28/02/2026
Ya Kamata Gwamnati Ta Ɗaura Ɗamara Domin Magance Matsalolin Tsaron Da Su Ka Addabi Yankin Arewa
Daga Ibrahim Imam Ikara
Matsalolin tsaro da ke addabar Arewacin Najeriya, matsala ce da ta shafi dukkan al'umma, sakamakon babu wata al'umma da za ta samu ci gaba mai ɗorewa, ba tare da zaman lafiya da tsaro ba.
Gwamnatin tarayya zuwa jihohi, da hukumomin tsaro su sake ɗaura ɗamara domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da su ka dabaibaye yankin Arewa, wanda hakan ya ke haifar da koma baya ga yankin Arewa, musamman a ɓangaren sabon Ministan Tsaro, da har yanzu al'umma ba su ga sabon chanji a zahiri ba, domin maimakon samun sauƙi, sai aka sake samun wasu matsalolin tsaro a wasu yankunan.
Ina kira ga al'umma da su ɗauki salon da zai haifar da zaman lafiya, ba ƙoƙarin ruruta wutar ƙabilancin da zai haifar da gagarumar matsala ba, domin ta'addanci ba shi da addini, ta'addanci ba shi da ƙabila, sannan ba ya wakiltar wata al'umma. A kowane rukunin al'umma ana iya samun masu aikata miyagun laifuka, don haka jingina ta'addanci ga wani addini, ko wata ƙabila kuskure ne babba, wanda hakan ya ke karkatar da hankalin al'umma daga hanyoyin da za a shawo kan matsalolin, har a magance su.
Tsaro nauyi ne na kowa, amma jagoranci nagari, da kuma kyakkyawan tsari ya na daga cikin ginshiƙin dawo da zaman lafiya.
Lokaci ya yi da gwamnati za ta ɗauki matakai masu tasiri, domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma. Zaman lafiya shi ne tushen ci gaba, don haka al'umma su na jiran su ga aiki a ƙasa.
Kuma mu ci gaba da addu'a da kai koken mu zuwa ga Allah mai girma. Allah ya ba mu zaman lafiya mai ɗorewa, Allah ya yi mana maganin ƴan ta'adda da ta'addanci a Najeriya.
Allah Ya hallaka da tona asirin masu hannu a rashin tsaro a Arewa, daga ciki suke ko daga wajen ƙasa, daga talakawa suke ko daga masu da shi, da ga mu ne ko daga su ne, musulmi da wanda ba musulmi ba, Fulani ne ko bahaushe ko ma ko wane ƙabila su ke, a masu mulki ne ko waɗanda a ke mulka ne, Allah ka san su ka saka mana, ka kawo mana ƙarshen rashin tsaro ya Rabbal Ibaad!