A M UMAR

A M UMAR Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from A M UMAR, Publisher, Kaduna.

Adalci ya zama "Tarihi"! a Nigeria, har abada "Nigeria"! ba zata taɓa gyaruwa ba, matuƙar wanda yayi laifi yana da mabiy...
10/04/2025

Adalci ya zama "Tarihi"! a Nigeria, har abada "Nigeria"! ba zata taɓa gyaruwa ba, matuƙar wanda yayi laifi yana da mabiya ko ɗan wata ƙungiya ne ta addini, ko yana da wata ɗaukaka za'a ƙyale shi, idan kuma talaka ne a hukunta shi, An taɓa yin sata a zamanin Annabi (SAW), to wacce tayi satar macece, kuma maɗaukakiyace tana da daraja, sai Usamatu bin zaid (RA) ya samu Manzon Allah SallaLlahu AlaiHi wasalLam yayi masa magana akan kada a yanke mata hannu, Sai Annabi (SAW) yace

أيُّها النَّاسُ إنَّما هلَكَ الَّذينَ من قبلِكُم أنَّهم كانوا إذا سرقَ فيهمُ الشَّريفُ ترَكوهُ وإذا سرقَ فيهمُ الضَّعيفُ أقاموا عليهِ الحدَّ وايمُ اللَّهِ لَو أنَّ فاطمةَ بنتَ محمَّدٍ سرَقَت لقَطعتُ يدَها

Ya ku mutane, lallai ne, abinda ya halakar da mutanen da s**a rigayeku, sun kasance, idan maɗaukakin mutum mai daraja yayi sata, sai su barshi, idan mutum mai rauni (talaka) yayi sata sai su tsayar masa da haddi, na rantse da Allah, da ace Fatima 'yar Muhammad (SAW) zatayi zatayi sata sai na yanke hannunta.

Saheeh Bukhari: 6,788
Sunan ibnu majah:2,088.

Tsabar adalci Irin na Annabi SallaLlahu AlaiHi wasalLam har rantsuwa Saida yayi da Nana faɗima (As) zata aikata laifi da sai ya tsayar mata da haddi, amma yanzu mutum a Nigeria matuƙar yana da wata daraja shikenan ya sha, Saidai idan talaka ne ɗan uwansa, sai ayi hukunci akansa, matuƙar Babu adalci kuwa ƙasa ba zata taɓa gyaruwa ba, Allah ya gyara mana.

06/04/2025

Kashim Shettima ya zame ma Tinubu Kadangare baki Tulu....

06/04/2025

Ku RUBUTA KU AJE 2027 IN SHA ALLAHU TINUBU BA ZAI CI ZABE BA

ALLAHU AKBÀR: Waɗannaɲ Fitattun Malaman Dukaninsu Sun Râsu Ranar Juma'a, Allàh Yasa Muyi Mųtuwãr Shăhąda.
04/04/2025

ALLAHU AKBÀR: Waɗannaɲ Fitattun Malaman Dukaninsu Sun Râsu Ranar Juma'a, Allàh Yasa Muyi Mųtuwãr Shăhąda.

29/11/2024

Anyi Ebola Mun Sha da Kyar Yanzu ga Bola yazo da Kan Shi ya Allah Ka Cece mu🤲🤲

21/10/2024

Wanda ba a yi ZABE ba aka ce yaci ya sunan Shi ❓

APC ❌❌

Mace ce bayan ta shafe shekara 42 tare da mijinta, wanda a bana ya cika shekara 60 a duniya, Allah Ya albarka ce su da '...
07/10/2024

Mace ce bayan ta shafe shekara 42 tare da mijinta, wanda a bana ya cika shekara 60 a duniya, Allah Ya albarka ce su da 'ya'ya bakwai da jikoki 10. Bayan mijin ya yi ritaya a bana, sai ya yi amfani da kudin ritayarsa ya auro mata sa'ar jikarta mai shekara 17.
Mece ce mafita musamman ga shi yanzu yana barazanar maka mata saki uku?

Man Of The Match ✅Best Player Of The Tournament ✅
25/08/2024

Man Of The Match ✅

Best Player Of The Tournament ✅

Destination In North Central 😍😍😍📷 WhereInNasarawaF@llow Man Man do man for more updates
18/08/2024

Destination In North Central 😍😍😍

📷 WhereInNasarawa

F@llow Man Man do man for more updates


09/08/2024

Da Masu Ɗaga Tutar Ƙasar Waje, Da Masu Sace Dukiyar Ƙasa Su Kaita Ƙasashen Waje, Su Waye Maciya Amanar Ƙasa❓

10/07/2024

ALAMOMIN SHAFAR ALJANU
********************************
Yadda zaka gane cewa Aljanu sun shafeka, ko kuma sun shafi waninka.

Duk wanda yake biye da ZAUREN FIQHU zai ga wani lokacin muna yin zurfafan bayanai game da lamarin Shaitanun Aljanu masu shiga jikin Bil Adama, har wasu suna ganin kamar ba haka bane.

Amma daliban ZAUREN FIQHU na whatsapp sun sha saurarar Audio na wasu rukiyyoyin da aka gabatar anan..

Yau kuma in sha Allahu zaku ji bayanin alamomin da ake gane shafar Aljanu ajikin mutum.

Wadannan alamomin sun kasu zuwa gida biyu. Akwai na fili, akwai kuma wadanda bassu faruwa sai alokacin barci.

ALAMOMIN 'BOYE:
********************
1. Bushewar idanu : Zaka ga mutum ya kwanta akan shimfidarsa amma barcin ba zai zo masa ba, sai Chan tsakiyar dare ko kuma wajen Asubah.

2. Yawan farkawa daga barci A FIRGICE!! . Wani zaka ga kusan duk minti talatin sai ya farka, ko Qasa da haka.

3. DANNAU: Mutum yana kwance zai ji wani BAQIN ALJANI yazo ya danneshi. Zai yi ta EEHU!!. Amma babu mai jinsa.. Wani lokacin wasu sunfi yinsa da safe bayan sallar asubah.

4. MAFARKAI MASU FIRGITARWA: Kamar kayi mafarkin an biyoka za'a yanka ka, ko kuma mafarkin fadowa daga wani tsauni, ko kuma kaga hallaka Qarara, idan ka farka zaka ji jikinka duk zuffa!.

5. MAFARKIN NAMUN DAJI : Ganin miyagun dabbobi amafarki kamar macizai, Karnuka, Kyanwa, Rakumi mai fada, Damusa, Saniya, 'Bera, suna bin mutum zasu kamashi. etc.

6. Tauna acikin Barci. (kaji mutum yana barci amma yana taune-taune).

7. Dariya ko Kuka, ko Eehu acikin barci.

8. Kaga mutum yana barci amma ya tashi tsaye yayi tafiya, sannan ya dawo ya kwanta alhali ko farkawa bai yi ba.

9. Mafarkin afkawa cikin ruwa, ko Jini, ko wani mummunan rami.

10. Mafarkin Matattu, ko ganinka a MAQABARTA, ko wajen yanka dabbobi, ko kwata, ko Juji, ko tsakiyar Daji mai duhu.

11. Mafarkin Gajerun Mutane, ko dogaye tsola-tsola. Ko farare Sol, ko bakake WULUK, masu ban-tsoro.

12. Mace ta rika yin Mafarkin wani namiji yana zuwa yana saduwa da ita, bisa siffar Mijinta, ko saurayinta, ko mahaifinta, ko dan uwanta, etc.

13. Namiji ya rika mafarkin wadansu mata suna zuwa masa suna kwanciya dashi.

ALALOMI NA FILI
*******************
1. CIWON KAI : Marar jin magani. Ko an sha magani ba zai dena ba. Kuma gobe ko jibi ma sai ya dawo.

2. FADUWAR GABA : Kaji Qirjinka yana bugawa FAT! FAT!! FAT!!! (kamar zai fashe).

3. JUYARWA daga bin Allah ko duk wani abinda ya shafi addini kamar Zikirin Allah, karatun Alqur'ani, da sauran abinda Allah yake so, kai kuma sai kaji baka so.

4. BAQIN CIKI : Haka kawai babu wani dalili sai kaji ranka yana ta baci, kana jin haushin kowa da kowa ba tare da wani dalili ba.

5. RIKICEWAR TUNANI: Kaji kamar komai ya chabe maka. Ka rasa yadda zakayi.

6. Rashin lafiyar wata ga'ba. Amma likitocin zamani sun gama bincike sun kasa ganowa ko magance chutar.

7. Rikicewar Jinin haila. Rashin zuwansa akan lokaci ko kuma zuwansa fiye da kima.

8. Yawan zubewar Juna-biyu. Ko kuma rashin samunsa kwata-kwata.

9. Jin tafiyar kiyashi ajikinka ko yaushe.

10. Jin maganganu masu tsoratarwa ba tare da kaga mai maganar ba.

11. Jin tsananin sha'awar aikata sabon Allah. Kaji kamar ana ingizaka.

12. Yawan mantuwar karatu, ko rashin fahimtarsa. Wato toshewar basira, alhali da chan ba haka kake ba.

13. Yawan jin waswasi ko kokonto ayayin tsarki ko alwala ko Sallah.

14. Yawan Kuka ko dariya ba tare da wani dalili ba.

15. Jin Kasala mai tsanani tare da nauyin jiki.

16. Tsoron shiga cikin jama'a, ka rika jin kamar zasu hallaka ka, alhali kuma ba haka bane.

17. Idan kina tafiya ki rika jin kamar wani yana binki a baya.

18. Yawan Qiyayyar juna atsakanin ma'aurata. Idan mijinki baya nan kiji kina mutukar sonsa. Amma da zarar ya dawo sai ki rika ganinsa kamar dodo, ki rika jin baki son ganinsa ko jin maganarsa.

19. Ciwon ciki ko baya, ko Qafa duk alokaci guda kaji kamar ciwon yana yi maka yawo ajikinka. Kuma ko anyi scanning ba za'a ga komai ba.

20. Kaikayin farji, ko Kuraje, ko fitar farin ruwa. Amma ko an sha magani ba ya denawa.

21. Jin zafi alokacin saduwa, ko daukewar Ni'ima, bushewar gaba, etc.

22. Son zama acikin BANDAKI, ko agaban dustbin, ko Juji (bola) ko kuma wani wajen Qazanta.

Idan kana fama da alamomi guda biyu ko uku ko sama da haka, kuma kana bukatar taimako, zaku iya

13/06/2024

Duk Wanda ya sake ciyo Bashi Dan ya Gina Nigeria 🇳🇬 Allah ya tsine Masa Albarka

Address

Kaduna

Telephone

+2348100333153

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when A M UMAR posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to A M UMAR:

Share

Category