01/06/2025
AJAM Ta Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Kan Nasarorin Da Ta Cimma Wajen Dawo da Zaman Lafiya a Arewa
Gamayyar Kungiyar Ayyukan Arewa (AJAM) ta jinjina wa Gwamnatin Tarayya bisa manyan nasarori da ta samu wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin Arewa, wanda da can ya kasance cike da matsalolin ta’addanci da miyagun laifuka.
Kungiyar ta bayyana musamman rawar da Ma'aikatar Tsaro ke takawa wajen aiwatar da manyan ayyukan tsaro masu amfani da fasahar zamani a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Tsakiya.
A cikin wata sanarwa da mai jagorantar kungiyar, Lauretta Bako ta fitar a ranar Alhamis, AJAM ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a fannin tsaro a yankin, wanda hakan ya biyo bayan dabarun rundunonin tsaro da gwamnatin ke aiwatarwa.
"A yau muna rayuwa a wani sabon yanayi na tsaro fiye da da, inda aka kore Boko Haram zuwa matsugunan duhu, yayin da shugabannin masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga s**a hallaka ko s**a tsere."
"Nasarorin da aka samu wajen kawar da ‘yan bindiga, ‘yan ta’adda da kuma sarkakiyar hanyoyin aikata laifi, tare da farfado da tattalin arzikin yankuna, ya nuna ingancin wannan tsari."
A cewar AJAM, daya daga cikin ginshikan wannan nasara shine Operation FANSAR YAMMA, wanda ya samu nasarori da dama, ciki har da hallaka sanannen shugaban ‘yan bindiga, Kachalla Dogo Isah, tare da wasu ‘yan ta’adda 44 a jihar Zamfara.
Sanarwar ta kara da cewa, “Kashe fitattun masu aikata laifi ciki har da masu sayar da mak**ai da shugabannin ‘yan bindiga ya tarwatsa manyan hanyoyin aikata laifi, tare da isar da sako ga sauran masu laifi cewa gwamnati ba za ta yarda da rashin tsaro ba.”
Tasirin wadannan matakan tsaro ya wuce kidayar alkaluma kawai; yana da tasiri kai tsaye ga rayuwar yau da kullum ta ‘yan kasa. Hanyoyi k**ar hanyar Kaduna-Abuja, wanda da can aka fi jin tsoro, yanzu sun fi aminci ga matafiya, hakan kuma yana taimakawa wajen kasuwanci da zirga-zirga.
Kasuwanni a wurare irin su Giwa, Birnin Gwari da Jibia suna samun sabuwar rayuwa, inda shugabannin al’umma da jama’a ke tabbatar da ingancin tsaro. Farfadowar harkokin kasuwanci na da nasaba kai tsaye da nasarorin da sojoji s**a samu tare da samar da yanayi mai kyau ga kasuwanci.
Gina Brigade na National Mission Force a Samaru Kataf shima ya taka rawa wajen warware matsalolin tsaro a Kudu ta Kudancin Kaduna, wanda ya haifar da ingantattun yanayin zamantakewa da tattalin arziki. A cikin watanni ukun farko na shekarar 2025 kadai, an hallaka ‘yan ta’adda 122 kuma an k**a fiye da 1,000 daga cikin masu laifi.
A matsayinmu na Arewa Joint Action Movement, muna tare da kokarin da Ma’aikatar Tsaro ke yi wajen kare al’ummominmu da dawo da fata a zukatan jama’a. Muna fahimtar cewa har yanzu akwai kalubale, amma nasarorin da aka samu sun haskaka mana hanya. Zamu ci gaba da goyon bayan manufofi da matakan da za su kawo zaman lafiya, tsaro da cigaba mai dorewa a Arewarmu.