09/04/2024
Ramadaniyyat: 1445 [30]
✍️Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo Hapizahullah
Rabbaniyyun: Ilimi da Malanta:
12.0. Kyautta mu'amla da mutane:
Ci gaba….
12.4. Cikin waɗanda s**a cutar da Ibnu Taimiyya akwai alƙali Ibn Makhluf. Wannan alƙali yi iya bakin ƙoƙarinsa ya ga an zubar da jinin Ibnu Taimiyya a kan wasu mas'alolin da suke saɓani da shi amma bai yi nasara ba. Shi kuwa Ibnu Taimiyya ta ɓangarensa ga abin da yake faɗa, ya ce: "Wallahi ina daga cikin waɗanda s**a fi kowa ba da gudunmawa wajen kashe duk wata wutar fitina da ta sharri, da kuma tabbatar da alheri a wannan gari Masar da sauran garuruwa. Duk abin da Ibnu Makhluf zai aikata min, ni ta ɓangarena duk wani alheri da zan iya yi masa, to zan yi masa, kuma har abada ba zan taimaka wa maƙiyinsa a kansa ba.. Wannan ita ce niyyata da ƙudurina, tare da cewa ina sane da duk abubuwan da s**a faru. Domin kuwa na san Shaiɗan yana tunzura tsakanin muminai, to don haka ba zan zama mai taimaka wa Shaiɗan a kan 'yan'uwana muminai ba..". [Duba, Ibnu Taimiyya, Majmu'ul Fatawa, juz. 3, sh. 271].
12.5. Bayan fitowar Sheikhul Islam Ibnu Taimiyya daga gidan yari, ya nuna wani hali na dattako lokacin da Sarki Nasir ya dawo kan kujerar mulkinsa. Sarki ya so ya yi ramuwar gayya a kan malamai da alƙalai waɗanda s**a ci amanarsa, s**a goyi bayan abokin hamayyarsa, watau Al-Jashankir. Kuma su dai waɗannan malaman su ne waɗanda s**a riƙa yanke wa Ibnu Taimiyya hukuncin ɗauri a jarabawarsa ta farko, a inda ya yi zaman kurkuku na tsawon wata goma sha takwas a sanadiyyarsu. Don haka sai Sarki Nasir ya nemi fatawa a wajen Ibnu Taimiyya cewa, wane hukunci ya kamata ya yi musu game da cin amanarsa da s**a yi? Sai Ibnu Taimiyya ya buɗi baki ya ce masa: “Jininsu ya haramta a kanka. Haramun ne ka cutar da su”. Sai Sarki ya ce: “Mutanen nan fa sun cutar da kai, sun yi ƙoƙarin kashe ka a lokuta da dama”. Sai Ibnu Taimiyya ya amsa masa da cewa: “Duk wanda ya cuce ni, to ni na yafe masa. Wanda kuwa ya cutar