12/08/2026
SPONSORED
SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR LERE YA KADDAMAR DA RABON TAKIN KYAUTA NA GWAMNA UBA SANI
Shugaban Karamar Hukumar Lere, Hon. Jafaru Ahmed, ya kaddamar da rabon takin zamani kyauta ga manoman Karamar Hukumar Lere, a matsayin wani bangare na tallafin noma da Gwamnan Jihar Kaduna, Mai Girma Sanata Uba Sani, ke bayarwa domin bunkasa harkar noma da tallafawa manoma.
An bayyana cewa wannan tallafi zai taimaka wajen rage wa manoma radadin tsadar kayan noma, musamman taki, tare da ba su damar kara yawan amfanin gona da samun ingantaccen noman zamani.
A nasa bangaren, Shugaban Karamar Hukumar Lere ya bayyana muhimmancin wannan tallafi ga manoma, yana mai cewa samar da taki kyauta zai taimaka wajen bunkasa noma, samar da abinci da kuma inganta tattalin arzikin al’umma.
Haka kuma, rabon takin na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na karfafa harkar noma da tallafawa manoma domin samun wadataccen abinci da inganta rayuwar al’ummar jihar Kaduna.
Ana sa ran tallafin zai kara wa manoma kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukan noma a wannan kakar, tare da taimakawa wajen rage matsin tattalin arziki da ke tattare da tsadar kayan aikin noma.
RAMKA MEDIA 📺 TV