
05/03/2024
Buba Marwa ya Buƙaci Musulmi dasu yiwa Tinubu, Da Gwamnoni addu’a A Watan Azumin Ramadan
Shugaban Hukumar Yaƙi da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya bukaci ‘yan Najeriya musamman musulmi da su yi wa Shugaban ƙasa Bola Tinubu da sauran jami’an Gwamnati addu’a a lokacin azumin watan Ramadan.
A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar A Yau Litinin, ya bukaci Musulmi da su yi addu’a ga Tinubu, Gwamnonin jihohi, ministoci, da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa a cikin ƙasar nan da addu’ar Allah ya ba su ikon kawo karshen matsalolin da s**a Addabi ƙasar.
Buba Marwa yayi wannan jawabin ne a Masallacin Jumat na tunawa da Alhaji Mohammed Lawal dake Asokoro, Abuja, a Ranar Lahadi, 3 ga Maris, 2024.
Buba Marwa Ya bayyana cewa, “Abin da nake faɗa Akwai shi A Littafi Mai Tsarki cewa mu yi wa shugabanninmu addu’a. Don haka wannan wata mai alfarma na Ramadan ya bamu dama mai yawa wajen yi wa daukacin shugabanninmu da s**a fara tun daga kan Shugaba Tinubu da Gwamnoni da ministoci da sauran shugabanni addu’a domin Allah Ya yi mana jagora a wannan babban aiki na jagorancin al’ummarmu a wannan mawuyacin lokaci Inji shi.”
NBPC News