
04/08/2024
WANENE SHEIKH MAHMOUD KHALIL AL-HUSARI ???
- Haihuwa a garin Tanta - Egypt (1917-1980)
- farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a duniya, da riwayar Imamu Hafsu daga Imamu Asim a shekarar 1961.
- farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a duniya, da riwayar Imamu warshu daga Imamu Nafiu a 1964.
- farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a duniya, da riwayar Imamu Qalun daga Imamu Nafiu a 1968.
- farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a duniya, da riwayar Imamud Dury daga Imamu Abu Amru dan Ala a 1968.
- farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a duniya mai dauke da salon koyar da Alkur'ani (Mu'allim) 1969.
- farkon wanda ya fara yin kaset cikakke na Alkur'ani a duniya da salo na tafsiri 1975.
- farkon wanda ya fara yin karatun Alkur'ani a zauren majalisar dinkin duniya 1977.
- Farkon wanda ya fara yin karatun Alkur'ani a fadar sarauniyar Ingila 1978.
- Farkon wanda ya fara karanta Alkur'ani a fadar white house da majalisar dattawa ta Amurka (congress)
- shugaban makaranta Alkur'ani na duniya a zamaninsa.
- Yayi wasiyya da sulusin dukiyarshi domin hidimtawa Alkur'ani mai girma da makaranta Alkur'ani.
- Mai son kwarewa a fannin karatun Alkur'ani ya makalkale mishi, babu kari babu ragi.
Allah jikansa ya gafarta masa tare da sauran hadiman Alkur'ani mai girma.
Yusuf Saidu Abusaeed 🙏🙏🙏