15/10/2025
DALIBAN HAUZAH ILMIYYA SUN ZIYARCI JAGORA (H)
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
‘Yan uwa daliban Hauzah Ilmiyyah, daga kasashen Iran, Iraq, Lebanon, Nijar da Mali sun gana da Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a gidansa da ke Abuja, a yammacin Talata, 20 ga Rabi’ul Thani, 1447 (14/10/2025).
Da yake jawabi ga maziyartan, Jagoran ya bayyana manufar ganawar, inda ya ce, don a tunatar da juna ne akan muhimmancin abinda s**a saka a gaba, ta yadda su kansu za su daura damara su dauki karatun da muhimmanci. “Ku san cewa kuna yin wannan (karatun) ne a matsayin sadaukarwa a madadin dukkanin al’umma.”
Jagora ya tunatar da su muhimmancin tsayuwa da karantar da mutane ilimi, ba kawai wa’azi irin yadda yanzu ake yayin masu wa’azi daban-daban a kasar nan suna yi a sigar hayaniya ba. Yace: “A zauna a yi karatu, a dauko littafi daga bango zuwa bango a karanta kowace kalma sanka-sanka a bi ta da bayani a wuce a sauke, sannan a dauko wani a sake sawa daga bango zuwa bango.”
Shaikh Zakzaky ya bayyana musu cewa, yana da kyau yin ma mutanen gari wa’azi. “Wa’azin da zai iya hada kan al’umma da fahimtar al’umma Musulmi a matsayin abu guda, wannan yana da kyau, ba wanda zai rarraba su ba.” Ya jaddada cewa: “ Amma karantarwa shi ne ‘ahammus shay’i.”
Jagoya ya ce, mutum ba zai karantar da ilimi ba, har sai in ya yi karatu, shi kuma karatun ana sadaukarwa ne a dauki lokaci a yi shi. Inda ya bukaci da su zama misalin kendir, wanda yake kona kansa don ya haska waje. “Abinda ya kamata ma’abota karatu su kasance kenan, su kona kansu don wasu su samu hasken ilimi.”
Ya kuma jaddada musu hadafin karatun a matsayin karatu don a karantar, inda ya ba da misali da yadda Malaman Zaure a kasar Hausa kan sadaukar su yi karatu mai zurfi don su karantar da sauran al’umma.
Jagora ya gargadi daliban ilimin akan tsayawa kyam akan tafarkin addini, ba tare da karkata ga azzalumai ba. Ya ce: “Abinda (wasu) suke ta kokarin su nuna mana shi ne, a zauna lafiya da hukuma. Mu ba mu ce ba za mu zauna lafiya da hukuma ba, amma a wane unwanin? A unwanin muna yaransu? Haihata! Haihata minnaz zilla! Haihata!”
Ya bayyana cewa, amma idan zama lafiya da su din a muna matsayin daidai da su ne, suna ganin mu ma ‘entity’ ne, suna bukatarmu, har suna neman abu a wajenmu, to Masha Allah, ka ga cigaba ne wannan. “Amma ka je a wulakance, kamar masu zuwa rarakan nan, har da cewa wai su ba a san da su ba, ba a yi da su, alhali suna da yawa suna da kaza, amma ba a wakiltansu…. To kaskanci ne wannan.”
Shaikh Zakzaky ya ce, abinda yanzu ake ta kitsa ma mutane kenan, su zauna lafiya da azzalumai. “Ban ki ba, idan mutum ya ga shi yanzu ba zai iya tsayawa kyam ya yi gwagwarmaya ba, ya koma waje daya ya ce koyarwa zan yi. Ba zan zarge shi ba.”
Ya ce: “Amma ya koyar din ne kawai, kada ya bude bakinsa ya ce masu gwagwarmaya laifi suke yi. Tunda shi ba zai iya ba, ya ja bakinsa ya tsuke, ya shiga lungu ya koyar. Ba zai iya wannan ba? To ya yi wannan din, amma kar ya zo ya ce, wadannan da suke wannan abin su bari.”
Ya kara da cewa: “Kowa ya yi nasa. Sadaukarwa ne, in ba za ka sadaukar ba, wani zai yi. An fahimta ai.”
Jagora ya ce, masu ganin cewa zama da mahukunta lafiya shi ne ‘aula’. Sai in ce, da haka nan ne, da Imam Husaini (AS) ya zauna lafiya da Yazidu, da ba a cire masa kai ba. Kuma na san ba za ka fi shi ganin maslahar al’ummar nan ba. Yace: “Yanzu irin wannan da’awar, su suna ganin kamar mu ne muke jefa kanmu a cikin wahala, mu muka ja ma kanmu.”
Don haka ya jaddada kira ga daliban ilimin akan lallai su san hadafin da ya kai su karatun. Wanda yace, hakan muhimmin abu ne. Ya yi musu nasiha akan su tsayu da karban karatu ne daga Malaman da suke karatu a wajajensu, amma su bar musu Fikirorinsu matukar ba ya dace da Fikirar da suke kai ne ba. “Da yake akwai masu Tunani daban daban a Hauzozi, a yi karatun kawai. Luga ne, ya iya Luga, ya koya maka Luga. Fiqihu ne ya iya, ya koyar. Usul ne ya iya, ya koyar. Amma ra’ayinka daban nasa daban, ya rike ra’ayinsa ka rike naka. Allahumma sai dai in ra’ayin naku iri daya ne, amma ba ka je ne a canza maka tunani ba. Yana da muhimmanci ka san diban karatun za ka yi don ka amfana, wani ya amfana da kai.” Ya jaddada.
14/10/2025