25/07/2026
Atiku Ya Caccaki Fadar Shugaban Ƙasa Kan Kwatanta Najeriya Da China
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya soki Fadar Shugaban Ƙasa kan amfani da tsarin shari’ar ƙasar China wajen kare Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa hakan ya sake jawo hankalin jama’a kan tsofaffin zarge-zargen da s**a shafi shugaban.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce Fadar Shugaban Ƙasa ta kauce wa mayar da martani kan muhimman batutuwan da ya gabatar, maimakon haka ta mayar da hankali wajen kai masa hare-haren siyasa.
Ya ce kwatanta batun da China ba zai amfani gwamnatin Tinubu ba, domin a cewarsa ƙasar na da tsauraran dokoki kan laifukan safarar miyagun ƙwayoyi da cin hanci da rashawa.
Atiku ya kuma jaddada cewa babu wata kotu a Najeriya ko wata ƙasa da ta taɓa samun sa da laifin cin hanci, safarar miyagun ƙwayoyi ko wani laifi.
Haka kuma, ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta fi mayar da hankali wajen magance matsalolin tattalin arziki, yunwa da rashin tsaro, maimakon shiga cece-kuce na siyasa.
Wannan martani ya biyo bayan kalaman mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, wanda ya zargi Atiku da cin hanci a lokacin da yake Mataimakin Shugaban Ƙasa. Sai dai Atiku ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa babu wata kotu da ta taɓa same shi da wani laifi.