sai Sarauniya Akisatul Sauwara taja
su
izuwa can gefe daya inda su Bakon Jarumin basu
ji
abinda zasu tattauna ba.Cikin nutsuwa Sarauniya
Akisatul Sauwara ta dubi Sarki Darmanu da
Yarima
Lubainu tace me kuke ganin ya k**ata muce da
wannan hatsabibin bakon jarumi?Kowannenmu ya
ga irin tsantsar jarumtakarsa ta ban
al'ajabi.Tabbas
idan muka yi kuskuren yi masa karya ko yaudara
zamu iya yin nadama.Koda jin wannan batu sai
Yarima Lubainu ya numfasa yace ai dama tun
kafin
na baro gida na dauki alkawaron cewa bazanyi
karya
ba,kuma bazanci amana ba,sannan zan zamo mai
cika alkawari saboda haka idan kun amince zan
wakilceku naje na yiwa wannan bakon Jarumi
bayanin komai bisa gaskiyar al'amarin kuma mu
nemi taimakonsa bisa hada wannan ALLON
SIHIRI
tunda a yanzu haka bamu san a inda Boka
Darbusa
ya boye nasa ALLON SIHRIN ba kuma bamu san
irin
tsaron da ya bashi ba bare har mu iya
daukoshi.To
amma fa akwai matsala guda daya,a tsakaninmu
mu
ukun nan babu wanda yasan abinda kowannenmu
ya
shirya a zuciyarsa.Babu mamaki bayan an hada
ALLON SIHIRI dayanmu ya shammaci sauran ya
cutar dasu ya gudu da ALLON SIHIRIN don cika
burinsa shi kadai tunda dole dai mutum daya ne
daga cikinmu zai iya cika burinsa a lokaci
guda,kuma dole sai yana tare da ALLON SIHIRI
zai
iya kammala sauran aikin cikia burin
nasa.Lokacin
da Yarima Lubainu yazo nan a zancensa sai
Sarauniya Akisatul Sauwara da Sarki Darmanu
s**a
dubi juna kowannensu yai shiru aka rasa wanda
zaice kala.Daga can sai Sarki Darmanu yace kai
yaro
ne tayaya zamu hadu da mutum a yau dinnan
rana
daya jal,kuma mu saki jikinmu dashi har mu gaya
masa sirrinmu?Shin baka tsoron cewa zai iya
cutar
damu ko kuma yayi amfani da sirrin namu sami
Damai-Akala?Kawai muyi amfani dashi wajen
cika
burinmu in yaso mu a tsakaninmu mu sasanta
yadda kowa zai amfana.Koda jin haka sai
Sarauniya
Akisatul Sauwara tayi murmushi tace tabbas
kazo
da shawara mafi alheri,shi kuwa Yarima Lubainu
sai
ransa ya baci ya dubesu su biyun yace,ni kam
daga
yanzu na fita daga cikinku domin bazan iya baku
yarda da amanata ba,tunda har zaku iya yin
karya
da yaudara,gwara na baiwa wannan bakon
jarumin
amincina saboda akwai alamun cewa zaifiku iya
rike
amanata.Koda gama fadin hakan sai Yarima
Lubainu
ya juya ya bar wajen su Sarki Darmanu ya nufi
inda
Bakon Jarumin da dan wada Dazyan ke
tsaye.Koda
ganin haka sai Sarauniya Akisatul Sauwara ta
ruga
izuwa gareshi tasha gabansa tace haba yakai
wannan dan Sarki,ka tuna irin halaccin danayi
maka
lokacin dakazo gareni bisa neman taimakona.Ka
tuna yadda na dauko ALLON SIHIRI NA kuma na
biyoka a cikin wannan tafiya mai hadarin gaske
don
kawai na taimake ka ka sami nasarar samo
lafiyar
jikinka ka koma ga matarka kuma masoyiyarka
YAZARINA?Idan ka tarwatsa mini nawa shirin
saboda
cikar burinka kaci amanata kuma ka nuna mini
cewa
kai
ba dan Halak bane!Koda Sarauniya Akisatul
Sauwara
tazo daidai nan a zancenta sai Jikin Yarima
Lubainu
yayi sanyi kuma hankalinsa ya dugunzuma har
idanunsa s**a dan ciko da kwallah,amma daya
sake
tuno da nasihar da aka bashi kafin ya baro gida
ta
rike gaskiya,amana da alkawari sai ya dubi
sarauniya Akisatul Sauwara yace,kiyi hakuri akan
fadin gaskiay saidai kice naci amanarki.Yana
gama
fadin hakan ya tunkari bakon jarumin gadan
gadan
yana shirin ya isa daf dashi sai dan wada Dazyan
yai
sauri ya shiga tsakiyarsu ya dubeshi a fusace
yace,doka ta farko ba a kusantar maigidana don
yin
magana dashi.Na gaya muku cewa ba kurma
bane
ba,don haka ko daga nesa zaka iya fadin duk
abinda
kakeson fada masa.Koda jin haka sai Yarima
Lubainu yayi murmushi yace hakikanin gaskiya ni
neman magani ne ya fito dani daga kasarmu.Nan
take Yarima Lubainu ya kwashe labarinsa kaf ya
zayyane bai boye komai ba harda batun
soyayyarsa
da YAZARINA wacce ta haddasa gaba a
tsakaninsa
da abokinsa YARIMA MANGUL har s**ayi gasar
neman aurenta ta hanyar yakar juna ya cirewa
Yarima Mangul hannun daya shi kuma yayi masa
asiri ya kashe masa Mazakuta.Yarima Lubainu ya
cigaba da bayani akan fitowar da yayi don neman
ALLON SIHIRI ya karantashi don ya gano inda
KOGIN
BAHAR IMFAL yake yaje cikinsa ya tsinko dan
itaciyar da zata warkar da wannan cuta tasa
domin
ya koma gida a matsayin Namiji lafiyayye yaci
gaba
da ZAMAN AURE da masoyiyarsa
YazarinaLokacin da
Yarima Lubainu yazo nan a labarinsa sai bakon
Jarumin da Dazyan s**a ji sun kamu da tsananin
tausayinsa.Bakon Jarumin yayi shiru yana tunani
da
nazari izuwa tsawon dan dakiku kadan sannan ya
dubi Dazyan yayi masa zancen kurame.A Sannan
ne
Sarki Darmanu da sarauniya Akisatul Sauwara
s**a
taho garesu da sauri domin suji abinda bakon
jarumin zaice.Dazyan yayi gyaran murya sannan
yace,yakai wannan dan sarki kayi sani cewa
shugabana yace inda zaka yi imani da
UBANGIJIN
MUSULUNCI ka karbi addininmu zaka iya samu
lafiyarka a rana guda a cikin dakika guda daya
ma jal
ka yankewa kanwa duk wahalar dake gabanka.To
amma ya fuskanci cewa zuciyarka da ta
wadannan
Abokan Gaba tana da rauni akan yin imani da
ubangijin musulunci saboda kun yarda da Addinin
iyayenku da kakanninku,kuma kuna gani k**ar
addinin naku shine addinin gaskiya,saboda kuga
zahiri kuma ku gamsu cewar addinin musulunci
shine na gaskiya mafin inganci da daraja akan
naku,shugabana ya amince zai ci gaba dayin
wannan tafiya tare daku amma duk inda akaje zai
barku ku jarraba kafin sihirinku da na damtsenku
wajen ganin cewa kun kawar da kowacce irin
masifa
da aka riska sai bayan kun kasa sannan shi ya
kawar da masifar da taimakon ubangijin
musulunci,amma fa sai idan kun dauki alkawarin
cewar bayan anzo karshen tafiyar zakuyi imani
da
addinin musulunci,idan kuma baku yarda ba da
wannan sharadi ba,to zai cigaba da binku kawai
a
cikin wannan tafiya ya zaman dan kallo ba tare
daya
taimaka muku da komai ba.Koda Dazyan yazo
nan a
jawabinsa sai hankali Sarki Darmanu dana
Sarauniya
Akisatul Sauwara ya dugunzuma ainun fiye da ko
yaushe s**a rasa abinda yake musu dadi a
duniya,shi kuwa Yarima Lubainu sai farin ciki ya
lullubeshi ya dubi bakon jarumin cikin murmushi
yace tabbas ni na yarda da wannan sharadi
naka.Koda jin hakan sai Bakon Jarumin yayi
maganar kurame ga Dazyan shi kuma Dazyan sai
ya
dubi Yarima Lubainu yace mai gidana yana
murna
dajin bayaninka.Dazyan ya juya ya dubi Sarki
Darmanu da Sarauniya Akisatul Sauwara
yace,maigidana yace ki kuma fa menene
ra'ayinku?
Cikin rawar murya da tuntuben harshe Sarauniya
Akisatul Sauwara tace babu matsala muma mun
amince da sharadin maigidanka to amma yanzu
yaza ayi akan batun ALLON SIHIRIN Boka
Darbusa
wanda mukazo nema a cikin gidansa?
pls Like nd comments
Ibrahim bebeji

Address

Ep 17 Lafiya Road Kinkinau Kaduna
Kaduna

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Littafin yaki by ibrahim bebeji posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Littafin yaki by ibrahim bebeji:

Share

Category