14/11/2024
Yan kungiyar da ke dauke da makamai na Lakurawa sun yi ta ja da baya a yayin da sojoji ke kai hare-hare ta kasa da sama a kan sansanonin kungiyar a fadin jihohin Kebbi da Sokoto.
Bayan wani hari da kungiyar Lakurawa ta kai kan al’ummar Mera a karamar hukumar Augie a jihar Kebbi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 17, hedkwatar sojojin ta aike da tawagar sojoji zuwa yankin.
Da isar sojojin a Birnin Kebbi, a cewar Abdullahi Idris Zuru, mai taimaka wa gwamnan Kebbi kan harkokin yada labarai, sun gana da mataimakin gwamna Abubakar Umar Tafida a ofishin majalisar zartarwa kafin su wuce zuwa Mera.
Zuru ya ce sojojin sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’addan tare da kwato shanu da dama da s**a bari a baya yayin da maharan s**a gudu.
Wannan aika aika ya zo ne bayan da gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ba da tallafin gaggawa domin magance yawaitar tashe-tashen hankulan da kungiyoyi masu dauke da makamai ke kawo cikas ga rayuwa a yankunan karkara.
Gwamnan ya yi alkawarin kare rayuka da dukiyoyin daukacin ‘yan jihar Kebbi, wanda hakan ya sa ya nemi gwamnatin tarayya ta shiga tsakani domin yakar ta’addanci a fadin jihar,” inji Zuru.
A halin da ake ciki, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya bada tabbacin cewa za a fatattaki ‘yan kungiyar Lakurawa dake ta’addanci a jihohin Arewa maso Yamma daga Najeriya.
Ribadu ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Larabar da ta gabata a Abuja a wajen bukin bude babban taron kwastam na shekarar 2024, inda ya wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Zamu fatattaki wadanda ake kira Lukarawa daga kasarmu. Za mu kunyata masu s**a, mu rufe bakunansu nan da nan.
Boko Haram da s**a addabi kasarmu, yanzu sun fara gudu.
Membobin kungiyar a yanzu suna tafiya zuwa wasu kasashe makwabta saboda Najeriya ba ta da amfani wajen gudanar da ayyukansu, in ji shi.
Najeeb Lawal Aliyu Saulawa