08/10/2025
Barayin Mashin Sun Jikkata Auwal Auta Kardi a Azare
Wani matashi mai suna Auwal Auta Kardi ya shiga mawuyacin hali bayan da barayin mashin s**a kai masa hari jiya yayin da yake kan hanyarsa zuwa gidansa a kauyen Kardi, cikin garin Azare, Jihar Bauchi.
Rahotanni sun nuna cewa barayin sun kwace masa mashin, inda har s**a jikkata shi sosai s**a cire masa hannu guda kafin su tsere.
Yanzu haka yana kwance a Asibitin Tarayya na FUHSTH Azare a sashen gaggawa, inda yake karɓar kulawa.
Ana roƙon ’yan siyasa, ’yan kasuwa, da masu hannu da shuni da su taimaka masa wajen samun lafiya da jinya.
Ko a kwanakin bayama wadanan Batagarin sun jikkata wani a yayin da suke kokarin kwace masa abin hawan sa.
Kwacen waya kuwa Yazama Ruwan dare a garin na Azare.
Wanda Wannan lamari ya tayar da hankalin jama’a, yayin da al’umma ke kira ga hukumomi da su dauki matakin gaggawa kan karuwar ayyukan ta’addanci da fashi da makami a yankin Bauchi, musamman garin Azare, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Idris Azare.