16/05/2025
🔒 KEYLOGGER: WATAKILA ANA SATAR BAYANANKA AMMA BA KA SANI BA!
An sha yi wa mutane satar sensitive information da makudan kudade a wayoyi da computers ba tare da sanin ta ina hakan ya faru ba. To keylogger ya kan iya zama daya daga cikin hanyoyin. Amma mene ne shi???
Keylogger aft?ck method ne da ake amfani da shi don satar bayanan da mutum yake rubutawa a waya ko computer ba tare da saninsa ba. Yana daya daga cikin hanyoyin da miyagu ke amfani da su wajen samun passwords, da private details, da sauran sensitive information na mutane.
Keylogger yana aiki ta hanyar bin duk wani keystroke da mutum ke rubutawa a kan keyboard dinsa. Misali, hanya ta farko ita ce software-based keyloggers wacce ta kasance a siffar software.
Kai ne ka yi installing app a wayarka ba tare da aminta da sahihancinsa ba, shi kuma ashe an sa masa cewa duk abun da ka rubuta a wayarka kamar password, PIN, bank details to ya dauka ya tura wa wadanda s**a kirkire shi! Tirkashi!
Ta wannan hanyar an sha yi wa mutane k*tse amma ba su gano hakan ba, saboda ba su cika duba sahihancin abu ba kafin su yi amfani da shi, musamman idan aka ce musu free ne ko kudi za su samu.
Ga wasu common infection methods nan da ake samunsa
—Shiga malicious websites
—Sauke cracked software
—Bude phishing emails da ke dauke da attachments
—Sanya malicious USB drive a device dinka
—Shiga websites na 'yan damfara
Sai dai ba lallai ba ne ka san akwai keylogger a wayarka, amma dai da zaran ka fahimci suspious activity to sai ka san tayi.
Allah Ya tsare mu, amin.