02/03/2024
BBC News, Hausa
Tsallaka zuwa abubuwan da ke ciki
Sassa
Labaran Duniya
Wasanni
Nishadi
Cikakkun Rahotanni
Bidiyo
Shirye-shirye na Musamman
Shirye-shiryen rediyo
Jihohin arewacin Najeriya da ke cikin haɗarin yaɗuwar cutar sanƙarau

ASALIN HOTON,GETTY IMAGES
Bayani kan maƙala
Marubuci,Nabeela Mukhta Uba
Sanya sunan wanda ya rubuta labari,Multimedia Broadcast Journalist
Twitter,
Aiko rahoto dagaAbuja
Sa'o'i 4 da s**a wuce
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, Nimet ta lissafo wasu jihohi a ƙasar da suke cikin haɗarin kamuwa da cutar sanƙarau.
A shafinta na X, hukumar ta Nimet ta ce jihohin da s**a fi haɗari galibi a yankin arewacin ƙasar ne da s**a ƙunshi Sokoto da Jigawa da Yobe da Borno.
Jihohin da suma suke cikin haɗarin ɓullar cutar sun haɗa da Zamfara da Katsina da Kano da Bacuchi da Gombe da Kebbi da Adamawa.
Bayanin na Nimet na zuwa daidai lokacin da a baya-bayan nan hukumomi a jihar Yobe s**a tabbatar da ɓullar cutar ta sanƙarau a makarantun sakandaren mata uku da kwalejin ƴan mata ta gwamnatin tarayya a ƙananan hukumomin Potiskum.

ASALIN HOTON,/X
Cutar ta yi ajalin ɗalibai 17 ƴan makarantar kwana yayin da ragowar ukun ƴan Firamare ne sai kuma wasu da dama da suke jinya a asibiti sakamakon kamuwa da cutar ta sanƙarau.
A asibitin ƙwararru na Potiskum, an samu adadin mutum 214 da s**a kamu da cutar sannan uku kuma suna cikin sashen kula da lafiya na asibitin suna karɓar magani.
A bayanin na Nimet, akwai jihohin da ke da sauƙin kamuwa da cutar da s**a haɗa da Kaduna da Filato da wani ɓangaren Adamawa da Neja da Kwara da Abuja da Nassarawa da Taraba da Benue da Kogi.
Sai kuma jihohin da ba sa cikin haɗarin kamuwa da cutar ta sanƙarau da suke yankin kudancin Najeriya.
A wannan maƙalar za mu duba alamomin cutar ta sanƙarau da kuma yadda mutum ke iya kare kansa daga ita.
Shin ajiye abinci a firji na da illa?18 Fabrairu 2024
Cutukan da ke yaɗuwa lokacin zafi da dabarun kauce musu16 Fabrairu 2024
Me ya sa tsofaffi